← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 208

Sashe 77

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai gayya kamar wasu yara cikin Aljihunsa ya saka hannu ya fiddo ku i bai san ko nawa ba ne ya mi a mata ta karba suka ha a baki wajen yi masa godiya ita da Mariya shi kuma da Sassarfa ya fita daga gidan sai dai su Nasir su ka cimmasa a kofar gida. Ji ya yi suna mganar ko su je gidansa su kwana ne? ai sai ya sha mur ya kalle su kafin ya ce" Gidan wa? nii fa ban gayyato kowa ba sabo da haka kowa ya kama gabansa." Mu'azzam ya nuna kansa ya na fa in"Har ni Yaya?. Kai tsaye ya ce"E, har kai in na ce, ka kwana agidanku mana." Me su Nasir za su yi in ba dariya ba tunda suka ji an kori Mu'azzam suka san har su in yau ba su isa su kwana a gidan Aji ba. Sa mashin insa daman ya zo ita ya hau ya yi tafiyar sa da Nasir ya yi masa gatsen tambayarsa yaushe na aurin auren? A kaikace ya kallesa kafin ya ce"Ka kira waliyin Mimi tsohon Sanata Hamza sulaiman Dabo shi ya san lokacin." Nasir ya ri e baki kafin ya ce"To ka yi a hankali surukai dai ba abun wasa ba ne" Haka ya tafi ya barsu kamar ba gobe ne Bbkin sa ba, a irin yadda ya ke nunawa shi ya sa Nasir ya ce ya saka ma auran Aji suna Auran aukan Fansa. ******* _Friday 20 September 2022_ *1:15pm* Karfe aya da wasu an mintina shaidu suka ka tabbatar da aure taskanin Mansoor ibrahim Aji da amayarsa Fatima Kabir Dabo( Mimi) a cikin haraban gidan Tsohon Sanata Hamza Sulaiman Dabo. aurin auran da ya samu hallatar mutane ba laifi, Shi kan shi Alhaji Hamza bai saki jiki ya yi gayya ba iya na jiki jikin sa ne, sai an uwa da abokan arzuka bangaran Aji shi dai bai gayyaci kowa da hannunsa ba sai dai ya ga kara na masoya da lama'ar anguwan su, bangaren Baba anjuma kan ya yi gayya sannan Baba Kabiru ya zo daga Bauchi har da Baba Karimu ma, sannan manyan yan wasan wallon kafa na ananun Team na anguwanni duk sun hallaci aurin auran na shi tare da wasu manyan shugaban ungiyoyin wallon kafa masu zaman kansu ciki har da na Kano ya zo masa sannan ya ga members in su na Gombe United duk sun hallaci aurin auran nashi tare da sauran yan wasan wallon matasa ma su tasowa da ya sani Couch ne duk ya yi masa wannan karan. Sai bangaran su Nasir abokansu tun na sakandiri da ya ma manta da su ya gansu a wajen bai yi mamaki ba yasan gayyar su ne, Aji ya saka fararan kaya har da babban Riga abunda bai ta a sawa ba, hulan kansa ba a ne haka ma takalmin kafarsa mai rufi ne na fata da bakin agogon hannunshi ma na fata ne,wannan duk shirin Mu'azzam ne kuma an sha daga da shi kafin ya saka kayan wai sun masa girma ya na jin zafi, su kuma sai suka saka shadda mai ruwan asa su hu un gaba aya suma wai harda manyan riguna haushi ya kama Aji acikin ransa ya ga kamar sune masu auran ba shi ba. Sun fa shirya ma bikin harda mai hoton su ke tafe, Aji na ta gaisawa da mutane akwai manyan nutanen da su ka zo aurin auran kuma suna bibiyan wasannin shi cikin gida gombe wani cikin su sai da ya yi ma Sanata maganarsa ya ce" Sanata ka ce surukin namu an ball ne, ai na san Aji yaron ya na ji da zamani ya iya buga wasa a cikin fili" Ba ma shi kadai ba ya samu irre iren su da yawa shi da yake kallon kwallo bai dame shi ba sam bai san wainar da ake toyawa ba ma, Baba anjuma ya gabatar masa da Baba Kabiru da Baba Karimu matsayin annen Mahaifin Mansoor na jini suk gaisa, ana gama aurin aure za su wuce masallaci Jumma'a daganan su je su yi reception saboda bayan la'asar ne buga wasan su wanda zai gudana acan Studio in su dake cikin gari. Dakyar Aji ya tsaya aka yi hotuna ba a ma gama ba ya ce shi fa ya gaji da tsayuwa ko a hoton ma sai buga uban shining yake yi, cikin wa anda ma ya yi ta hannu da su bai gane su ba harda Dr. Sulaimam da mazajen su Madiha, har da Jaheed a cikin su ma a wajan aurin auran suna ta jin labarin shaharan Aji a bakin Matasan sannan a gaban idanuwansu aka ha a rukunin Gombe United har da Couch in su aka auke su hotuna bayan angama suna ta bashi hannu suna fa in"Allah ya sanya alheri Captain". Sai Sulaiman ya ji ya burgeshi domin daga ganin shi cikakken namiji ne ya hango haiba da mazantaka ba Laifi in har a yanzu Mimi ba ta daina son shi ba ya cancanta ne. Sannan abokan aikin Mimi sun yi mata kara sosai wajen tururuwan zuwa mata aurin, sannan wasu sun sha mamakin mijin da ta aura ko wani bai sani ba sai wani ya fada masa ai an wasan wallon kafa ne Captain na ungiyar kwallon kafa mai zaman kanta na Gombe United. Suna barin wajen aurin auren suka je masallacin Jumma'a daga nan kuma suka isa restaurant in da su Nasir suka kama saboda reception an ci an sha kuma daga nan su ka auki Aji da suka i bari ya gudu zuwa gidan Wanzamai in da ya cika da mutane ba matsaka tsinke Inna Meri ai ta ga an Adam Allah ya taimaketa tana da a su Amina ke ta kai da kawo da ba i ga Surukan kwarai irin Hibba sannan ga yan'uwansu Mu'azzam da su ka zama cikin Iyalin Inna Meri Magajiya ta san ko ta shiga bikin ko kar ta shiga ba abunda za a fasa Inna meri ta shiga ta fita jaihuwa ta yi mata rana Ko da ya ke har Magajiyan Mu'azzam ya yi ma inkin bikin amman ta i sakawa Atamfar gaba aya aka yi har su Gaje an inka musu suma su Baba sani an inka musu Shaddodi amman ba su gode ba suka ri unkuni tunda ba'a inka musu babban Riga irin ta Baba Danjuma ba. Kamar wani yaro haka su Nasir suka ti o Aji har akin Inna Meri sai waje ya kaure da gu a har da Bintu acikin ma su yi, amman duk wannan zagaayensa da an uwansa suka yi bai saka an ga mirmishin Aji ba. Fuskarsa ba ta iya fassara yanayin da yake ciki ba an yi hotuna da su Inna da su Amina tare da an uwansa na dangin Uba har da su Bintu ba su wani jima ba su ka bar gidan tunda la'asar ta yi Nasir ke fa a ma su Bintu za su iya zuwa kallon wasan tunda har da mata za su iya zuwa shi Aji bai ma san an yi haka ba. Ashe har Mimi suka tura ma katin gayyata da sunan za su iya zuwa can Studio domin kallon buga wasan Auran su ita da Aji ba ta dai ce za ta zo ba ko ba za ta zo ba. ****** A can gidan su Mimi ma haka ne an rinca e da shagalin biki lokacin da aka zo ana fa in an aura auran ta sai da ta fa ii ta yi sujudan godiya ga Allah kuka reras ta saka. Dakyar Rukayya ta lallasheta ta yi shuru Allah yasa ba a yi mata kwalliya ba a lokacin sai bayan aurin auran sannan aka ranga a mata kwalliya mai kyau da kayatarwa. Mimi ta yi shigan wani leshi a kallah ya ba ma dubu ari baya mai kalan pick da milk ya yi mata wani irin kyau in da ba ta ta a yi ba hannu da wuyanta da kunnenta gwala gwalai ne, kafarta cikin wani takalmi mai ruwan milk kamar na silba, aramar Jakar hannunta kuwa wajen dubu Hamsi take mai stones tana kyalli sosai kowa ya ganta sai yace ta yi kyau kuma ta burge su ma ba su jira Aji ba Mimi da Rukkya da Wuri su ka yi booking wani h en mai hoto ya zo ya na ta yi musu ruwan hotuna. Sannan Mimi ba ta da awaye daga Mimi sai abokan aikinta na Karamchi kuma da gaske ne masu karamchi ne domin ta ga karamchi. Bikin ya yi da i saboda komai cikin aji da wayewa aka yi shi abincin bikin ma kaf ba anan a ka yi ba aikatau aka ba da sai dai aka kawo shi a dafe kuma Sarve your self ne ba ruwan wani da kai ka ci iya ada din abunda kake bukata. Khadi ta fara orafin ango ba zai zo a yi hotuna ba ne? Mimi ba ta ce komai ba mijin nata ai dl an Kamfani ne ita ina za ta iya cewa ya zo a yo hotuna Mutumin da bai ta a kiranta ba. Rukky ma ba ta yi mgana ba domin ta jima da saka ma Aji suna da mai bakin hali ta ce ba shi da mutumci sam. Mommy ma jama'arta sun zo ma ta lauyoyi daga Abuja sun mata wannan karan, Mimi ta yi kyau duk in da ta gifta kallonta kawai a ke yi masha Allah kawai za a ce, gidan ba hayaniya ko kadldan ballanta ace an saka wani ki a a'a kowa na gefe ana cin abinci wasu na hira ana shan Iskar fanka da ta A.c irin su Khadi suna can haraban gidan wajen wani tanti da mazajensu suna cin abinci suna hira Khadi saboda Isgilanci har tana tambayan mijinta wai ya ga mijin Mimi? Kai tsaye ya ce mata" fantastic ganin sa ya fi jin sa." Hararansa ta yi shi kuma sai ya koma ya na mata dariya saboda ita take kushe Aji a wajensa shi kuma da ya gansa ya tabbatar da namiji ne in aka kira sunan cikakkun Mazac zai amsa. Sun yi family picture ba Abi sai kuma suka tuna shi sai kuka Mommy sai ta rikice gabadaya da kuka domin ita in
Chapter 77 · 0% Book details