← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 208

Sashe 66

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an Certificate na wata makaranta koyon na'ura da ta yi ne zuwa kuma ta ha aa kayanta da sauran su amman Dr zai sako min ita a Jirgi cikin Sati nan mai shiga in sha Allahu". Hajiya tace"Shikenan kin samu yar dudurwa Allah ya taya ki riko Murja ki yi ta hakuri kin ji ko? Ina miki fatan ki samu miji ki yi auran ki." Da Sauri Mommy ta kalle ta cikin mamaki sai dai ta asa mgana Hajiya kuma sai kawai ta kauda kai haba ai Murja da kuruciyanta ba za ta barta ta yi ta zama ba aure ba ita aikwai ma wani Tunani a ranta amman bari a gama da Mimi tukunna sai ta yi mganar saboda Murja kamar a ce a wajenta ba Suruka ba kamar yadda za ta so ma Yadikko rayuwa mai kyau itama haka za ta so mata. Azumi uku Mimi ta yi a jere na godiya ga Allah ranar da ta gama kuma ta saka Baaba Uwani ta Dafa abinci mai yawa megadi ya tara almajirai aka yi ta musu rabo ga ruwan roba ga lemun gora, amman wannan Sadakan tace ta na fatan ladan ya kai kabarin Abi ne, Mommy da Hajiya suka ji da i da ya ke ba ta samu tafiya a ranar ba saboda tsaikon Jirgi sai washegari Daddy ya zo sun yi sallama shi da su Mama Mimi na jin Anty na kara yin mganar Jaheed Mommy mirmishi kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Saboda Hajiya ta ce ta bar mganar a hannunta in komai ya dai dai ta ita za ta kira Daddy da Yadikko ta sanar da su. Mimi da Hajiya da Daddy su ka kai Mommy filin Jirgi ba su baro ba har jirgin su ya aga zuwa Abuja sannan suka dawo gida. Mimi ta sauya kaya ta wuce wajen aiki Hajiya kuma tana gida tare da Baaba Uwani, Sai bayan ta isa wajen aikin ne suka yi waya da Dr ta ce masa yanzu ba jimawa Mommy ta tashi zuwa gida sun yi dai mgana ka an kafin su yi sallama Saboda yace mata yana da tiyata yanzu. Dukkansu sai da suka kira har Khadi da ba sa wani shiri saboda sa onta ne waya goma sai sun yi fa a gwara ma yanzu bayan rasuwar Abi sun daina yawan Fa a da Juna ita kuma daman madiha yar jin kai ce kamar ba uwarsu daya ba yanayin rayuwarta ma ba daya ba ne da su miskila ce mai ra'ayin ri au kamar Abi kenan. Ita Khadi maganar Mimi ta dai dai ta da Jaheed su yi aure shi kuma Dr ya ce kada a takura mata tunda Abi ma da kansa ya ce in ba ta so ba za'a yi ba ita kuma Madiha yar ba ruwanta ne amman a cewarta Hajiya ce ta kara sangarta Mimi ita ta tsani goyon kaka sannan ta na bleeming in Mommy ne ta ce har da ita a kara shagwaba Mimi da sai abunda ta ke so shi za ta yi. Tunda bayan rasuwar Abi ana mganar Mommy taje can garin su ta auko wata saboda su zauna tare sai ta ga why not Mimi ta baro aikinta na Gombe ta dawo Abuja ta nemi wani aikin saboda ta zauna da Mommy ita fa a ganinta da a nemo wata duk da ba bare ba ne gwara Mimin amman sai Mommy ta nuna a'a ba za ta takura ma Mimi ba so on an so on dai, tun daga lokacin ta kauda kai akan lamarin Mimi tun da ta fahimci she has da Power ta bangaren Hajiya sannan Dr ma ba shi da zafi shima kokarinsa ma cewa yake Abi ya ce a yi mata abin da take so ne. Shiyasa ba dai kaga Mimi na tattauna wani abu da ya shafe ta da an'uwanta tunda ba mai iya fahimtar ta awayenta kenan Hajiya da Mommy sune ke ba ta karfin gwiwan akan dukkan lamarinta, A yanzu ma ko Rukky da su ke tare da jimawa ba ta yarda ta yi mata zencen Aji ba to mutumin da ta gaji da Jiran kiransa har ta fidda rai wayarta na tare da ita a koda yaushe ta ji kira sai ta auka shine sai kuma ta ga sa anin haka ya ce ga Shara insa ta ce ta amince amman shuru sai ta yi tunanin nemansa sai wata zuciyar tace meye na gaggawa Fatima? Kika yi jiran shekaru gomaa ma ballana jiran yan kwanaki? Tuna hakan kan saka ta sauya tunanin kiransa ko tura masa sa o har a chart ta jima ta na duba shi ba ta ga alamun ma ya na hawa ba amman tana ganin Status in su Mu'azzam wani lokacin ma suna gaisawa. Maimakon Aji ya ri a kiran ta Jaheed ne ya fara damun rayuwarta da Kira shi a munafarsa sai ya samu kanta ta amince sun yi aure ita kuma ta kasa iya ga ya masa gaskiyan bayan Aji ba za ta iya son wani namiji ba. Duk da dai yafi Aji komai da komai na rayuwa amman ita zuciyarta har gobe Ajin dai Mansoor Aji ba shi da na biyu a wajenta. Duk sai ta rasa mafita saboda ita ba za ta iya yi ma Jaheed wulakanci ba ai an uwanta ne ko Rukky mitan ta kenan ya kamata ta yi amfani da damarta ta rumgumi mai sonta ba Jiran wanda ba ta da masaniyar yana sonta har yanzu ko ba ya sonta ba. Ta na da kwarin gwiwan ba da amsan cewa har gobe Aji na sonta sai dai kila su ne idanuwansu ya rufe sun kasa gane irin tasirin da soyayyarta ke da shi a rayuwarsa. Koda yaushe suka yi waya da Mommy sai ta tambaye ta yadda ake ciki Sun yi magana da Aji ko ya zo? Sai tace mata a'a itama case dake hannunta mai zafi ne ba ta samun zama a gida shiyasa sai ba ta samun sararin yin wani tunani har aka auki lokaci ita kuma Hajiya ta ce a bashi lokaci ne ka da ya ga kamar sun dame shi. A haka har wata aya ya zo ya shu e ba Aji ba labarinsa sai Hajiya ta yanke shawaran kiran Inna Meri ta ji a inda matsayar su ta tsaya. ******* _Wednesday 05 July, 2022_ *10:54pm* Inna Meri na zaune saman sallaya a tsakar akinta sallar walha ta idar tana lazimi har barci ya kwasheta ba ta sani ba, ga casbahan hannunta ya fa ita kuma ta sunkuya tana ta barci Walida kuma daman tun safe ta yi sharan aki ta yi kaye kayen tsakar gida ta na kuryan aki wayar Inna Meri na hannunta ta na dannawa, waya ma ta gama yi da ita domin ta ha u da wani saurayi a wajen yin Jamb har ta bashi Lambar wayar Inna suna mgana ta nan. Game take yi sanda kiran Hajiya ya shigo wayar ta gane ta tunda da ita Inna Meri ta ba ma lokacin ta yi ma ta Saving da Hajiyar Shagamu. Da sauri ta diro daga kan gado ta yi falo ta na kwalama Inna Meri kira ita kuma acikin barcinta ta ji ana kiran sunanta sai ta firgigit ta farka. Da yake daman barci ba mai nauyi ba ne a zaune ne ta fara yin shi. Ta kara watsakewa da ta ji Hajiya ke kiranta a waya Walida ta aukan mata wayar sai ta cire hijabin jikinta da sauri ta kara wayar a kunne cikin mutumtatawa kamar yadda suk saba suka gaisa da Juna Inna Meri ta ce"Hajiya kin ji ni shuru ko? Abubuwa ne sai a hankali amman ina nan zuwa in sha Allahu." Hajiya dagacan bangaren ta ce"E, fa na ji ki shuru Meri tunda Mansoor ya fa i sharu ansa kuma Binta ta amince bai zo ba kuma bai kirata ba , kema daga bangaren ki ban ji wani mgana ba shi yasa dai nace bari na kira na ji yadda a ke ciki." Cikin mamaki Inna Meri ta ce" Sharu a ? Cikin sigar tambaya Hajiya ta amsa mata da cewa"E, sati uku kenan da ya yi ma Binta sa on cewa bayan Sadaki ba ya son wani bidi'a sannan kuma shara insa na biyu a tare dake yake so Binta ta zauna ni kuma nace ai bakomai za ki ri e Binta kamar a in sha Allahu." Inna Meri ta ude baki ta rufe yafi sau uku saboda mamaki acikin ranta dankari kawai ta ke fa i mamaki ne ko alja'abi ne ya kamata ta rasa kama ma rukunin da take cikin karin son jin ma mganar domin ta rasa makama ta ce"Tsaya Hajiya ban gane ba, wai a tare dani kamar ya ban gane ba? Hajiya ta ce" To ya na nufin a gidan nan za ta zauna tare dake mana Meri ko bai ga ya miki ba ne? Inna Meri ta jinjina kai kafin ta hadiye wani miyau mai kauri kafin ta ce"Ya kwana biyu bai zo gidan ba amman zan sa ka a kiramin shi yadda mu ka yi zan kira ki Hajiya." Da haka su ka rabu da Hajiyq Inna Meri ta sauke waya daga kunnenta. Kafin ta ha a da Ajiyar zuciya lokaci aya kuma ta ce"Uhm yau naga buruba da Iskanci." Sai kuma ta koma ta yi shuru wai Baban Inna ya na da lafiya kuwa? A wani gidan zai ijiye yar mutane? a nan gidan ya na da waje ne? Ko ya na da gado ne? Ko ya manta ba gidan Ibarahin sufi ba ne? fitinar yaron nan ta isheta ta ga take takensa ba zai barta ta huta ba. In ya manta matsayinsa bari ita ta tuna masa maras mutumci yaro kawai mai janyo ma kansa da mutane fitina yanzu wannan mganar in ta fita me za ta ce ma mutane? Yaro kawai ya yi ta janyo ma kansa tsiya da fatara ba shi da gida ne? Ko kuwa son ya ga iyakar mutane ita fa daman tasan da wata kasa haka Kurum Baban Inna ba zai yi laushi cikin sau i ba ashe tsiya ya shirya. Kyafci ta yi ranta in ya yi dubu ya aci Walida ta walama
Chapter 66 · 0% Book details