Sashe 102
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mganar inki sannan ta sani ita telan ta tun na gida ne, da ta je wajen aiki ta ba ma Rukky ta ce ta kai masa, tunda ta san shi itama ta na kai masa inki, Inna Meri ma ba ta samun zama tun satin take zuwa can ana hidima da ita tunda an zama aya. Har ga Allah Mimi ta auka da amincewar Aji a mganar zuwa sha'anin bikin nan tunda ba ya mata mgana tunda ya dawo in ta gaishe shi sai ya ga dama yake amsa mata. Ta ga kuma abu na gida ne gaba aya. Tun ranar Al'amis ba ta da aiki ba ta je ma'aikata ba ta na gida daman Hibba tun ranar talata tattara ta koma gidan su. A kace za'a je Walima su Yaya Amina suka ce ta shirya su tafi Mu'azzam zai kai su a motar shi, ganin suma dukkan su sun saka dogayen riguna da mayafi harda Yaya Halima Bintu ko nata ma mayafin arami ne har Yaya Amina na mata mgana ta ce shi za ta saka, itama sai ta je ta shirya cikin ba ar abayar ta ta yi rolling in mayafin a saman kanta. Ba kwalliya ta yi ba amman kallo aya za ka yi mata kasan Mimi mace ce ta nuna sa'a jakarta da takalminta na wani kamfani ne mai tsada da yarari, su kansu su Yaya Amina suna ta cewa kai Mimi kin yi kyau. Bintu ta saka wayarta ta auke ta Hoto ta na fa in" Sai Baban inna ya siya wannan wankan." Ita dai sai dariya take yi, Walida ma ta ce ba za ta je ba Abayan ta ta tsufa ba ta da na Yayi, Mimi na jin haka ta ce" Mu je akina ki za i abaya sai kin darje, zan saka wata awata daga egypet take tana saidawa ta turo miki ki zaba sai na siya miki, kina da Yaya kama ta, ba ki ba kukan Abaya Walida." Bintu ta saka gu a ta na kirari" Takawarki lafiya Hajiya Fatima. Uwargida kuma a Amarya a gidan Mansoor." Yaya Amina da Yaya Halima nata dariya, Mariya ba ta nan, tana gidan Zuwaira ba wanda yasan abin da ya sa Magajiya ke yawan tura ta can gidan. Walida ta darzo wata uban su Abaya sau aya ma Mimi ta ta a saka ta ta ba ma dubu hamsin baya ta ji duwatsu ta saka Mimi ta na a mata mayafi, Mu'azzam su ka yi ta jira ya ce suna tare da Mansoor a gidansa ganin zai ata Lokaci ya sa Mimi ta ce bari ta hau abun hawa ta je gidan Hajiya ta auko motar ta, da yake an gyara tuntuni haka ko akayi tare suka je da Walida da Bintu san da su ka je Hajiya na barci sai Baaba Uwani ka ai sai ta ce a kyaleta mota za ta auka. Sai da su ka auko motan su ka dawo sai ga Mu'azzam ya zo, sai a ka raba wasu suka shiga Motar Mimi wasu ta Mu'azzam sai Tudun Wada, Mimi ba ta auka za ta iya sakin jikin ta acan ba sai ga shi ta saki jiki Saboda an karramata kowa ya zo sai ace wannan fa matar Mansoor in Inna Meri ce nan da nan sai a shiga gaisheta ana mata lale, Mimi ta fahimci Karamcin da Inna Meri ke da shi a wannan Ahalin ita da ya'yanta sun zama yan gida ba Nuna bambamci ba za ka auka ma ita yar gidan ce. An yi walima an ci an sha, an yi kuma wa'azi biki ya yi da i har dare suna can ita kuma ganin suna tare gaba aya ya sa ba ta damu da daren da su ka yi ba, shi kuma bayan sallar Isha'i Mansoor ya je gidan Bangaren Inna ba kowa ko'ina a kulle sai ransa ya aci a zaton sa tana wajen aiki ba ta dawo ba, shi ya manta da wani biki duk da a azun Mu'azzam ya yi masa zencen. Wayar Mimi kira lokacin suna gidan su Hibba an dawo daga walima, sun yi salla kenan suna cin tuwo miyar kubewa ayan ita da Bintu wayarta na wajen Walida tana kallon hotuna. "Anty Mimi ga wayarki Yayanmu na kiran ki" Sai da gaban Mimi ya fa i, wani kiran na Aji ba alheri ba ne, hannunta na cikin tuwo ya sa Bintu ta ce Walida ta aukan mata wayan ta saka mata a kunni. "Kina ina ne? Abin da ya fara tambayan ta kenan, kai tsaye ta ce" Muna gidan biki tare da su Bintu." "Wani gidan bikin? Ya kara tambaya ta, mamaki ya kamata ga mutane a falon ga su Bintu a wajen sai ta Sassauta murya tana fa in" Gidan su Hibban Mu'azzam,gkbe bikin yayarta shine muka zo Walima." Sai a lokacin ya tuna da mganar biikin sai kawai ya ce" Ba kusan dare ya yi ba ne? In su ba su da hankali sai ki biye musu ku zauna har dare acan? Da sauri Mimi ta ce" Za mu dawo yanzu, da Inna mu ke jira to ta ma ce anan za ta kwana." Jin sunan Inna ya sa mganarsa ta are sai ya kashe wayar, ya koma yana kiran Mu'azzam shi kuma wai yama fa a masa ya na gidan Nasir ya je barka matarsa ta haihu. Sai ya tuna tabbas Mu'azzam ya sanar masa matar Nasir ta haihu amman abunda ya bashi mamaki maza na zuwa barka ne. Tambayar da ya yi ma Mu'azzam kenan shi kuma ya ce" Sosai ma, suna zuwa in ya zama dole." Aji ya ta e baki kafin ya ce" Ni dai a sanina barka ai na mata ne, ka ce ma Nasir duka duka yaushe ya yi auran da har zai yi a biyu.? Ashe Nasir na kusa sai ji ya yi ya fizge wayar yana cewa" Kaji sharri shekara ta hu u kenan da aure, miye nufin ka? Aji ya yi karamin tsaki kafin ya ce" Duk abin da kake nufi dai." Daga haka ya katse wayarsa, ya so ya koma gida sai dawowar Baba ya sa suka tsaya in da aka buge akin kwanansu tun na samatarka aka fitar da akin da matar Saddiqu za ta zauna, anan wajen wai har 2bedroom da kitchen za a yi waje bai isa ba har san ta a uwar akin Magajiya ta ce daman ya yi mata girma a fasa a di a a bar mata rabi. Gaba aya sai aka sauya fasalin gidan, Mansoor dai fatan alheri kawai ya yi, Daganan ya koma gida Mu'azzan kuma bai koma Tudun wada ba, tun da har su Yaya Amina anan za su kwana tunda mahaifin Hibba yayan mahaifiyar su ne, Walida ne kawai da Bintu da Mimi suka dawo gida. Washegari kuma yinin biki Tana da Karanta Labaran yamma sai ta kira Manaja ta ce ba za ta samu zuwa ba Salin ya fanshe ta. Tun Safe karyawa kawai suka yi Bintu ta biyo musu su ka koma gidan bikin. Daman Rukky ta kawo mata inkin ta kuma ta aukan masa mayafi da jaka da takalmi, ganin kowa da mayafin shi ina za ta ri a yawo da hijabi a gidan Biki. A can su ka yini suna ta shan biki, Mu'azzam da Mansoor sun zo aurin auran kuma har cikin gidan sun shiga suna gaggaisa da mutane. Aji ya jujjuya ko zai ga Mimi amman bai ganta ba, idanuwansa suna mararin ganinta amman ba su nan sai Mu'azzam ne ya ji yana tambayar wata mata ina su Hibba? ta ce duk suna wani gida can gaban su inda Amarya ke zama, shi ya sa daga nan suka je restaurant suka ci abinci suka koma gida su ka huta da la'asar kuma Mu'azzam ya bi Aji zuwa Studio in su daman azu da suka je sun ga junior sai Mansoor ya ce su auke shi su tafi da shi tunda uwarsa tana biki ta bar yaro ta na gararamba a tsakar gidan biki. A can kuma gidan biki ba'a san sun tafi da shi ba gida ysaru e da neman sa tuni Hibba ta dawo hayyacinta sai kuka, Inna ce ta ce a kira su Mu'azzam tana da tabbacin su suka auke shi Ilai kuwa tana kiran shi ya ce ga Junoir nan tare da su sannan hankula suka kwanta aka Ci gaba da shirye shiryen kai Amarya. Tunda nan kusa ne ba nisa tsakanin su bai wuce naira ari ba. Mimi da Motar ta ita ta auki su Bintu suka je su ka ga akin Amarya tunda ba kwana an riga an yi jere kafin mangariba duk an watse shi ya sa suma suna idar da salla Mimi ta ce su zo su tafi sai suka yi ma su Inna sallama ta saka su aukan Towon shinkafa miyar allayahu ta ce a kai ma Mu'azzam bawan Allah. Bintu na gefe ta ce" Inna shi ka ai? Ban da Baban Inna? Inna ta ce" Wannan ga matar shi nan za ta ba shi abinci, kuma ni na fi tausayin Mu'azzamu an inna" Wata abokiyar wasan su Mu'azzam ta ce" Ke dai Inna son kai kike son nunawa, amman itama matar tashi nan ta yini, in ta koma gida ai sai dai ta kwanta ta huta ta sha gajiya." Inna Meri ta ce" To na ji, su tafi da shi gaba aya da Mu'azzamun da Baban inna ba shike nan ba." Lokacin suka dawo a kofar gida suka iske Baba anjuma da Mu'azzam da Mansoor sai Auwalu a saman tarbama da yake garin an fara zafi haka, da farko har Mimi ta haske su da hasken motar ta kafin ta rage filitan gaban, a kofar gidan take ijiye motan tun fara bikin suna dawowa late ba lokacin komawa gidan Hajiya. Tana ganin shi sai ta gyara zamsn mayafinta ta ora saman kanta Alhalin ko Bintu a saman kafa a ta rayata nata, sun fito daga motan Walida ke auke da Kulan tuwon Bintu ta auko na miya. Suka durkusa nan suna gaishe da Baba ya amsa lokaci aya yana fa in" Sannan ku da zuwa, Bintu Walida, Fatima ya gajiyan hidima? Suka amsa da lafiya lau, Mu'azzam ya gaishe da Mimi ta amsa