← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 208

Sashe 9

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murya ta ce"Ki fa a mata kar ta damu da ni ina lafiya." Daga haka ta juya ciki ta koma ta zauna ta yi tagumi. Tana tunanin makomar rayuwarta anan gaba, ko ta amince ko kar ta amince rabuwarsu da Mansoor ta har Abada ce kuma da gaske yake yi da ya ce zai gogeta daga tunanin sa da mafarkin sa gaba aya. ***** *08 Feb 2022.* 6:00pm Yana studio insu yau sun yi afternoon training ne ya samu wayar mijin Bintu Bashir yana fa a masa tun safe Bintu ta rufe Kitchen ta kuma oye makulli ta ce ta ga wanda ya isa ya dafa abinci ya ci acikin gidan nan, Bashir in ya ce ya yi ta ro onta bata saurare shi ba, sai yaji ransa ya aci daman ya na ta so yaje gidan sai kuma wasu abubuwan suka auke masa hankali. Amma tunda abun har ya kai ga haka ai shike nan zai je gidan yaji ta inda iskancin na Bintu ya fara. Coach in su ya sanar ma zai je gida ana nemansa daman da mashi insa yazo sai ya sauya wandonsa jikinsa daga gajere zuwa dogo tunda gidan surukai zai je kuma a matsayin sa na babban yaya ya rike girmansa. Cikin lokaci ankani ya iso gidan tun da nan anguwan Arawan ne daga can baya ba su da nisa daga gida. A kuma Kofar gidan ya ci karo da Bashir in yana jiransa. A yadda ya gansa duk ya yi wani firgai firgai sai ya fahimci Bintu na iskanci kala kala acikin gidan nan tunda har mijinta na tsoronta. Gaisawa suka yi bayan sun yi musabaha Bashir in ya fara fa in "Wato yayanmu lamarin ne ya fara fin karfina. Wajen sati aya gidan nan ba ma zaman lafiya." Mansoor ya ka a kai kafin ya ce"Ka yi min izini mu shiga gidan tare." Ya na jin haka ya fara sosa kai yana Fa in"To to shike nan Yayanmu ammh don Allah kar ka ce za ka yi mata fa a a bi ta a sannu." Takaici yasa ya wuce yana fa in"Kai dai ba ta gagare ka ba? to ni ba za ta gagare ni ba don ubanta." Ya na fa in haka lokaci aya ya yi sallama acikin gidan. Bashir na binsa a baya jikinsa na faman rawa.. Uwar gidan Bintu ce a tsakar gida ita ta amsa masa sallamansa, ba saninsa ta yi ba domin bata ta ta ganinsa a gidan ba amman ganin yadda ya shigo gidan ga Bashir a bayansa yana wani sunne kai. Kafin ma ta yi mgana ya yi saurin tare ta da cewa"Hadiza. Yayan Bintu ne" Kai tsaye ta kallesa tana fa in"Ayya ina yini? Bai kalleta ba ya ce"Barkan mu da yamma, ina ne akin Bintun? Ya fa a ya ma kallon Bashir saboda shi dai yasan gidan ammh bai ta a shigowa ba, shima abin da ya sa ya sani saboda Mu'azzam sun ne ta a wucewa ta kofar gidan ya nuna masa ya ce ga gidan da Bintu ke aure. Da dai Mu'azzam ne shi kam kamar wani mace gida gida na mata ya iya shiga. Bashir na gaba yana bayansa har akin Bintu Hadiza ta bi su da kallo, ko shi ne yayanta wallon kafa wanda a kace zuwa da shi garin aka yi? domin ta san ayan yayan nata an sanda ne tun da yana zuwa gidan in yazo garin, kuma ga dukkan alamu wannan bashi da wasa, kuma sai yanzu ta ga kamansu abu aya ne ya bambamta su ita Bintu fara ce shi kuma ba i ne. Ta e baki ta yi domin ita abun ya isheta Bashir ya zama sallamame tsoron Bintu yake ji, bai iya wani kuzari in tana wajen shi ya sa take yin abin da ta ga dama. Ita dai ta fa a masa ta gaji, ko ya auki mataki ko ta bar masa gidansa ya zauna da yar so Bintu. Duka duka s haihuwanta aya ne ya karo mata kishiya da fitinanniyar yarinyar nan tunda ta shigo gidan ta daina barin su cikin sukuni. Tana kokarin shiga akinta bata san mai ya faru ba taji muryan yayan Bintu cikin tsawa yana fa in"Ina za ki je kuma? dawo nan ki zauna munafuka." Kuma ta ji ko motsin Bintu bata ji ba, a ranta tace kila dai wannan ne mai maganinta. Tana yar dariya ta shige akinta. Abin da kuma ya faru shine suna shiga akin nata, Mansoor ya zauna a falo Bashir kuma har ya mike jikinsa na rawa zai je ya kirata sai ga ta fito. Sai dai jikinta ya yi sanyi da ta ga Baban Inna ai ta shiga uku. Sai ta juya da sauri za ta koma shine ya daka mata tsawo ya ce ta dawo ta zauna. Sai gata ta dawo sumi sumi jikinta na rawa ta zo ta zauna kan kujera ta kuma ga mijinta a asa wani kallon da Baba inna ya yi mata ta bakin ta yasa ta sauko kasa bata shirya ba. Gyara zamansa ya yi shi cikin kaushin murya da ba wasa ya kalli Bashir yana fa in"Me ya faru ne? Ka yi mini bayani tun daga farkon rigimar har zuwa yau. Bashir ya gyara zama ya fara fa in duk fa rigiman akan less ne da ta gani a jikin Hadiza ne shine ta saka rigiman ya ci amana ya siya ma Hadiza leshi bai siya mata ba, shi kuma ya rantse mata da Allah ba shi ya siya ba da ku in adashenta da ta kwasa ta siya saboda aninta zai yi aure. Shi ne Bintu taki yarda ta rika zage zage tana cewa ya ci amananta shima sai ya siya mata wannan leshin za'a zauna lafiya, ganin abun nata ya i wucewa ya sa ya ce in ya samu ku i zai siya mata amman ta ce ba ta yarda ba har abun ya kai yau ta rufe kitchen ta ce ta ga mai girki a cikin gidan balle aci abinci." "Wlh karya yake yi, shi ya siya mata saboda cin amana..!" Kafarsa ya saka ya hambareta ya ma manta ba a filin wallo ya ke ba, da ace da karfi ya haureta da sai ta ci ha o da bakinta. Cikin tsawa ya ce" Ashe baki da mutumci ban sani ba? mijin naki kike arya ta wa? Ya fa a cikin takaicinta yarinyar nan fa ta yi nisa. Ita kuma sai ta koma gefe ta fashe da kuka tana fa in"Wlh ba gaskiya ya fa a ba, shi ya siya mata ni dai na ce wanda ya zalunce ni ban yafe ba." "In kika ara mgana ba tare da nace ki yi ba, na rantse da Allah sai na yi biji biji da rayuwarki anan wajen." Ya fa a mata cikin tsawa ganin yadda yake huci ya sa ta shiga taitayinta kar ya yi wallo da ita ya za ta ko ball ce ya samu, ta kuma san shi da bakar Zuciya kamar Kuturi ya yi zuciya to sai fa ran kowa ya aci. Shi ya sa ta koma gefe ta yi shuru ta na hararan Bashir kamar Idanuwanta za su fa o. Ba dai ita zai ha a da Baban Inna ba, sai ya gane kuransa. Kuma duk yana ganinta ta na harare harare, kuma abun haushi Baahir din na bata hakuri da hannu. Sai ya ji ba Bintu ba ce abun duka harda Bashir din tunda ya fahimci sakarai ne. Bai yi mgana ba sai da ya saka Bashir in ya kira matarshi Hadiza. Ta sako hijabinta tazo ta zauna itama ta tambayeta ta maimaita abin da Mijinta ya ce ta karishe da fa in "Wlh ni na siya leshin nan da ku ina, ba Baban Afra ya siyamin ba gaskiyan magana kenan." Ba domin Baban Inna na wajen ba mikewa za ta yi ta karyata su ammh tasan ta sake magana sai an yi abun kunya a gaban kishiyarta. Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya kalli Bintu ya na fa in "Ba ki da kaya ne da za ki ta da rigima saboda leshi? Ko a tsirara kike yawo ba mu sani ba? Bintu ta yi kwalkwal kafin ta ce"Ina da shi, amma Baban Inna." A tsawace ya ce"Ke sunan nan ya fita daga Bakin ki ko naci aniyan ki wlh." Daga nan ta san kuskuren da tayi da sauri ta gyara da fa in" Yayanmu shi ya siya mata fa, kuma ai ina da ha in nima ya siyamin tun da adalci aka ce ayi." Ta gama fa a ta na harare harare. Cikin jin haushi ya ce"To na ji ya siya mata ke bai siya miki ba sai aka yi ya ya? uwarsa ce ke da dole sai ya siya miki duk abin da bai yi niyya ba? In ma ya siya mata da ita kika zo gidan kika gansu kuma gidansa ne yana da Ikon ya yi abin da ya ga dama, kin rufe kitchen kin ce ba wanda ya isa ya ci abinci nace abinci daga gidan Wanzamai kika zo da shi?. Na ce daga can kika zo da shi? Ya karishe fa a cikin tsawa sai Bintun ta saki kuka za ta sake mgana cikin ara daka mata tsawa ya ce"Ba da ke nake mgana ba? da sauri ta ce"A'a. Kai tsaye ya ce"To ashe iskanci ne a cikin kanki ban sani ba, ba ki da mutumci na jima ina jin labarin ki kuma daman ina jiran wannan ranar, daga nan wajen wallahi na kashe wannan mganar, ko da wasa kika kara tada mganar leshi na ji labari zan yi miki abin da ba ki yi tsammani ba, sannan ki auko Key din kitchen ki ba ma mijinki ki kuma bashi hakuri, sannan kar na sake jin kin fito kin yi zage zage ko rashin kunya, kin sanni kin san halina ba ni da kyau ko nayi wanka kika bari na kara takowa cikin gidan nan sai nayi miki dukan mutuwa wlh, kuma kinsan ina fa ar abinda zan iya aikatawa ne ba wanda bazan iya ba." Ya karishe fa a lokaci aya yana mike wa Bashir ma ya mi e shima da sauri yana fa in "Ai Yaya Mu'azzam
Chapter 9 · 0% Book details