← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 208

Sashe 189

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata sallama suka fita tare da Baban ta bi su da kallo tana girgiza kanta, Ko ta i ko ta so ayan Meri da agolan da ta raina su ne su, yaran nata kuma da ta nuna sun fi kowa ga shi nan su ne rayuwarsu ke wula anta gwara gwara ma Auwalu da shi yanzu ya zama Enginer ba ya gini sai dai kar an kwangilan gini kuma ba laifi yana samu sannan ya na yi mata tunda ba halinsu aya da Saddiqu ba, Jummai sai dai ta zo ta arbe na ta, har gwara ma Zuwaira to yanzu haka shi kan shi Saddiqun kusan ci da shi na wajen su ne tunda ba shi da komai yanzu sai bakin rai. Mariya kuma ba domin su ba da tuni itama rayuwarta ba ta inganta ba, tana da tabbacin da bikin ta in ya zo su ne za su yi komai da abunda uwa za ta yi da abin da ubq zai yi ta na da tabbacin suna yi domin Allah ne ba domin komai ba in da ace suna yi domin ganin ido ne da tuni sun daina tun baya da take nuna hassadatan a fili, yanzu kan ta saduda tunda ta ga jama'a ma suna gudunta har su Gaje yanzu sai su yi wata ba su le o ta ba, ko wani abu ya faru a anguwa sai dai in ta biya musu su ce sun shiga jaje ko Allah ya kyauta, amman ba sa nemanta Ta dai fahimci duniyar ce gaba aya ta sauya gwara ka aikata alheri yanzu in da mutuwa ta yi fa? Haka mutanen da ta zauna da su za su yi mata? ta kuma fahimci lalle ka zauna da mutane lafiya shima wani abu ne, Sannan ka aikata alheri tun kana duniya za ka ga amfanin haka, ga shi Meri ta bar mata gidan amman kamar ta tafi da duk wani albarkan gidan gaba aya. ****** Tunda Inna Meri ta ga Baba anjuma da Mansoor ta san aranta ya kai. Shi ya sa tunda suka shigo ta ha e rai, ta ga fa zuwan su suna zaune a falo suna jiranta Baba anjuma ke saman kujera Mansoor kuma yana zaune a asa. Walida ce ta kawo musu ruwa Aji sai faman waige waige yake yi ko zai ga Mimi amman ba ta fito ba. Inna Meri ko kamar da gayya ta shiga aikace aikacenta wai wanke wanke da daddare saboda dai kada ta sauraresu. Mansoor yunwa ya ke ji bai ci wani abun kirki ba, sai ya tambayi Walida abin da suka dafa kai tsaye ta ce"Tuwo Inna ta yi da rana na zubo maka ne? Sai ta amsa mata da eh, ai kam tana zuwa Kitchen in Inna ta ga za ta zuba abinci ta tambayeta wa zai ci? Ta ce yayanmu ne. Kai tsaye Inna Meri ta ce"ba zai ci tuwon ba, rufemin kular nan" Cikin mamaki Walida ta ce"Saboda mene Inna? Inna ta mata wani kallo kafin ta ce"Sai na ji sha a sannan." Walida na jin haka ta yi sum sum ta fita daga Kitchen ta koma ta gaya ma Mansoor abin da Inna ta ce sai ya yi mirmishi kawai ba tare da ya yi mgana ba Baba anjuma ya ce" Me ya sa Meri take hakane? Ban san ta da wannan fushin ba." Kawai sai ya mi e yana fa in bari ya je ya sameta a cikin madafin. Yana ta shi, Mansoor ya kalli Walida yana fa in" Ina Antyn ki? Sai da ta kalli akin sannan ta ce"Tana ciki, kila ta kwanta ne" Kai ya jinjina mata sai kawai ta wuce ta shiga akin nata, ta iske Mimi kwance amman ba barci take yi ba, ta na shiga ta yi saurin mi ewa zaune lokaci aya tana fa in" Aji ne ya zo? Sai Walida ta ce"Eh shi da Baba, wai me ya yi ma Inna ne? Abinci ma fa hana shi ta yi.". Mimi ta zaro ido kafin ta ce"Kai.! Walida ta zauna gefenta tana fa in" Wlh Allah, kuma fa ta ga har da Baba amman ta na kitchen tana wanke wanke." Sai Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba, to ita me za ta ce? duk da ya yi mata ba dai dai ba amman bai kamata Inna ta hora sa da rashin abinci ba, gaba aya tausayin shi ta ke ji, Kamar ta ta shi ta je ta roki Inna kuma tana da tabbacin bai ci wani abinci ba tun jiya nan, amman ba za ta iya ba sai Inna ta ga kamar ta yi rashin kunya kuma duk abin da take yi ta na yi ne saboda ta watan mata ancinta. Suna ciki suna jin tashin maganar Baba da Innar a talon, kenan Baba ya samu nasaran Fito da Inna Meri daga cikin kitchen. Inna Meri na saman kujera Baba anjuma na gefenta Mansoor na gefen Baban kansa a asa. Shi kuma Baba anjuma sai faman kallashi inna yaoe yi da kalaman ban hakuri fa i yake yi" Haba maryamu ban san ki da dogon fushi ba, ina miki shedar ke macece mai afuwa, tunda har ya san ya yi laifin kuma ya ce ya yi nadama ya ba da hakuri to me zai hana ba za ki yi hakuri ki ba shi matarsa su koma gida su daidaita ba?. Inna Meri ta yi shuru kafin ta muskuta lokaci aya tana fa in" Ya gaya maka zargin matarsa yake yi? Ya sanar da kai shi da kansa ya ce ta fitar masa a gida, shi isheshe mai gida ba." Ta fa a tana hararanshi lokaci aya tana cigaba da fa in" Ya yi sum sum da kai kamar mutumin warai. Ahalin ya iya aikata tsiya kala kala, ace a shekaran Baban Inna talatin da oriya bai san ciwon kansa ba? anin sa Mu'azzamu wlh ban ta a jin kansu shi da matarsa ba. Amman shi kamar wani aramin yaro daga wannan sai wannan., ni kuma na gaji da wata rana ya yi abin da za mu kasa shiga mutane gwara ya sauwa e mata cikin girma da arzi i na maida ma Hajiyar jikarta na ba ta hakuri." Inna Meri ta gama fa a tana ara ha rai shi dai Mansoor sai faman ba da hakuri ya ke yi, Baba anjuma ma haka. "Duk ya fa a min wlh, na kuma yi masa fa a tunda dai ya yi nadama ki duba girman Allah ki yi hakuri Maryama.." Baba ya kirata da mafi soyuwan sunan da ya ke kiranta da shi wani lokacin, ta ago ta kalle shi daga shi har an na shi sun maraiiraice sai ta ji wani abu a asan ranta, Da sauri ta kauda kai tana fa in"Shi mai uba ko? Ya je ya auko ka, kun yi min taron dangi saboda ni kunga nawa uban ya mutu ko? Da Sauri Baba ya ce"Ko aya, ke yanzu kin fi wata mai uban, Allah ya ba ki aya sanyin Idanuwanki wa anda suka lullu eki da alheri sannan kina da ni, ina da tabbacin kin gama samun komai a nan duniya sai fatan cikawa da Imani kawai Maryama Inna Meri kauda kanta ta yi tana share wallah kafin ta ce"Shike nan amman ya sani wannan ne na farko kuma na arshe wallah tallahi in ya sake aikata wani kuskuren sai ya rasa Binta." Da sauri Mansoor ya ce"Ba zan ara ba Inna, ki yarda da ni." Kallonsa ta yi kafin ta ce"In ka ji irin haka ya shige ka, ka kira sunan Allah domin ka samu natsuwa ina ara yi maka nasihan cewa ka koyi sarrafa wannan zuciyar taka saboda watan wata rana za ta kai ka ga aikata abin da ko kaso ka gyara ba zai ta a gyarun maka ba." Kansa na asa ya ce"In sha Allahu." Baba anjuma na Mirmishi ya ce"Mun gode, Sai ki yi mata mgana ta fito su tafi, In sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba." Inna Meri ta gyara zama kafin ta ce"A'a.." A tare suka kalleta cikin mamaki kafin ta cigaba da fa in" Itama macece mai anci ita kuma ya yi ma wannan laifin zan kirata a gabanka a gaban shi, in ta amince ta masa afuwa ba zan hana ta bin sa ba amman in har ta ce ba ta hakura ba, ba zan iya hana kaina goyon bayanta ba." Baba anjuma ya ce"Ba ma za'a yi haka ba, Kirata ta zo nima na ba ta hakuri." Inna Ta mike lokaci aya tana fa in"Ba ma ta da lafiya, gwara ta zauna waje na har sai ta warware wannan mara tunanin magana kawai zai iya gasa mata da zai aga mata hankali wani abu mara kyau ma ya faru. "Me ke damun ta? Baba anjuma ya tambaya kafin Inna ta yi mgana da sauri Mansoor ya ce"Baba Inna ce ta ce Mimi na da ciki, tsakani ga Allah kula da mai ciki ai sai uban cikin ko? Inna ta ji kunyar duniya ya kamata Baba ma kai ya kauda kafin ya ce"Wannan gaskiya ne. To to Allah ya raba lafiya." Inna meri kuma da uwa ta maka ma Mansoor kafin ta ce" Ba ka da kunya ko? Sai a lokacin ya tuna tabargazan da ya yi da sauri ya maida kai asa yana sosa keyarsa ya na yar dariya. Walida Inna ta kwalama kira bayan ta fito sai ta ce ta kira mata Binta. Mimi daman tana zaune nem Jin Inna na kirata ya sa ta mike ta zura hijabin Walida zuwa Falo tun da kuma ta fito gogan ya kafe ta da ido kuma maganar gaskiya ta rame ta yi wano fayau to wai daman haka alamun cikin yake? Me yas a shi bai gane ba? Kusa da Inna ta zauna kanta na asa ta gaida Baba ya amsa cikin sakewa lokaci aya yana fa in"Ya jikin Fatima? Kanta na asa ta amsa da sauki ya ce Allah ya ara lafiya Mansoor a ka bari da amsawa Inna ta wurgeshi da maficin Hhnunta sai da ya same shi shi ya sa ya kama bakin shi. Bayan tattaro duka bayanan Baba anjuma ya sake ba ta hakuri da cewa"Ki yi hakuri kin ji
Chapter 189 · 0% Book details