Sashe 123
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
falon ba, duk yadda Mimi ke da son yara wannan karon ba ta bi ta kan su ba, Hajiya da ta ga Mommy ta damu sai ta ce ta kyaleta ta huta in ma wani abin ke damun ta za ta warware daga baya. Mommy ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Hajiya ko dai Mimi ba ta farinciki a wannan gidan ne? Hajiya ta girgiza kanta kafin ta ce" A'a kar mu zo wannan ga ar, sai dai kila matsalolin yau da gobe na tsakanin zamantakewar ma'aurata guda biyu. Amman kada ki damu ba wata matsala ina da kyakyawan tabbacin cewa Meri ba za ta ta a bari wani abu mara kyau ya samu Binta ba." Mommy ta jinjina kai kafin ta ce"Hakane! Na fi tunanin ila saboda rashin zuwan mijin nata ne." Hajiya ta yi wani irin dariyan su na manya kafin ta ce" To ai wannan kuma bai kama ta ta damu ba. Ba kuma lalle ne sai an takura masa ya shiga cikin hidimar mu ba, ana tafe dai wata rana da kanshi zai zo ya gaisheki ba tare da ita kanta Binta ta sani ba, ka dai a yi gaggawa a bi komai a sannu." Mommy ta yi shuru ba ta yi mgana ba Hajiya ta dafa kafa arta lokaci aya tana fa in" Kar ki damu komai zai yi dai dai in sha Allahu." Daga nan suka bar maganan sai su ka gangara kan mgananr gadon yaran da ya sa ta kira yaran daman tana so ne Khadi da Mimi a dan ama Mazajensu ha insu su rike musu, in kuma su za su iya ri e ku in su shike nan daman a ha i mazajensu su zama shaida a kan dukiyar su. Ko da daddare eajen cin abinci a dinning table, ba ta wani saki jikinta ba tsakuran ma abincin ta yi ta tashi, Mommy ta bi ta da kallo kafin ta ce" Mimi baki ci komai ba fa? Yamutsa fuska ta yi kafin ta ce" Cikina ya cika ne Mommy. Kuma ai naci da yawa kin gani." Ta fa a tana nuna mata filet in gabanta wanda ko rabi ba ta ci ba, Mommy za ta yi mgana Hajiya ta hana ta sai ita ce ta kalli Mimi lokaci aya tana fa in" Tunda ya ishe ki shike nan Binta." Mimi ta ka a Lokaci aya tana fa in" Zan shiga ciki, sai da safen ku." Suka amsa mata da sai da safe, Mommy ta bi ta da kallo Khadi ce ta ijiye cokalin hannunta tama mai fa in" Mommy ba ki lura wani abu na damun Mimi ba? Ta zama wata so cool da ita." Madiha na cin abincin ta ba ta yi mgana ba, sai Muhammad ne ya ce" Kila saboda gajiyan tafiya zuwa gobe za ta warware." Khadi ta yi shuru kafin ta ce" Anya? duk da haka dai yau ta zama wata iri, wani abu na faruwa, Mommy ba ta fa a miki wani abu ba? "Ki tambayi Hajiya, za ta fi Mommy sanin wani abu tunda tare su ke acan, Hajiya me ke faruwa ne? Madiha ta fa a kai tsaye tana kallon Hajiya, ita kuma sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kowani an adam yana da matsalolinsa, ba ta fa a min komai ba ni kuma ban matsa mata sai naji ba, Binta matar aure ce tana da iyalai yana da kyau a bar ta tayi fafutukan rayuwarta da zamantakewar ta, tunda ita mace ce, wata rana kuma ita in uwa ce" Muhammad ya jinjina kai kafin ya ce" haskiya ne Hajiya. Mtsalolin nan na rayuwa kowa na fuskantar su,sai dai na wani ya fi na wani kawai." Hajiya ta amshe da cewa" kuma ba duka muke iya sanin matsalolin junan mu ba, wani ma rashin bayyana sa yafi alheri saboda zai iya zama in wani ya sani ya kasa sukunin rike damuwar, shi ya sa kar ka matsa a dole sai ka san damuwar wani in har ba shi ya yi niyar sanar da kai da kansa ba." Kowa ya nuna ya gamsu da bayanin Hajiya amman ban da Madiha da ta ta e baki kawai, domin har Hajiyan tana jin haushi domin da aurin gindinta komai ya faaru. Ita dai Mimi tana akin ta, ba ta san wainar da suke toyawa ba. Allah ya taimake ta da wuri ta yi barci, sun yi waya da Rukky sama sama sannan ta Kira wayar Inna Meri suka yi magana ta sanar da ita ta isa tun azu. Ba su jima suna mgana ba ta ce dai an gaishe mata da Hajiya da Mommy daga karshe ta ba ma walida wayar suka gaisa. Har barci ya auke ta tana tunanin Aji, ace ko ya kira ta ya ji yadda take? Wato ko a jikinsa bai damu ba duk sai gwiwarta ta yi sanyi ta ji ga adaya auran da shi kan shi Ajin sun fara fita daga kanta, ta fara hango Rayuwarta nan gaba ba tare da shi ba matukar bai gyara ba to rayuwa ba za ta yi da i ba, Ta fara hango kanta ta samu wani mijin ta aura ta zauna lafiya da daidaiciyar rayuwa. Washegari tun kafin azahar Dr da Iyalansa suka sauka a Abuja sai gidan ya ara aukan Murna Shi kan shi Dr da Mimi ta zo su gaisa sai da ya tambayae ta ko ba ta da lafiya ne? Ta ce lafiyan ta kalau akwai dai gajiyan zirga zirga ne a tare da ita. Zuwan su ma ya sa ta an Saki Jikinta Tunda suna asawa da Jawahir mai ciki, ashe daman ciki ne ke wahalar da ita Tun auran Mimi ga shi nan ya fito, sannan ta shaku da mai sunan Mommy tun zamanta tare da su a kano sai zuwan su ya yi awon gaba da kaso mafi girma daga cikin zuciyar ta. Ranar yini a ka yi zaman hira, Mommy daman ba ta je aiki ba tana gida tare da anta da surukanta da iwar mijinta da aka dun ule aka zama aya gaba aya. Khadi daman irin ta irin mijinta haka ma Madiha irin ta, irin mijinta ne, shi ya sa ba kasafai ra'ayin su ke zama aya da su Khadi ba ballantana Dr da ba ruwan shi ga sanyin halin itama matarsa Jaawahir haka take ba ta da mgana sosai. A ranar dai an ji hiran Mimi har suka ta a halin ita da khadi da gaddama ta sarke su sai da Dr ya raba fa an, Sai hakan ya saka damuwarta ta ragu, ta fara sakin jikinta cikin an'uwanta tana walwala. Tuni ta fara kokarin mantawa da abin da ta baro ta yi tunanin gwara ta ijiye matsalan shi a gefe ta fuskanci rayuwarta anan gabam Sannan za ta mori wannan hutun tare da iyayenta da an'uwanta, sun zauna sun tuna da mahaifinsu suka yi masa addu'a. Mimi har kuka sai da ta yi ita da Mommy sauran kuma sai dai suka share kwalla. Vhajiya ke ta musu nasihan su daina kuka addu'an dai ita Kabiru ke bukata, Allah ya kai masa rahama a kabarin sa. Sai daddare bayan an gama yin dinner suka koma falo kowa da kowa aka zazzauna Dr. Sulaiman shi ya bu e taron da addu'a sannan ya kora jawabin sa, tunda ku in gadon Khadi da Mimi suna hannun shi ne, Mommy itama ta yi nata bayanin ta ce kowacce za a ba ta gadon ta ko ta ba ma mijinta ko ta siya hannun jari ko ta siya gold ta ijiye, sannan tana so su ha a hannu su gina masallaci Domin ladan ya kai kabirin Abi. Kowa ya yi na'am da shawaranta, Ita Khadi ta ce a raba ku in ta biyu rabin sai ta auka rabin a ha a a yi hidimar gyaran masallaci sauran gidajen da suka gada kuma za su bar shi saboda adara anan gaba, ita kuma Mimi sai kuka kawai take yi ta kasa mgana Hajiya daman ta ce ita komai ba ta so, duka abin da ta gada a auka a ha a wajen gina masallacin wanda ake shawaran a inda za'a gina masallaci kowa na ba da na shi shawaran ita dai Hajiya ta ce a nemi wani gari anguwan da ba yawan masallatai sai a gina musu sada tul jariya, Muhammad kuma ya ara cewa za'a iya yin tuka tuka na ruwa a anguwannin da suke wahalar ruwa, Mommy ta ce wannan ma shawara. Mimi dai sai faman sharan walla take yi ba ta ce komai ba, Dr ya kalle ta lokaci aya yana fa in" Mimi ki yi hakuri kin ji ko? addu'a Abi ke bukata.". Sai ta gya a masa kai, nan ya ce" Ina shi Mijin naki? bai samu zuwa ba ne? Da kai ta ba shi amsa, shi kuma daman ba mai damuwa ba ne sai kawai ya jinjina kai kafin yac e" Ba matsala abin da aka tattauna za ki iya sanar da shi game da dukiyar ki, ko ba zai amsa ba yana da hakkin ya sani kamar yadda Mommy ta ce." Kan Mimi na asa ta ce" Ni a auka duka a yi amfani da kudin wajen sada atul jariya ladan ya kai ma Abi acikin kabarin sa." Sai kawai ta ara fashewa da kuka Hajiya tace a'a tana da bukata ta auki rabi sai ta ba da rabi, ha in ta ne kuma tana da sauran kuruciya itama saboda komai na rayuwarta na wuyan daddy ne ba ta da bukatar ku i, komai take so tana samu shi ya sa ta sadaukar da abin da ta samu ga sadakatul jariya Sai anan Mimin ta ce a raba itama nata gida biyu a ba ta rabi, rabin kuma a yi amfani da shi. Daman kuma ku in Dr ya saka su a hannun Jari na shekara aya to shekaran ta yi ku i sun dawo har da uban riban da aka samu. Madiha daman tuni ku inta na hannunta sai dai sauran kaddarori kamar gidajen da suka mallaka, ita sai ta ce za su ba da iya abin da za su iya ita da mijinta in sha Allahu. Har an gama tattaunawar an tsaya a za a yi masallacin a