Sashe 19
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haifa a tsakaninsu, Mu'azzam ya yi mirmishi kafin ya ce" Shi ya sa har gobe ba ni da kamar ki Inna ta, Allah ya kara miki lafiya da tsawon kwana." Suka amsa da Amin gaba ayan su, Itama ta amsa da Amin tana fa in" Nima ai bani da kamar ka an Inna Allah ya cigaba da tsare min kai a duk inda ka sanya kafa Allah ya yi maka jagoranci.' Cikin bayyana farinciki ya amsa da Amin lokaci aya yana kara fa in " Inna in na samu ku i zan kai ki Makka kafin ki mutu ke da Baba za ku je ziyara dakin Allah in sha Allahu." Gaba ayansu suka amsa da In sha Allahu Allahu ya sha. Inna Meri kamar ta yi kuka ta ce"Amin Amin Allah yasa muna da rabon zuwa, Baban Inna shima kullum zencen sa kenan Allah ya cika muku burin ku na Alheri" Mu'azzam ya ce"Mun fara magana da shi, Inna suprice za mu ba ku in sha Allahu." Yan'uwan suka taya Inna da amsawa da cewa Allah ya nuna mana lokacin. Hira suka cigaba da yi suna hirar su Walida ta je ta zubo ma Mu'azzam anwake ya zauna yana ci lokaci bayan lokaci yana tsoma bakinsa cikin mganar an'uwansa mata. Inna ya kallah sai faman wahala take yi da yara iyayensu na gefe suna hiran su ko ajikinsu. Cikin fa a ya kalle su yana fa in " Wai don Allah Nanny mai reno kuka mai da inna? tunda kuka zo gida nan ina lura da ku kowacce ta sauke a'yanta sai Inna ke ta faman wahala da su." Bintu ta ce"Ai sun fi son renin Innan ne ni fa ba domin Bashir ya ce a'a ba da tuni na dawo da su Hassan wajen Innanmu na gaji wlh." Hararanta ya yi kafin ya ce"Dole ki kwaso ki kawo mata mana tunda kin samu jaka ko ita ta ce ki je ki haihu." rufe baki Bintu ta yi tana dariya Yaya Amina na gefe ta ce" Inna fa ke son kiriniyan yara nan, ko zuwa mu ka yi ba mu zo da su ba sai ka ji ta ce kuka bar iyan ga a gida ba ku zo min da su ba" Inna na yar dariya ta ce"Kyale su an Inna rai ne ya kaini, yau in da ba na raye wajen za su je? Wata rana ba za su ganni ba gwara su mori kakar ta su tun yanzu." Har suna ha aa bakin wajen fa in"Ba yanzu zaki mutu ba Inna." Yaya Halima ta kar e da fa in"Ita Inna daman akwai kiran mutuwa ana zaune lafiya." Mu'azzam kuma ya ce"Inna sai kin auki an Yaya Mansoor ko arsain sha Allahu." Inna ta ce"Allah yasa, amman na cire rai da ganin Auran Baban Inna, ganin auransa da ya'yansa ai sai mai yawan rai tunda na ga ba shi da niyyan auran kwata kwata." Mu'azzam ya ce"In sha Allahu zai yi Inna mu ta ya sa da addu'a don Allah." Inna ta sauke numfashi kafin ta ce"Addua'armu kullum ba ta yankewa a gare ku, Allah ya sausasauta masa wannan zuciyar ya sanya masa salama acikinta." Suka amsa da Amin gaba ayan su Yaya Amina tace"Nifa ina tunanin yarinyar nan ce har yau ya kasa cire ta acikin ransa." Yaya Halima ta ce" kike gani? Yarinyar da ya zo ya tsani jin sunanta. Ranar Babansu Khairi na kallon labarai nake gaya masa Mansoor ya sota tun tana matashiyarta a zamanta hannun kakarta sai dai sun rabu da jimawa, itama fa ba ta yi aure ba har yanzu" Bintu ta ce"Ba ta yi aure ba mana, amman fa tana da kyau ga iya kwalliya ni dai wlh Saboda ita nake kallon tashar su har ga Allah tana burgeni kuma sun bala'in dacewa da Baban Inna." Inna na jin su duk ba ta yi mgana ba sai da ta nisa kafin ta ce"Ba wanda yasan abin da ke zuciyarsa, ba na tunanin ita ya ke jira saboda ai shi ya fara yanke alaqa da ita ko bayan dawowarmu Mu'azzam kai ka fa amin tana ta kiransa a waya ya auka sannan shi ya yanke sauran alaqan da ta rage tsakanina da kakar yarinyar nan. Tun daga lokacin ban kara taka kafata gidan ba itama Hajiya ba ta kara nema na ba, abu ne ya riga ya faru sai a manta baya a fuskanci gaba kullum ya zo nan babanku zai zaunar da shi yana masa nasihan hakuri da rayuwa sai ya nuna kamar ya ji ammh sam Baban Inna ba'a gane in da ya dosa shi dai wallon nan da ya saka gaba ita ya rike bansan kuma me yake tunanin ya mai da rayuwarsa ba." Inna Meri ta arishe fa a cikin bayyana damuwarta Yaya Amina ta dafa kafa arta lokaci aya tana fa in"Bakomai Inna, zai wuce in sha Allahu Baban inna zai yi aure har ki ga ansa" Bintu ta yi karaf ta ce"To ai abun haushin ma ko budurwa ba shi da ita." Mu'azzam ya yi jim kafin ya ce"Ai ina jin tun bayan rabuwarsa da Fatima Baban Inna bai kara son wata mace ba, ban jin ma mata yanzu suna burgeshi ta sauya shi fa fiye da tunanin ku, yanzu haka abokan mu sun gaji da min korafi sun hakura ana gari aaya sai su yi wattani ba su gan shi ba ya koma rayuwar ka aici abin da na fahimta har gobe abun na ranshi ya kasa mantawa ne." Yaya Halima ta ce"Nima abin da nake tunani kenan, cire abun a ranshi zai taimaka masa wajen fuskantar wata rayuwar a gaba." Mu'azzam ya ce"Yau ai wajen sa zan kwana zamu tattauna Allah yasa ya bani damar haka." Inna Meri ta amsa da Amin a samam labbanta har aka kira mangariba suna tattauna abubuwan da suka faru a shekarun baya ne. Kiran sallar Mangariba ya tada su Mu'azzam ya yi alwala zuwa masallaci su kuma matan suka yi na su agidan. Yaya Amina ta fara tafiya tunda ta fi su nisa, Yaya Halima kuma daga baya Bintu dai har sai bayan Sallar isha'i da Baba anjuma suka dawo tare da Mu'azzam da Auwalu. Har akinsa ta bi shi suka gaisa Magajiya ke da miji sai kuma abin da Baba Danjuma ya gani ruwa ma Inna Meri ce ta kawo masa mai sanyi tunda tana da aramin firiza a akinta na Yaya Halima ne da mijinta ya siya mata Babba sai ta kawo mata wannan. Sai da ya sha ruwan ya ji ka ma oshi acikin ransa ya yi saka ma matar kirki irin Meri albarka yana tuna karamcinta a garesa tun na tsawon shekarun da suke tare. an Biyun Bintu suka hau jikinsa suna wasa yana dariya yake fa in"Ku yi min a hankali kar ku arisa ni domin na ga kuna ji da karfi." aka saka dariya gaba aya, Auwalu yace"In na kalle su sai na tuna yarinyar nan Bintu ai itama ta yi rashin jin mgana, ba domin Mansoor na tsawarta mata ba da sai Allah." Bintu ta tura baki kafin ta ce"Haba Yaya Auwalu yaushe na kai yaran nan rashin ji." Mu'azzam ya ce"Kin fa yi Bintu ai har gobe baki daina ba sai dai in yan abun naki ba su motsa miki ba." Tura baki ta yi tana fa in"Baba ka gansu ko? Ka yi mu su mgana." Baba Damjuma yace"Ku bari mana Fatima Bintu sunanta mai daraja ne babu ruwanta da rashin arziki." Nan fa suka yi ta wasa da barkwanci har Bashir ya zo tafiya da Bintu gida Inna Meri tun azu ta yi mata mgana ta tafi gida ta ce ita fa a kusa ta ke daga zuwa gida Inna ta fara cewa ta zo ta tafi, Ahalin tun safe ta zo ta riga kowa ma zuwa shi ne take cewa ba ta da e da zuwa ba Inna na koranta gida tunda ta ji haka sai ta kyaleta ta sanya mata ido da kila Baban Inna ya zo ne shi ne dodonta yana cewa me take yi har dare ba ta tafi gida ba? Jikinta na rawa zata ha anta ta wuce tana tura baki iyaka dai ta kwana biyu ba ta zo ba in Inna Meri ta aika walida a duba ta sai ta ce tana nan lafiya ai Baban Inna ne ya koreta kuma a gaban inna ba ta yi mgana ba. Sha'anin Bintu ai sai ita iyar mace ce irin Mansoor wasu Lokacin suna da kamceceniya ta bangaren hallaya. Ko domin suna matsayin uwa aya ne? Mu'azzam sai wajen tara da rabi ya bar gidan nan zuwa Tunfere gidan Mansoor daman ya tura masa sakon in bazai zo ba shi zai je Camp ya kwana gobe suna da morning trainig shi ya sa ya yi ma su Inna sallama da Baba ya wuce tare suka fito da Auwalu ya rage masa hanya ya sauke shi a gidan shi sannan ya wuce. Lokacin da ya isa wayar Mansoor ya kira ya ce masa ga shi a waje, sai da ya ata lokaci sannan ya fito ya zo ya bu e masa get ya shiga da motar Ciki ya yi parking in ta kusa da ta mai gidan. Yana tsaye a bakin falonsa daga shi sai gajerun wando, ba nepa akwai kuma zafi a garin shi ya sa ya zauna haka, bai koma ciki ba har sai da Mu'azzan ya bu e bayan motarsa ya auko karamar jakarsa ya shiga falon sannan ya maida kofar ya rufe ya bi bayan sa. ******* Dukkansu sun sake wanka, Mansoor daman baya shiri da zafi sai ya yi wanka sama da sau hu u a dare aya. aramar katifan Mansoor suka kwanta dukkansu, shi Mansoor filo bai dame shi ba sai ya ba ma Mu'azzam ya dora kanshi a saman matashin, daman ya saba kwana in dai ya shigo garin tuni akinsu na samartaka na gida su ka bar ma Saddiqu yanzu shima yana okarin siyan fili ne ya fara ginin muhallin da za su rika sauka shi da Hibba in sun zo garin. Suna kwance Mu'azzam na ta Juye juye Mansoor ya ce"Kana jin zafi ne? duba bayanka akwai mafita sai ka yi amfani da shi." Mu'azzam ya ce"Gaskiya ya