Sashe 190
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko Fatima? Itama uwar taki mun ba ta hakuri kuma ta ce ta hakura amman mu tambayi izinin ki, ina so ki cire komai a ranki ko domin lafiyan abib da ke cikin ki, ki tashi ki bi mijin ki kin ji ko? Bai kyauta ba mun masa fa a ya kuma ya ce ba zai ara ba, mu abin da kika yi mana na an mu iyayen ki ya fi komai yi mana a i Allah ya yi muku albarka Allah ya zaunar daku lafiya tare da zuru'a mai albarka." Wannan karon gogan a cikin ransa ya amsa sai Inna ce ta amsa a fili. Mimin kanta na asa ta kasa mgana. "Kin yi shuru Fatima? Ki ce wani abu mana." Baba anjuma ya tambayeta. Sai ta ara sadda kanta asa kafin ta ce" Na hakura Baba, ni daman saboda zargin yake yi min ne ya sa na kawo muku wannan mganar." Da sauri Baba ya ce"Eh wlh, kuma kin kyauta mganar zargi ai babban mgana ce, an yi masa mgana ba zai ara ba." Sai Mimi ta jinjina kai kafin tac ce"Shike nan zan bi sa mu koma." Baba ya ce Alhandulillah Allah ya yi miki albarka Mansoor kuma har da sauke Ajiyar zuciya. "Amman kuma ina da shara i. Shara in nawa kuma ina so ku zama shaida Baba da Inna.." Haka ta fa a kai tsaye tana kallon Aji da ke kallonta, Inna ta yi mirmishi kafin ta ce" Fa i sharadin ki, muna goyon bayan duka hukuncin ki Binta." Sai ta kauda kanta kafin ta ce"Na yi hakurin zargin da ya jefeni da shi, amman ku zama shaidata wlh tallahi in har ya ara maimaita wani abu makamcin haka zan tafi, kuma in na tafi bazan dawo ba, domin ba zan iya zama da wanda bai yarda da ni ba sannan ba zai iya shaida na ko da a bayan idanuwana ba ne." Baba ya jinjina kai kafin ya ce"Gaskiya ne, In sha Allahu ma haka ba zai ara faruwa ba." Inna Meri kuma ta ce"Kin yi min dai dai, ni da kaina wlh in ka ara sai na tursasa maka ka saketa, in dai kai ba ka san baiwar da Allah ya yi maka ba to ka in ka yi sakaci Binta ta bar ka sai dai ka mutu ba ka yi aure domin ban ga macen da za ta yi hakuri ta zauna da kai da mummunan hallayarka na rashin lissafi ba. kishi ai ba hauka ba ne sai ka hana yarinya walwala kawai saboda kishin ka na banza? To wlh ka shiga hankalin ka tun kafin wata rana ka yi ta kuka ba mai share maka hawaye." Baba anjuma ya ce"Gaskiya ne, amman duk hakan ba zai kai ga faruwa ba in sha Allahu" inna Meri ta harari bangaren Mansoor kafin ta ce"Shi dai ya sani,damar ta karshe gare shi, ki je ciki ki shirya sai ku tafi." Mimi ta mi e a sanyaye ta wuce Mansoor ya bi ta da kallo, shi yanzu ai yana cikin TSAKA MAI WUYA. Ya san yana da kishi amman kuma dole ya koyi sarrafa kishin sa matukar yana son zaman lafiya. Bayan tashin Mimi nasiha fa a haka Inna da Baba suka tasa shi suna yi har sai da Mimi ta fito Walida ta rakota da jakarta da kayanta da Walidan ta wanke mata. Inna ta kalli Mimi lokaci aya tana fadin"In kina bukatar wani abu ki gaya min sai na saka Walida ta kawo miki kin ji ko?. Sau ta gya a kanta, so take yi ta ce a zuba mata tuwo amman ta kasa mgana sai Walida ta yi ma ra a ita kuma ta gaya ma Inna. Mirmishin su na manya ta yi domin ta na da tabbacin domin Mansoor za ta auki tuwon nan sai ta ce Walida ta zuba musu a kula su ta fi da shi. Mansoor ya ce Baba ya zo su fara sauke shi a gida yace a'a zai samu mai mashin su dai su tafi. Har bakin mota Walida ta rakata ta saka musu tuwon a bayan mota da jakar Mimi da kayanta tare da magungunta. Har su ka bar anguwan nan kallo Aji bai ishi Mimi ba shi kuma sai ya rasa abun cewa, ya kalleta sai ya ga ta na kallon gefe ne ba ta ma son kallon shi, sai ya rasa abun cewa sai da ya ji ta na tari sannan ya ce"Sannu, ko a rage A.c ne? Ta yi masa banza da kansa ya rage iskar motar sannan ya koma yana fa in" Har da mura ke damun ki ko? Kamar ba ta motar haka ta yi masa, Ya yi ta ta alan mgana amman Mimi ko uffan ba ta ce masa ba, har suka isa gida yana hon megadi ya bu e musu get suka shiga gidan yana gyara parking ta yi saurin bu e motar ta fito, baya ta bu e baya ta auko jakarta da ledan mganinta da sauri ya zagayo ya kar a lokaci aya yana fa in"Ke da ba ki da lafiya ina ke ina aukan kaya Mimi? A sanyaye ya yi mganar, sai kawai ya ga ta ara kauda kai ta sakar masa kayan hannunta ta juya a hankali ta nufi cikin gida shi a ka bari da kwaso kayan har da kwandon da Walida ta zuba musu tuwon ko da ya shiga falon har ta shige ciki ya duba ba ta a bedroom insu a she akinta ta shige a bin ta yana shiga kuma ya ganta ta tu e za ta shiga wanka, bai yi mgana ba ganin kallonsa ma ba ta san yi, dole ya koma falo ya zauna yana shafa kansa. Mu'azzam ne ya kira shi suka yi mgana ya ce masa Inna ta hakura, shima sai da ya ara yi masa fa a sannan suka yi sallama Hibba na gefensa da katon cikinta ta ce"Kai ni dai na kasa gane halin yaya Mansoor." Mu'azzam ya ce"Ya dai kusa zama uba watarana sai labari." Hibba ta zaro ido kafin ta ce"Mimi na da ciki? Sai ya gya a mata kai, sai kawai ta saka shewa har suna tafawa da Mu'azzam a fili ta ce wa ya ga Yaya Mansoor da a akwai shan kallo, Aji baya jin kunyar fa an Mimi da na ciki shi a ganinsa abun alheri ne miye kuma na oye oye. Ya na nan zaune ya na uba sa onnin sa na kan WhatSApp da ya kwana biyu bai duba ba, har da na Makama ya tura masa hoton jaririyar, tun ranar da a ka yi haihuwar bai ma duba ba kuma ko barka ma bai kirasa ya yi masa shima yana cikin wani hali alokacin. Sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa tunda Mimi ta dawo gare shi, a kasan hoton jaririyar da Makama ya turo masa ya yi tagging ya rubuta" Allah ya raya, nima nan da lokaci ka an za'a haifa min irin ta ko irin shi a gidana." Ya gama rubutawa kenan ya ji bu e kofa, Ya juyo sai ya ga Mimi ce ta yi wanka ta saka rigar barci riga da wando masu taushi, ba ta kalle shi ba ta nufi jakarta da ledan mganinta ta auka ta juya kenan ta ji ya ce"Tuwon fa? Ko ba za ki ci ba ne? Ba ta juyo ba a sanyaye ta ce" Na oshi." Daga haka ta yi shigewarta aki, yana jinta tana saka key sai kawai ya yi zaune yana bin akin da kallo, tun bayan auransu ba su ta a raba aki ba, ko da sun samu matsala ba ta kai su ga raba makwanci amman yanzu kan ya san bashi da gaskiya shi ya sa ya kasa wani motsi. Zai jure har sai ta sauko ya godema Allah tunda Inna ta ba shi matarsa. Haka ya zauna ya ci tuwon nan sosai leda aya ya rage kawai sannan ya tattara komai ya maida kitchen miyar ya saka ta acikin Fridge ya kashe komai na falon sannan ya shiga akinsa ya yi wanka ya yi shirin kwanciya sai ranar ya samu yin barci sosai da safe shi ya tashi ya buga ma Mimi ofa sai ya ji ta na tashi tunda ta yi masa gyaran murya, Mimi gasan uma ta ke yi ma Mansoor ba ta masa mgana ko zai yi mganan duniyan nan daga eh sai a a ne, Tunda ta dawo za ta yi masa abun karyawa da na rana da na dare, a baya in ta ce ya zo ya taya ta aiki sai ya ce shi ta na bashi wahala amman yanzu haka ya ke zagewa ya na shige mata da faman nacin da me zai taya ta sai ta ce bakomai, har girkin ya ce ta daina yi tunda ta na da juna biyu, itama fa haushi yake ba ta tunda har bai yarda da ita to ba ta ga amfamin soyayyar dake tsakanin su ba. Sannan duk shi ya ha a mganar cikinta har Mommy sai da ta ji,Hajiya da Baaba uwani sun zo dubata, ta ji sauki sai dai kasala da jiri take fama da shi da tsinkewar miyau sai zazzabin dare, ba ta koma aiki ba amman Rukayya ta zo dubata, kuma daga can ma'aikatansu ana ta kiranta ana gaisheta. Jaheed ya kira ta sau biyu shima bai samu natsuwa ba sai da ta ce masa ta koma gidanta sannan ya samu salama har ya na cewa"Kina ganin kiran ma da nake yi miki ba matsala? Kai tsaye ta ce"Kada ka damu ba zai kara kuskuran da ya aikata ba, ko ba soyayya kai shakikina ne saboda haka bai isa ya hanani mu'amala da kai ba." To ai bai ma ga fuska ba,Mimi ko da yaushe fuskarta a kirne kuma ba ta son ma kallon shi in zai fita ta ce masa a dawo lafiya in ya dawo sannu da zuwa ta yi masa duk abin da yake bukata ta shige aki ta kwanta. Ko zai yi ta mgana ba ta amsa masa, Saboda dai ya saka su fita ya ce ta shirya su je barkan matar makama. Jin gidan Bibi ne ya sa ta shirya suka je da daddare suka yi mata barka an