Sashe 45
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gina taka rayuwar ba? to ka yi ta kanka Nasir." Daga nan akayi rabuwar baram baram, shi kanshi in da ya san cin zarafin da za'a yi masa a gidansu Mimi kenan har Abada bazai ta a zuwa ba. Hajiya ita ta hana su bin motar haya ta saka Alhaji Hamza ya ba da direbansa ya auke su Mansoor da Mu'azzam, sai garin Abuja Aji ya yi shigar manyan kaya shi da Mu'azzam har da hulunu ko alama bai karaya ba.Sun yi kyakyawan sallama irin ta Masoya da Miminsa, sun iso Abuja da yamman saboda tafiyar mota. Sai dai tun daga bakin get suka fara raina kansu wani makeken gida mai cike da tsaron dakarun Sojoji. Sannan Sojan dake kofar get ya ce bai san da zuwan wasu ba i ba saboda haka ba za su shiga ba sai ya samu izini daga cikin gida. direban ya kalli su Mansoor lokaci aya yana in"To ku kira mana, ina ce asan da zuwan ku." Mu'azzam sai ya kasa mgana sai zaren ido yake yi, Mansoor kuma yana shirin kiran Mimi sai ga sa on ta. "Aji Nah kun isa? "Eh mun Iso, amman wani soja ya hana mu shiga ya ce sai ya samu izini daga cikin gida." Shima ya maida mata da amsa, tana ganin haka ta yi saurin tashi ta je akin Hajiya ta gayamata, Hajiya tace bari ta kira Kabiru sai dai kuma ta yi ta kiransa bai auka ba alhalin sun yi waya da safe ta gaya masa zuwan su Mansoor. Ganin bai auka ba sai ta Kira Murja itama kiran wajen hu u sannan ta auka cikin yar damuwa Hajiya tace"Murja kina ina ita faman kira shuru? Baki sun iso suna waje an hana su shiga." Mommy na jin wani iri ta ce"Hajiya ba ni da wannan ikon, Major ya ce sai shi da kanshi ya ba su izinin shigowa." Hajiya tace"Lafiya me ya faru? Shi kabirun ya ce haka? Mommy ta ce"Hajiya ya hana ni mgana ne, amman na so na kira ki na ce kada yaron nan yazo wlh major ya shirya wulakanta yaron nan ne Hajiya" Da sauri Hajiya ta ce"Innalillahi wa'inna illahirraju'un.." Da kuma sauri ta yanke kiran Mimi hankalinta ya tashi ta ce"Hajiya lafiya? Hajiya ta ce"Maza ki kira Mansoor ki ce direban da yakai su ya juyo da su." Mimi ta dafe kirji kafin ta ce"Me ya faru Hajiya? Abi ne ya kore su? Hajiya ta mike tana fa in"In ma koran ne da sauki, Kabiru ya rufeni a baibai." Hankalin Hajiya duk ya tashi ta kuma ta da hankalin Mimi sai dai Mimi ta yi ta kiran wayar Aji ba ya tafiya, Hajiya ta saka ta kira Alhaji Hamza Daddy shi kuma suna wajen taron siyasa bai aga wayar ba Hajiya ta kasa zama waje aya fa i kawai ta ke yi" In har kabiru ya wulakanta yaran nan ba zan yafe masa ba." Hankalin Mimi ya tashi ta fara kuka ta yi ta turama Aji sako. "Aji Nah kun shiga gidan? "Hajiya ta ce ku juyo Abi ba zai amince ba.". Amman ina shuru kuma ko an kira wayar ba ta shiga, su kuma a lokacin suna nan a kofar gida kamar wasu kayan wanki, saboda direban da ya kai su ya ce kai su kawai akace ya yi nan ya zube su ya juya mota ya yi tafiyarsa, abun tausayi Mansoor da Mu'azzam zaune a kofar gidan su Mimi tun karfe biyar har aka yi mangariba, sojan nan ba Imani a ranshi tuni ya shige ciki ya rufe get sai a Aji ne ya gangara can bakin hanya ya siyo musu ruwa suka yi alwala suka yi salla akan dandalin Kofar gidan su Mimi. Mu'azzam ya gaji ga yunwa ga kishi cikin galabaita ya kalli Mansoor dake nuna dakiya ya ce"Yayanmu ka kira Mimi mana, wlh na gaji da zama anan." Shuru ya yi ya na wani tunani, da gaske a san da zuwan su amman me ya sa za'a kira su daga wani gari kuma a tozarta su?. aramar wayarsa ya duba sai ga layinsa Emergency ba ya iya ma kira sai kawai ya kalli Mu'azzam kafin ya ce"Ba Network, mu kara jira dai mu gani." Tun suna ganin abun wasa har dai suka tabbatar da an kira su ne domin aci zarafin su. Sauro sun yagi rabon su ajikinsu, su ne anan kamar wasu almajirai har karfe goman dare. Mu'azzam yunwa ya ke ji kuma gashi anguwan ta masu ku i ce babu masu saidae saide a wajen. Mansoor yace bari ya je can bakin titi ya gani ko zai samu ko mai doya ne ya siya musu. Mu'azzam ya rike masa hannu ya na fa inn"Mu tafi gida, daman an kira mu ne domin a ga an wulakantamu." Aji ya yi shuru yana kallon aninsa da yunwa ta galabaitar dashi daman a hanya gurasa ka ai suka siya kuma ba ta da wani yawa.. Shi kan shi ya na yin dauriya ne, amman ya ku sa gazawa. Soyayyar Mimi ta makantar da shi da ganin laifin abin da ke shirin faruwa. Kafin ma Aji ya samu zarafin mgana sai ga wata katuwar mota ta zo za ta shiga gidan, direban ma soja ne sun ga dai ya tsaya Sojan da ke gadi ya sunkuya ya yi masa mgana su ka ji yana fa in" Yes Sir..! Motar na shigewa Sojan ya zo ya ce musu su tashi su shiga ciki in ji Oga. Jiki duk ya saki Aji ne mai kaurin jiki Mu'azzam duk ya gama laushi. Ashe ba cikin gida za'a kai su ba nan katon haraban gidan aka ce su zauna su jira tun suna san ran ganin an zo an kira su har suka sare haka Mu'azzam ya fara amai sai ruwa saboda yunwa. Hankalin Mansoor ya tashi saboda Kaninsa na gaba da soyayyar Mimi. Kokarin fita daga gidan ya ke yi saboda ya je ya samo ma aninsa abunda zai saka a bakinsa. Sojan nan ya ce Oga bai ce su bar shi ya fita ba, ransa ya aci zuciyarsa ta yunkuro daman ga shi ba ta da kyau balle kuma an ata mata. Sai ya yi kokarin fita da karfi wannan Sojan ya saka katon takalmin kafarsa ya shure shi sai da ya fa i. Mu'azzan na ganin haka ya tashi sai ya ma daina jin jiri ya je ya rike an uwansa yana ba ma Sojan hakuri da har ya fara nuna Mansoor da bindiga. Dakyar ya hakura sai da wani sojan su masu tsaron kofar shiga gidan ne ya yi masa mgana cikin harshen turanci sannan ya yaleshi. Shi kuma Mansoor sai faman sakin huci yake ke yi, an riga an yi sara kan ga Kuma a dai dai lokacin megidan ya ce a shigo da su kamar zai ce sun fasa shiga sai kuma wata zuciyar ta ce ya je ya ga waye wannan Mutumin da ya ke da zarran wulakanta shi, sai ya mi e shi da Mu'azzam sun yi laushi kamar lawashi, Allah yasa daga su sai kayan jikinsu da ai sun rena kansu. Soja nan na gaba suna bin shi a baya haka suka shiga falon gidan, Ba kowa a falon sai Abi ya na zaune kafa aya kan aya ga bindiga a saman tuburen dake gabanshi suna shigowa ya mike a fusace bayan ya yi ma Sojan da ya rakaso alamun ya bar falon. Sai da ya fice sannan ya musu wani matsiyancin kallo Mu'azzam ne ya yi saurin zubewa a saman cafet domin ya kasa iya tsayuwa cikin muryan da ta ji jiki ya gaishe da Abi ko kallonsa bai yi ba cikin araji ya ce"Wane ne daga cikin ku yake son Mimi? Ya fa a kai tsaye cikin takama Mu'azzam ya tsorata domin ko iya kallon Major Kabir bai yi ba saboda ya yi masa kwarjini sannan muryansa ma ka ai abun tsoro ne. Mansoor na tsaye i kam ya ce"Ga ni nan.." Major Kabir ya tako har kusa da shi ya kallesa daga sama har kasa a ransa yana fadin lalle yaga tsaurin idon yaron. Cikin Yanayin maaganarsa ya ce" Wani zarra gare ka da ya sa har ka iya takowa gidana acikin falona kana gayamin kai ne kake son Mimi? Kai ne ka hure mata kunni take kokarin sa a ma umarnina miye matakin da ka taka a rayuwa? Ya fa a yana kallon Mansoor da ya yi kamar bai ji shi ba, ya dunkule hannunsa kamar zai kai naushi sai faman huci yake saki kamar shi ne Sojan ma. Major kabir ya kallesa cikin mamaki kafin ya daka masa tsawa yana fa in" Ina tambayarka kana min shuru? kuma ina mgana kana tsaye? Ka rage tsawon ka a asa na ce.!" Ya fa a a tsawace amman goganka ko gezau sai ma Mu'azzam da ya kallah cikin fitar numfashi ya ce"Tashi mu tafi Mu'azzam." Major kabir ya ga kamar Mansoor ya raina shi ya zo har gidan shi bayan ya aikata masa wannan laifin kuma yana masa mgana shi zai nuna ma jan wuya lalle bai san me ake kira da Soja ba yau zai sani. Magana kawai ya yi sai ga sojoji kusan hu u sun bayyana afalon cikin huci nan da nan ya ba su umarnin su rike masa Mansoor su ban are shi, Mu'azzam ya fashe da kuka yana fa iin"Ka yi hakuri don Allah kada ka saka a dake shi." Cikin fusata Major kabir ke fa in "Kamar ni? Kamar ni wani talakan agolan da ubansa har ya mutu a auye, tarihin rayuwarsa kaf babu abun mamora. Yaron da uwarsa ke aiki a karkashin mahaifiyata ba ka da wani Future mai inganci anan gaba, ka yi min laifin ka yi soyayya da ata ba da sanina ba ka hure mata kunne ta sa a ma umarnina maimakon ka nemi afuwata sai ka zo har gabana kana min takama. Who are u.? "I SAID WHO ARE U...? Ya ara fa a cikin matsancin tsawa, ya kuma saka kafarsa lokaci aya ya daki kasa sai da suka ji karan bugun takalminsa Mu'azzam tsoro ya kama shi ya fara makyarkyata shi kuma Mansoor Major Kabir ya ce su ban are masa shi nan da nan ko