Sashe 79
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mimi, ga shi anguwan ba eutar Nepa akwai duhu sai dai a ka ri a amfani da fitilar waya ire iren su khadi suna kofar gida suna jiran su Mimi ba su ma kai ga shiga cikin gidan ba. Sai da su ka kariso sannan Dr. ya damka ma Inna Zainaba Mimi tunda shi ba shiga gidan zai yi ba amman sai da ya kare ma gidan kallo duk da acikin rukunin layin gidan ya samu kyakyawan gyara amman duk da haka gidan ya yi ka an a wajen zaman Mimi kama ta ya yi gidanta ya zama ita ka ai sai dai bai yi kuskuran saka wani abu acikin ransa ba, ya bi ta da fatan alheri da samun zaman lafiya na har Abada kuma shi dai ari bisa ari Aji ya burgeshi sannan yana da yakinin nan gaba wani ne a duniya ba ma kasar Nageria ba. Saboda duhu ba hasken wuta sai dai su khadi suka kunna fitilolin manyan wayoyin su lokacin da za su shigar da Mimi cikin gidan. Magajiya mugun halinta bai saka ta fita zuwa akin Inna meri ba, tana cikin akinta ta ga wucewar tawagan amaran an nata ma kaf suna bangaren Inna Merin domin tarban Amarya hatta Matar Auwalu kuwa budurwan Saddiqu ce da su ka zo azu ita da kanwarta ke zaune a falon na ta, Ko Mariya tun da rana rabon da ta saka ta acikin idanuwanta. In da ace akwai zaman lafiya da amana Magajiya za ta kar i Amarya amman saboda Sanin halinta ya sa Inna Merin ba ta fara ma tusa kanta ba. Cikin tsakiyar akin Inna Meri su Mama da Inna Zainaba suka dire Mimi wacce ta saka wata atamfa super ce mai kyau a jikinta akwai kalan ja shiyasa liyafan da ta yane jikinta da shi ja ne sannan takalmin kafarta ma, a cikin falon inna Meri akwai duka anta su Amina da Halima sai Bintu da Walida Hibba sai su Mariya jummai da Zuwaira har ta su Gaje da ya'yansu suna ciki, akin dai ya cika sai uban zafi tunda ba hasken wuta. Inna Meri da Yalwa sai Maman Bauchi ke zaune waje aya sai wata wacce take matsayin yayarta daga can Argugun ta zo, sai anwar mahaifiyar su Amina da tare da ita ake tun ana Jibi biki ta ke kwana a gidan Inna Meri. Sauran kuma daga can gefe Matar Mu'azzam ne Hibba da sauran an' biki na jiki jiki an uwan su Baba anjuma Kuma daman a ka'ida su za su kar i Amarya tunda an riga an aura aure. Mama ita ce kamar uba a wajen Inna Zainaba kuma kamar uwa Rukky na ma ale kusa da Mimi su Khadi suna daga Kofa a tsaye suna haskowa da Wayoyin su sauran kuma suna daga kofar akin wasu kuma sun bu akin Mimi suna cikin irin su Bibi saboda can akin inna ya cika ba ma wajen tsayuwa ballatana wajen zama. Mama ita ta fara mika wajibinta da cewa ga amanar arsu nan sun kawo domin Allah Inna Meri ta ri e ta bisa amana da gaskiya sun samu kyakyawan shedanta wajen Hajiya za ta yi ma Mimi rikon a ce ba suruka ba, Inna Zainaba ta kara da cewa Mimi kamar a take a wajenta tunda ta haifar mata miji kuma ta aura daboda haka duka anta ta ri e ta amana in ta ga kuskurre sun ba ta cikakken daman ta yi al alanci ta kuma tsawatar. Inna Meri cikin jin kunya ta ce ta kar i wannan girman amana in sha Allahu za ta ri e Binta amana da gaskiya kamar sauran anta bayan nan sai ta ce ga Ahalin dangin mahaifin Mansoor Yalwa ta wakilce su tunda mazan duk sun koma garin su matan dai suka bari sai an gama biki. Yalwa ta yi ma Mimi nasiha sosai kamar arta kafin ta gangaro kan wata gabar Inna Meri cikin Alfahari ta ce" Za ki ji da in zama da Meri domin macece mai ha uri da kawaici uwa ce goya marayu ta goya anta ta kuma goya an wasu nan akin akwai an mijinta ita ta ri e su bisa amana da gaskiya in ba ka sani ba ma ba za ka iya bambamce su da sauran anta ba, mun so meri domin mun yi zaman amana da ita mutuwa ita ta auke Yayan mu Ibarahim ta yi sanadiyar barinta cikin mu amman ba ta ya da mu ba duk abunda ya ta shi na sha'anin farinciki ko aka sin sa tana zuwar mana sannan Mansoor wajenta ya girma acikin wannan gidan kuma su ka yi masa kyakyawan ri o da tarbiya muna gode mata ba mu da kamar ta, Mansoor yaron kirki ne ba wai domin ya na an yayana zan yabe shi ba, ki yi masa biyayya iya iyawarki wallahi tallahi abunda yaro nan yake yi mana makwafin ubann shi ne ya rime mu ahalin sa bai kuma manta damu ba. Maraya ne da nahaifinsa ya rasu tun yana arami amman bai ta shi cikin maraici ba tunda mallam anjuma ya ri e bisa amana da gaskiya ina yi miki albishir da ki yi hakuri ki zauna lafiya da auran ki tabbaci nake baki ba za ki ta a samun matsala da kowa ba In sha Allahu." Bayan ta gama kanwar mahaifiyar su Amina itama ta yi nata jawabin. Maman Bauchi ma ta yi nata, kowa dai sai ya ce Mansoor na da kirki Rukky a cikin ranta ta ce wannam mara mutumci ne mai kirki tab lalle, Inna Meri ta ba da turare da cingam na saukan amarya maman Bauchi kuma ta Ha a da Dldubu goma su Amina suka ri a sakin gu a ana ta dariya ana shewa ana kuma addu'o'in zaman lafiya har Inna Zainaba suna wasa da Yalwa in da ta ri e hannun Mimi ta ce sun kar i amaryansu su ta shi su tafi sun gode. Ana ta raha da dariya Yaya Amina ta aga hannu sama tana fa in "Innar mu tunda iyaye sun yi na su nasihan a bar ma yayye bangaren su, muma muna da abun cewa." A ka kwashe da dariya Khadi da Madiha sun gaji da tsayuwa sai tsaki suke yi, tun kafin a bai wa Amina damar magana ta taso ta zo gaban Mimi ta aga mayafinta fuskarta ya bayyana hibba kuwa ta kashe mata idanuwanta da filita Rukky ta kare ta lokaci aya tana Fa in" Kuna kashe mata ido." Bintu ta yi zaraf ta ce"Ai ta zama tamu yanzu. Suka saka dariya har suna tafawa ita da Hibba, Mimi kanta na asa tana faman tsane hawayen Idanuwanta da tissue a gabanta ta zauna ta ri e hannayenta sannan ta ce su Halima su taso kafin ka ce me har da su Bintu sun zagayeta Yaya Amina da karfi ta fara mgana tana fa in" Amaryar mu wani sirri zan fa a miki amman kafin nan zan fara da baki Amanar anin mu, Mansoor na da kirki amman kila kafin wasu su san kirkin sa sun san akasin sa Nasan kinsan halinsa na zafin zuciya da kafiya sannan da ri o amman ke da kika san shi fiye da kowa in kika kiyaye masa za ki zauna Lafiya, ki ri e mana shi amana sabo da muna son shi muna kaunar shi, ki kuma so dangin mu saboda mu kaf inmu muna da son junanmu Inna Ita ce uwarmu ita ce komai namu ki so mu a yadda muke ki kuma bar mu a yadda muke. Sirri na farko shi ne mijin ki mai arzi i ne arzi in da mu an uwan sa muke ci, kada ki ga ya ijiyeki a wannan gidan ki yi wani tunani ba ma ke ba na san wasu daga cikin an uwan ki za su yi tunanin haka to ki sani yana da gidan da zai ijiye ki sai dai ba ya ra'ayi ne ya za i ya ijiye ki kusa da wacce ya fi auna ki gode ma Allah, ki yi amfani da damarki domin gyara zamantakewar ki sannan kuma ki sani shi fa me yi ne an dangi ne kuma gaba da baya, duk abunda kika gani yanzu kada ki yi amfani da shi ki yi amfanin da zahirin waye kika aura sannan sirri na arshe shi ne mijin ki na son ki. Wallahi tallahi yana sonki duk wanda ya ce baya sonki to ya fa i son ran shi so ne ya sa ya aureki ba komai ba." Yalwa na gefe ta yi karaf ta ce"Sosai ma nan wani irin ciwo ne bai yi saboda an hana shi ita ba, yaro nan kamar ba zai ara wata rayuwa ba Allah ya kaddara ke in dai ke ce matarsa saboda haka ki ri e maraicinsa domin Allah ku zauna lafiya." Khadi na gefe ta ce"Itama fa Mimin nan marainiya ce, an tasa ta ana ta ba ta amanarsa shi ma muna son ganin shi bisa adalci mu ba shi amanar nata shima." Dariya aka yi mata itama da gaske take yi har cikin ranta domin gani ta yi kamar suna da son kansu. Yalwa tace gaskiya a kira waya Mansoor ya zo shima an uwan Mimi su ba shi amanarta. Hibba ce ta kira wayar Mu'azzam ta ce ana kiran Yaya Mansoor daga cikin gida su a lokacin ma suna ofar gida gaba ayan su amman Aji sun rabu da shi tun a Studio sai dai shi Mu'azzam ya kira shi a waya a lokacin suna Camp ib su tunda ai suna da bami daga can jin kiran Inna ne yasa ko gidan da ya so ya wuce ya yi wanka bai samu dama ba sai ya taho kawai daga can Mashin in haya ya hau tunda mashin dinsa na gida sannan motarsa na hannun su Nasir. Jiran sa suka yi sai da ya zo sannan ya ga sun tasa shi gaba zuwa cikin gida abun sai ya ba shi mamaki har ya fara tunanin ko wani abu ne ya faru. Cikin ar damuwa ya kalli Mu'azzam yana fa in" Mu'azzam me ya faru a cikin gidan? Nasir ya yi karaf ya ce"In mun shiga za mu gani." Aji ya harare shi