← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 208

Sashe 117

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ne, ba kai ba ne." Ta fa a tana wani sosa saman giranta irin na rigima dai na mata. Kasala ara rufe shi ya yi, ba shi da mafita illah na bin abin da tke so domin in ta cigaba da yi masa irin wannan abun zai iya rumgumeta ya sa a alkwarin da ya yi masa kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" To na ji ni ne, daman ai ni sarkin yan laifi ne, me kike so yanzu? Kai tsaye ta ce" To ba ka ci abinci ba ka huta ba, kuma wai ka ce za ka tafi." Cikin kauda kai ya ce" Zan je gida na huta ne Mimi. Na gaji sosai ba ki ga daga tafiya nake ba? Cikin sanyin murya ta ce"Ga gado? Ba sai ka kwanta ka huta anan ba." Ta fa a tana nuna masa gadonta da ya ji shimfi un alfarma na kamfanin FHB CLOTHING Phone no 08034109622 Wtsapp no.08080266674 juyawa ya yi yana kallon gadon zuciyarsa na kai kawo. "Don Allah kar ka tafi, ka kwanta ka huta anjuma sai in tashe ka. Ka yi sallah sai kaci abincin ko? Kallonta ya sake yi, yana so ya ce A'a ne amman sai wata zuciyar tasa na jansa da ya amince mata. "Kaji Aji Nah...don Allah.." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Na ji shike nan,." Ya fa a yana kallonta asa asa,mSai kawai ya ga ta yi tsallen alamun murna saurin kauda kai ya yi saboda ji ya yi kamar ya jawo ta ya rumgumeta. Yana tsaye sai ji ya yi ta kama kokuwar kar an jakar hannunsa dole ya sakar mata kada ya ki ta saka masa kukan shagwa a. Wadrope ta bu e ta saka Jakar a ciki sannan ta dawo ta kara gyara gadon duk da a gyare yake sannan ta kalleshi tana Mirmishi kafin ta ce" Sir.." arare ya hau kan gadon daga gefe ma, ita kuma sai ta ariso kusa dashi ta ja bargo ta rufa masa daga Kafarsa zuwa ugunsa. Sannan ta kshe masa hasken akin ta fice bayan ta jawo masa Kofar lokaci aya tana fa in" A yi barci lafiya." Falo ta koma ta zauna tana mirmishi ita ka ai acikin ranta take jin wani irin sanyi da farinciki. Shi kuma har ta fice y na bin ta da kallo, jin sa yake yi wani iri, akin ya yi duhu sai karan fanka komai na akin kamshin Mimi yake da filon da zanin gadon da komai. Kwanciyar da ya yi yasa kasalan shi ta ara dawo masa sabuwa yana kwantar da kansa saman filo ya ji wani irin natsuwa na shigarsa. Duk yadda tunani ya so ya yi masa hawan awara bai samu muhalli ba,domin wani irin nauyayen barci ne ya kwashe shi mai cike da salama da farinciki a cikin sa. Barci ya yi sosai gashi barcin mai nauyi, kuma ita Mimi ba ta tashe shi ba daga karshe ma bayan ta gama latsan wayan ta gaji akin Inna Meri ta koma wajen Walida, da Inna ta tambayi Mansoor cikin kunya Mimi tace ya kwanta, inna Meri t ace ai ya kamata domin akwai gajiya ya a kwance ya na barci har azahar ta yi bai sani har biyu ta gota Inna Meri ta ce ma Mimi ta tada shi ya yi salla haka nan barcin ya yi yawa..ita kuma ba ta son ta shin sa tun da ya fa a mata da bakin shi ya gaji sannan yanayinsa ya nuna haka. Sai dai tana shiga ta ga bashi a saman gadon. Sai ta ji aran zubar ruwa a tiolet yasa ta san yanaa ciki sai ta fito falo ta bashi waje, shi kuma daman yana farkawa ya duba agogon wayarsa da ke gefensa ya ga biyu ta gota ya yi ta mamakin barcin da ya yi. Kasalan ta bar jikinsa sanman ya samu hutu shi ya sa ya sauko daga kan gado ya fa a tiolet ya auko alwala akwai darduma a nan saman side drower in gadon ya auka ya dai dai ci gabans ya ta da Sallah. Bayan ya idar ya da e zaune yana tunanin yau shi ne ya yi barci a akin Mimi abinda bai yi tunanin faruwar shi nan kusa ba. Yana zaune saman darduma Mimi ta dawo akin tana masa maganar abinci ta kawo nan ne ko zai fito falo? Sai ya ce ta bari ya fito falon kamar mai ciwon baki, bai tsammanci Mimi ta damu da shi haka ba sai da ya ga kayan tarban da ta ha a masa a falo ya zauna a kasa domin ta cire centre in tsakiyar akin ta shimfi a masa wani dardumaya zauna ta ha a masa abincin, da yake fav food insa ne shi ya sa ya saki jiki ya ci sosai kuma da ya ke ta ba shi waje akin Inna ta koma su ka cigaba da hira da Walida Shi ya sa ya samu damar ci ya oshi kuma ya ci abincin da ya jima bai ci kamar shi ba Tun bayan tafiyar da su ka yi in dai ba wajen Inna ya zo ba, abincin siya ba sosai ya kan zauna ya ci sosai ba. Sai bayan ya gama cin abincin sai kuma ya ji barci barci ya fara ko arin ara aukan sa, ta shi ya yi ya haye kan Kujera ya kwanta kamar wanda kuma aka sakar masa wata gajiya Kasalan ta dawo ta ara rufeshi bai so ya kwanta ba tun da an kusa la'asar amman bai san barcin ma ya ara aukan sa ba amman shi barci ba shi da makunni ballantana ka kunna sanda ka ga dama sannan ka kashe a lokacin da ka ga dama Ana fara kiran sallar la'asar Mimi ta dawo akin sai ta ganshi kwance kan kujera yana barci, ita ta auko masa Bbanket ta rufa masa a kafafunsa zuwa kugunsa sannan ta kwashe duka kololin abincin da ya yi amfani da shi, ta yi mamakin yadda ya ci da yawa sannan ya sha zo o da kunin ayan da yawa kila su suka ara sakar masa da kasala. Tsab ta gyara wajen sannan ta shiga ciki ta auro alwala, tana cikin yin sallah ya shigo shima ya yi alwala ya fice, masallaci ya je ko da ya je ma taka'a faya ya samu sai dai ya rama su daga baya. Daga nan ya dawo gida sai a lokacin ya ci karo da Magajiya a shashenta ya yi mata barka da yamma ta amsa tana bin shi da kallo, akin Inna Meri ya shiga itama tana sallah sai ya zauna ya Jirata ta Idar suka gaisa a lokacin ma yana zaune ne amman kasala yake ji da barci barci sai Inna Meri ta fahimci haka sai ta ce ya je ya kwanta ya huta. Yana shiga akin Mimi na fitowa auke da wayarsa ta ce ana ta kira yana kar a sai ya ga Mu'azzam ne ya auka suka yi magana daman sun yi mgana da Slsafe ya ce masa sun kwana a hanya amman kokacin za su arisa gombe in sha Allahu. Nan saman kujeran ya sake kwanciya amman Mimi ta shagwa e masa sai ya koma ciki ya kwanta bashi da mafita dole ya tashi ya kara komawa saman gado ya kwanta ya cigaba da barcinsa Ita kuma sai a lokacin ta samu daman auko tsaraban da ya ce nata ne ta bu e wata riga ce T. Shirt fara a jikin rigan an rubuta Beauty da manya ba i zanen kuma an Rubura shi da pick clour ne, sannan sai wata hula ta mata wacce take a bu e a tsakiyar ta sai a daga saman wajen kan ta ke da ar kwalliya itama oick ce da zanen fari a jikin zanen an rubuta Pretty. Sai wani an kwali irin mai santsin nan na aurawa a wuya guda biyu suma dukkansu suna da zanen fari da pick a jikinsu Mimi ta ri a gwadasu tana kallon kanta a jikin cameran wayanta tana dariya haka ta rika aukan kan ta delfi. Walida ce ta katseta lokacin da ta kawo mata su ayaba oemo kankana apple tsaraban Mansoor kenan sai ta kar a ta saka a fridge tunanin ko da daddare ne sai ta yi masa fruit salat ya sha. Shi dai Aji barcin sa ya yi tasha sai mangariba ya sake tashi ya yi wanka. akwai ruwan zafi tun da suna samun wuta Mimi kuma da kittle ya tafasa sai ta juye a Fulas, sai da ya yi wanka ya fita sallar mangariba bai dawo ba sai da aka yi isha'i suka shigo gidan tare da Baba anjuma a akin Inna Meri suka zauna Mimi ta zo ta gaishe da Baba anjuma ya amsa cikin fara'a ga Inna Meri da daddare tuwon shinkafa ta yi miyar Ku ewa anya ita mansoor ya kara ci gaba aya sai ya ji nauyin jikinsa ga shi ya so ya le a gidansa yau saboda ya motsa jiki sannan ya sauya kayan jikinsa ya samu cikakken hutun da yake bukata amman kuma kasala da Nlnauyin jiki sun hana shi, ana ta hira a akin Innar amman shi barci barci ne a Idanuwansa Baba Danjuma da ya lura sai ya ce ya je ya kwanta ya yi barci sai sun ha u da safe. Yana shiga akin ya iske Mimi ta yi walliya da rigar da ya siyo mata da hula sai ta saka wani bakin plazo mai bu ewa. Ta yi masa wani irin kyau in da sai da ya yi mata kallon Kurillan da bai ta a yi mata a bu e ba, sai dai a fakaice. Ta tare shi da hadad en fruit salat in da ta ha a masa duk yadda ya koshi ba ta kyaleshi ba sai da ya sha da ya ce cikin sa ya cika sai ta kwa e fuska za ta yi kuka shi kuma a gajiye ya ke ba zai iya da wannan rigimar ba. Bayan ta maida komai kitchen ta dawo kawai yana zaune ya an kishingi a saboda ba ya so ya kwanta a haka gwara dai ya bari abin da ya ci ya sha ya fara sauka. Sai kawai ganin Mimi
Chapter 117 · 0% Book details