← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 208

Sashe 85

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

20k ya ba su yace sauran zai sha mai ne, amman zai yi musu sa o suka kar a dai kamar ba su gode ba kadahan kadahan ya na sallaman su sai ga Auwalu ya zo shima da na shi matsalolin wai jari ya ke so, so ya ke ya kama wata sana'ar tunda aikin ginin sai a Hankali, Mu'azzam ya bashi ha uri da cewa bashi da ku i yanzu amman da zaran ya koma duk yadda ake ciki za su yi mgana ta waya, duk da Auwalu yayansu ne duka gidan Zuwaira ce kawai ta girme shi, Amman haka ya ke ta yi ma Mu'azzam godiya domin ba zai manta da shi ba, shi da Mansoor suna taimaka masa sosai ansa ma da aka koro daga makaranta ba ku in da zai maida su, Mansoor ne ya gansu suna garamgaram a gari ya masa mgana shi ne ya fa a masa, acikin kwanakin ya biya ku in makarantan aran su ka koma makaranta. Saddi anin sa ne kuma ba laifi ya na samun ku i amman yana yashin ya taimaka masa Allah na tuba ko magajiya ba ta san fa i ne amman ko ita ba wani abun arzi in ya ke yi mata ba, yanzu dai gaba aya hankalinsa ya tattara shi wajen auran da ya ke shirin yi, kuma Magajiya ta na mganar shima a gidan zai gyara ya zauna kuma ya amince amman shi a ganinsa in dai kana da rufin asirinsa mai zai sa sai ya zauna anan gidan? Suna tunanin Mansoor ne, kuma shi ko yau ya ga dama zai iya tashi ya koma gidansa, ko kuma ya kama hanya a wani wajen duk ya na da ku in da zai yi hakan. Duk suna ofar gidan har su Mu'azzam su ka aga ya so daga nan ya yi wucewarsa ne amman sai Baba anjuma ya ja shi suka koma cikin gidan tare a akin sa suna ta hira na wani lokaci har sai da rana ta aga sannan yace zai fita yau akwai inda za shi, shiyasa ya yi masa sallama ya fito dalilin da yasa ya arisa akin Inna Meri ya shiga kenan, Duka suna cikin akin suna karyawa da kunu da osai, ya na shigowa Inna Meri ta ce ko a zubo masa ne? Ba gaddama ya ce eh saboda ko jiya da daddare da yunwa ya kwanta. Nan Inna Meri ta saka Bintu ta samu kofi ta zuba masa kunin osan kuma a wata karamar kula, zama ya yi a saman cafet in Inna ya fara shan kokonsa lokaci aya kuma ya na ha awa da kosan shi, ya na jin su suna ta Hiran su amman baya saka musu baki. Ya na akin ya ji Inna Meri na fa in kafin su tafi su taya ta ta raba wannan kayan fulawan su ma su ibi nasu sauran a raba ma mutanen gida. Bintu ta yi zaraf ta ce" Inna ni gaskiya ki ibar min nawa da yawa, kinsan ina da kishiya gwara na je na kai mata na tashi kanta tasan mu dangin mu ba matsiyata ba ne." Sai da ta fa a sannan ta juya su ka ha a ido da Mansoor ko hararanta bai yi ba, amman sai da ta sha jinin jikinta shi ko a lokacin ma ya na wani tunani ne, bai ma bi ta kan mganganunta ba amman ita sai ta tsargu. Su Amina nata yi mata dariya, Inna Meri na gefe ta ce" Walida ko za ki je ki duba min Binta ne? Har tara ta gota ba ta tashi ba." Halima tace"Inna Amarya ce fa, ko sha biyun rana ta kai ba ta tashi ba lokacinta ne" Amina ta amsa da cewa" Ga kuma gajiyam biki kuma ki yaleta Inna har sai ta tashi." Inna ta ce"To daman kada abun aryawan nata ya huce ne." Bintu ta ce"In ma ya huce Inna sai a yi mata wani ba shike nan ba." Yana jin su amman sai ya yi kamar bai ji ba, bai gama cinye kosan ba amman ya shanye kunun duka sannan ya mi e yana fa in" Bari na je Inna" Inna Meri ta ago ta na fa in" Yau dai gida zai watse, su ma da ka gansu nan zuwa anjuma za su koma gidajen su kada ka bar yarinyar nutane da suka baka amana ita ka To kawai yace ya fice daga gidan ya na wani tunani har sanda ya fito saida ya ara kallon ofar akinta sannan ya ka ai kai ya fice daga gidan gaba aya motarsa ya shiga ya bar anguwan ya na hanya Ahmad ya kira shi yace ya au hanya sai ya yi masa fatan ssuka lafiya yace ai Mu'azzam bai jima da tafiya ba. Mimi ko ba ta san duk abunda ya faru a gidan ba, ta na can ta na barcin gajiya daman ga shi ta na hutun sallah, ba ita ta tashi ba sai wajen aya da rabi na rana shima Inna Meri ce ta damu tace shurun ya yi yawa a buga mota ofa aji lafiyanta. Shine Bintu ta je ta fara mata knooking can acikin barci ta ji ana bugun kofar saboda ma ta samu hutu wayarta ma a silet ta sakata shiyasa su khadi suk yi ta kiranta ba ta sani ba. Dakyar ta iya saukowa daga kan gado saboda jikinta ke yi mata ciwo ko'ina, daga ita sai rigar barci sai kawai ta saka wani dogon hijabin da take sallah da shi jiya ma suka zo mata da shi acikin kayanta ta zura silafis inta na yawo cikin aki daga gida ta saka aka zo mata dashi ta fita zuwa falo ta bu e kofar ta le a sai ta ga Bintu wace ta yi mata Mirmishi. Itama sai ta maida mata martanin mirmishin, lokaci aya tana sakin hamman barci. Bintu tace"Sannu, kin sha barci." Mimi ta sauke Ajiyar rai kafin ta ce" Ke dai bari gajiya ce a jikina sai a hankali. Ki shigo ciki mana." Ta fa a ta na ko arin wangale mata ofar sai Bintu ta girgiza kanta lokaci aya tana fa in" A'a daman Inna ce ta damu sai an duba ki ko kina lafiya, kuma fa mun gaya mata lafiyan ki, lau kawai kina barcin gajiya ne." Mimi ta ji kunya sai ta dukar da kai kafin ta ce"Laa ki fa a mata lafiya kalau bari na yi wanka sai na zo na gaisheta." Da Bintu ta tambaye ta ko ta na da bukatar ruwan zafi sai tace a'a akwai a fulas zai ishe ta daga haka suka yi sallama Bintu ta wuce ita kuma ta maida kofa ta rufe. Tun da ta riga ta tashi sai ba ta koma barcin ba, tiolet ta shiga ta fara wankewa duk da bai yi datti ba jiya ma ai Asma'u ta wanke mata. Sannan ta Juye ruwan zafin cikin Fulas ta yi wanka da shi bayan ta fito kafin ta shiryya sai da ta gyara gadon sannan ta zauna ta shafa mai ka an saboda an fara zafi zafi sannan ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da ta ji stone work rigar ta yi mata kyau a jikinta masha Allah. Tana cikin aurin ankwali ne ta ji ana sake buga mata kofar sai ta yi saurin aurawa sannan ta fita zuwa falo ta bu e kofar sai ta ga Walida rigi rigi da faranti cike da kayan tee sai kuloli guda Biyu wai kayan aryanwan ta ne ta amsa tana godiya Walida tace inna ta ce in ta na bukatar wani abu ta yi mgana Sai Mimi ta ce ba ta bukatar komai ta gode. Daman yunwa ta ke ji, a falo ta zauna ta arya, Koko da kosai ta gani ai kamar an saka ta a Aljanna ko tea in ma ba ta sha ba, ballatana su wai in da aka yi mata gwaninta aka soya mata, har aukan sauran kokon ta yi ta saka su cikin karamin fridge inta ta ce na anjuma ne osan kuma ta kai shi uwar akinta, domin Mimi na son kayan abincin gargajiya duk da ba ta wani iya su ba, girke girken zamani ta fi iyawa suma saboda waya ne ta na shiga cooking clasess har ba ta san iyaka da kuma ma banking in kayan fulawa. Bayan ta gama ta natsu sai ta auko wayarta ta ga su khadi sun kirata har da Madiha, Mommy ma ta kirata sai ta fara kiran Mommy shine ta ke fa a mata, ai yan'uwanta ne za su tafi shi ne suka kirata su yi mata sallamaa. Cikin Mamaki Mimi tace" Har da su Dr. Sun tafi suma? Mommy ta ce"Eh ai shi jirgin safe ma suka bi, daga shi sai Madiha Ita Khadi tafiyar mota ce." Mimi tace" Na auka za su zo mu ara yin sallama." Mommy ta ce" Sun ce ai kun yi jiya, nima gobe nake son na koma saboda aiki na sannan ina so Asma'u ta fara karatu" Sai Mimi ta fara mata shagwa an don Allah kafin ta koma ta zo ta ganta sai Mommy ta ce ta bari za ta yi ma Hajiya mgana sai su taho tare. Jin haka yasa Mimi ta ji da i, ta ce ma za ta kira Hajiyan da kanta ta ro e ta. Bayan Mommy sai ta kira Madiha wayarta a kashe kila tun a jirgi bayan ta sauka kuma ba ta kunna ba. Sai ta kira Khadi ba ta auka ba sai ta kira mijinta Muhammad shi ne ya ce yanzu suka sauka kaduna Khadi na tiolet. Dr kuma ko da ta kira shi baya nan yana asibiti a gida ya bar wayarsa sai dai ta aiki ya tafi da ita sai dai ta gaishe da jawahir da ta ce ai ta ji sau i ta yi ta mata tsiya Amarya har ta ji kamshin amarci. Sai da ta gama wayoyinta gaba aya, sannan ta saka mayafinta ta auko takalaminta kalan mayafinta mai sau en tudu ta saka sannan ta fita falo ta auki faratin da Walida ta kawo mata ta fita da shi waje, ta iske Amina a ofar akin Inna Meri ta na girki su ka gaisa cikin fara'a
Chapter 85 · 0% Book details