← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 208

Sashe 73

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gane ba, Sannan akwai bukatar sanin muhallin da Mimi za ta zauna domin sanin yadda za'a kawata ma shi dalilin haka ya sa Hajiya ta kira Inna Meri ta yi mata mgana duk sai Inna Meri ta ji ta muzanta domin Baban Inna bai kara wani motsi ba tun bayan saka ranar, sai da Hajiya ta yi mata mgana ta saka a ka kira mata shi a waya ta masa mganar dangin Mimi suna bukatar son ganin a inda arsu za ta zauna. Sai ya nuna mata kamar ya sha'afa amman Auwalu zai kawo ma'aikata za su zo su duba akin domin ganin abunda ya kamata tunda daman akin Silif kwai akayi ba simimti ba Komai sai kofa kawai. Da yake Auwalu na aikin gini shi ya saka a kan gaba shi har ga Allah ya auka wani waje za'a gyara a gidansa sai ya jii aikin a cikin can cikin gida ne. Ba wanda ya sani sai ganin ma'aikata aka yi sun zo har lungun Inna Meri sun duba aki sannan sun yi lissafin abubuwan da za'a kashe gaba aya. akin ciki da falo ne amman falon arami ne ciki ya fi girma, a daran ya tura musu ku in aikin washegari sai kayan aiki da Ma'aikata shi kan shi Auwalu ya sha mamaki lokacin da Mansoor ke sanar da shi Matar da zai aura ce za ta zauna a kusa da akin Inna Meri shi kuma ya sanar da Magajiya da ta yi masa mgana tunda shine enginer ginin shi ya kawo ma'aikatan. Ai sai bala'i ya tashi a cikin gida har da su Baba Sani a cewar su ai Mansoor ba shi da gado a gidan da zai ce anan gidan zai zauna, Magajiya kuma a tsakar gida take ta bala'i da jaraban cewa Auwalu ma sanda zai yi aure hana shi zaman a gidan Baba anjuma ya yi amman saboda shi ba adali ba ne ya auki aki ya ba ma an so kuma Agola har ta na cewa yau ita ta ga rahin godiyar Allah ina gidan da aka ce ya gina? Bayan ana nuna shi mai ku i ne amman ya are da za ma a gidan da ba shi da gado aciki itama nan ta ce sai Baba anjuma ya fitar ma da Saddiqu shima akin da zai zauna domin uban kuturi ya yi ka an Inna Meri ko fitowa ba ta yi ba daman abunda ta guda kenan amman shi Baban Inna ta lura fitina acikin jininsa take yi har jin da i yake yi ya auko musu fitinar da ta fi karfinsu. Fisabillahi in ba nenan fitina ba, da gidan ka da komai me zai kawo ka zama a inda ba ka da hurumi? Baba Danjunma dai ya kashe mgana ya ce bangaren Meri da na Magajiya duka mallakinsa ne domin a shekarun baya kannen nasa su ka saida masa da rabi rabin gadon su a gidan shiyasa bangarensa ke da girma, in da suke ciki a yanzu nan ne ha nsu. Maganar aki kuma ya ce ya ba ma Mansoor halas makal wanda ya isa ya hana Ita kuma Magajiya ya ce mata shi bai hana Saddiqu zama ba in ya ga wajen zama sai ya zo shima ya zauna ga fili ga mai doki, ba Magajiya ka ai ba hatta anta Zuwaira da Jummai suna ta bala'i akan suma Baba Danjuma ba ya yi musu adalci. Daga karshe su Baba Sani suka ce tunda dai gidan yake so za su fita su bar masa gidan sai su koma wanda ya gina tun da kamar sun ga nan in yake sha'awa shi fa gogan ma duk bai zo gidan ba a satin sama su na shirun zuwa Kano pillas za su buga wasan sada zumunci a tsakanin su suna can suna fama da traning tare da shirin su. Inna Meri ce ke da hakuri kunsan kullum cikinyada mata mgana ake yi a cikin gidan nan to ya za ta yi? daman ance ai an kuka ke ja ma uwarsa jifa ita dai Baban Inna ya gama ja mata duk wani tozarcin duniya. Bai kuma zo gidan ba sai bayan sun dawo daga kano, wannan karon an tashi wasa biyu da aya ne, Kano Pillers ta doke su da ci aya san da ya zo an gama komai na akin sai abunda ba'a rasa ba har tayels an saka Inna Meri ta dawo musu da aiki baya domin tun yana Kano ta kira shi tace sai ya yi ma Mimi tiolet a cikin aki da farko cewa ya yi ta yi amfani da na su Inna ma, Inna Meri ta ce sai ta ci masa mutumci in bai shiga taitayinsa ba, Umarni ne ba shawara ba a yi ma Mimi makewayinta acikin aki har da kitchen. Dole akunan aka rage musu girma daga cikin uwar akin aka Yanki makewayi na bayan gida da na wanka a ha e, sannan daga karshen akin aka iri aramin Kitchen in da Inna Meri ta ce sai an yi, duk domin ta tsira da mutumcinta amman a gatan Mimi tafi arfin wannan wajen da Aji ke neman sakata aciki. Cikin Sati uku aka gama komai har fenti da saka wuta, sannan sai aka ha e gidan gaba aya aka yi masa sabon fenti har akunan su Inna Meri da uwar tsiya Magajiya bangaren su Baba Sani ne bai kai ga su ba, suna ta kunkuni duk da akin ya yi kyau tun da dalilin Mimi shima Koridon in shashen Inna Meri aka kankare shi aka yi masa Interlock aki ya yi kyau dai dai na zaman yar talaka amman ba Mimi ba. Su Amina duk sun zo sun ga waje ba wanda dai ya yi wata mgana amman a ransu suna auna yanayin da dangin Mimi za su nuna in suka zo su ka ga in da za ta zauna Bintu kuma ta na can tana Uban gayya a anguwa ita a dole yayanta zai yi aure zai auro mai aikin gidan talabijin in nan yar gayu Mimi. Inna Meri duk ta bi ta damu amman shi gogan ko a jikinsa a ce za ka yi aure bayan Sadaki ba za ka yi komai ba, har ta da kayan lefe ma ba shi cikin tsarin Mansoor. Kundunbala Inna Meri ta yi ta kira Hajiya ta sanar da ita an gama gyaran za su iya zuwa su ga wajen zaman Mimin daman kuma su ake jira. Sai Hajiya ta yi mgana da su Mama tunda su ne a hakku su je su gani. Mommy ma an sanar da ita ta kuma sanar da Khadi da Madiha, Madiha dai tac e sai satin biki khadi kuma tace da wuri za ta je gombe saboda ta ga in da ma Mimin za ta zauna. Dalilin haka yasa Hajiya ta ce a jira ta sai da ta zo sai aka shirya zuwa gidan da babar iyar Yaddiko sai Mama da Anty su uku kawai Hajiya ta ce sun isa ai ganin waje ne kawai ba wani abu ba. Ba su san gidan ba watance Hajiya ta yi musu bayan ta kira Inna Meri da kanta ta fa a mata masu ganin aki suna tafe, Inna Meri da rawan jiki ta saka Walida ta yi gyare gayren waje aka tanadar musu da ruwa lemu, Khadi tun da taji sunan gidan wai gidan Wanzamai take ta zagin Mimi acikin ranta Tabbas gidan ba oyayye ba ne sun gane watance sannan kuma sun yi tambaya, farat aya sai ga su a kofar gidan ba laifi ai an gyara gidan sai dai ai ba kamar in da Mimi ta ta shi da rayuwarta ba. Khadi ta saka wani katon gilashi da ya kusa rufe mata rabin fuskarta sai faman kallon mutane take aya bayan aya. Magajiya dai na tsakar gida ita suka fara tambaya ta nuna musu lungun Inna Meri su ka fara isa can. Sun samu tarba sosai tunda Bintu ma ta zo gidan Mama ce kawai da Hadiza su ka zauna Khadi a arare take ta na kare ma ko'ina kallo charting take yi da Madiha tana Labarta mata abunda ta ganin ma idanuwanta a inda a ke tunanin Mimi za ta zauna. Mama ka ai ce ta sha ruwa daga nan su ka ce sun zo ganin aki ne, Inna Meri kunya ya hanata zuwa sai dai ta ce Bintu da Walida su kai su akin, ga shi dai sun sha Kofofin alfarma tunda ma su tsada aka saka amman suna Shiga wajen Khadi ta duba ciki da waje Tsab sannan ta kalli Bintu kafin ta ce"Amman akin da Mimi za ta yi kiyon kaji ne in ta zo ko? domin ya fi kama Keji ni a wajena" Bintu da ya ke itama a ce dariyan ta saka kafin ta ce"wani kaji? In da dai amaryan za ta zauna ne ki duba da kyau." Khadi ta saki tsaki kafin ta ce"This is Serious."! Kawai sai ta aga waya ta kira Madiha Vedio call tana nuna mata akin Fa i take yi"Sisto ta ya ni gani? da me akin nan ya yi miki kama? Ta fa a ta na zagaya akin tana nuna ma Madiha ita kuma ta ce aki kamar akin kwanan sauro ai ko dabbobi ne, akin nan ya yi musu ka Bintu da Walida na gefe suna kallon ikon Allah hatta Mama wajen bai yi mata haba dai kamar zai saka kaza aciki Haka Anty Hadiza ma sai da ta ce" Gaskiya wajen ya matse da yawa ko iskar kirki babu." Mama ta ce"To ai karshen gida ne fa" A cewar su ko duka aku nan aka ha e ba zai iya aukan ko da kayan kitchen in Mimi ba ne ballatana wani aramim Kitchen kamar na kiyon Kaji da zabbi. Madiha ta ce a auki Video a kai ma Hajiya sannan Khadi ta tura ma Mommy ta gani, Mama ma ta ce za ta tura domin ta gwada ma Sanata ita kanta abun ya bata haushi haba ai tuwon girma ai miyarsa nama. Khadi ba ta da mutumci kusan duka gidan sai da ta auka a Video yanayin yadda su ka fita yasa Inna Meri tasan ba su ji da i ba, Bintu da Walida suka zo
Chapter 73 · 0% Book details