← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 208

Sashe 70

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta koma ta zauna gefen gado ta dafe kanta sai hawaye ina laifinta domin ta amince da auran wanda take so? Ita ba ta ga laifi ba domin tun a farko ai shi aka sa ama wa, me ye aciki domin an je an ba shi hakuri ai ya cancanta ne. Kuka ta yi ta yi, Hajiya ma ta san za'a yi haka tun da ta ga Yaddiko ta tasa Bintar da mgana ta san sai sun sakata kuka haka ta zo ta isketa tana ta kuka kwance a kan gado. Hajiya a ka bari da lallashinta, Mimi fa i ke yi" Hajiya mene laifi in n cce zan auri Mansoor? Ko shi menene laifinsa a wannan maganar? Hajiya ta ce"Share hawayen ki, ba ki da laifi shi ma kuma ba shi da laifi a wajena." Ashe har gwara Madiha ma Khadi sai da suka yi kaca kaca da Mimi domin kai tsaye ta ce" Mimi da gaske ne fa Yaro nan ba Ajin ki ba ne wlh, an san dai ba'a kyauta masa daga farko ba amman miye na wani zubar da daraja don Allah? Ko a saninsa da na yi a baya gayen ba shi da wani kwarjini da gaske fa takala ne an takala mai rayuwa a anguwar talakawa me ya tara? Auran wahala za ki je ki yi kina yi ma uwarsa bauta da shi kanshi aikin banza kawai." Ita kuma Mimi ta ce ina ruwanta? ta ji ta gani ta na son abunta a haka Khadi ta ce"Wait wai me kika gani a wajen wannan ba in yaron da kika kasa daina son sa ne? Kai Tsaye Mimi ta ce" Abin da kika gani a jikin Muhammad har ki ka aure shi." Sai Khadi taji haushi ta fara Masifa ta na fa in" ke kada ki kuskura ki ce za ki ha a mijina da wannan banzan saurayin naki, kinsan dai ya fi arfinsa da duk abunda ki ke tunanin ya mallaka da duka danginsa gaba aya, in ma kina tunanin wai ya na wallo to uban wa ma ya san shi ko iya walln anguwanni ne, domim ba wanda ya san sunan shi cikin jerin sunayen an wallon kafan naija rubbish kawai." Itama Mimi ta gatsina mata magana da cewa" Ko ma dai menene kowa da sandan hannunsa yake duka." Kowa ya katse wayarsa ya na huci Dr ne kawai ya kirata suka yi mgana ta fahimta shi da ya ke har Abuja Mommy ta kira shi ya je ta yi masa bayani sauran kuma daman ta waya ta sanar da su suka nuna ba sa goyon baya. Shi dai Dr tunda ya ce "Kina son shi Mimi? Za ki iya zaman aure da shi? Ta ce eh shi daganan yasa ki ya yi ma ta fatan alheri a fili da sarari. Saboda Mimi ta ce idan an an ciza, to ya kamata a hura, ka da a zo daga baya kuma nadama. Cikin kwana biyu labarin za a zo kawo sadakin Mimi ya je kunnen kowa har Jaheed haka ya kira Mimi kamar ya yi kuka yana fa in" Yanzu har wani can bare ya fini a wajen ki Mimi? Ita nata kawai ka yi Hakuri Jaheed har Hajiya ya kira yana ce mata ta za i wani bare a kansa kai tsaye Hajiya ta ce" ba haka ba ne, na dai za i farincikin Binta ne." Da har garin ya so ya dawo Daddy ya kira shi yace a kul insa kada ya ji ya zo garin nan ya zauna ya yi aikinsa shi yasa bai zo ba amman ya yi kuka bai auka Mimi za ta yi masa haka ba. Sannan shi bai ma wani samu bayanin wanda Mimin ke so ba ya dai san mganar tuntuni amman kuma yasan bai fishi komai ba a yanayin ma abunda ya raba su tun farko. Bangaren Mimi kuma ta kasa fa a ma kowa hatta da Rukky ta bari sai sun zo sannan, kuma abunda ke ba ta mamaki tun daga wannan sakon Aji bai kara ce mata komai ba, ba kira ba sako kuma ta yi masa sallama ta chart ya yi ticking biyu alamun ya shiga amman bai bu e sa onta ba, ita kuma ta na ji a jikinta Mansoor na sonta sai dai kuma wani lokacin Jikinta na sanyi in ta ga yadda ya ke tafiyar da ita amman tunda ta ji ta gani ba ta nuna gazawarta ba. ****** Ranar Alhamis Mu'azzam da Iyalansa su ka iso Gombe, ballatana ma tunda ya ji harda shi za'a je kai sadakin auran Mansoor sai bakinsa ya ki rufuwa. Daman tun a jiya Baba anjuma ya yi mgana da su Baba Sani kan zuwa gidan su Mimi tunda Hajiya ta ce gidan Sanata za su je, Sanda su ka ji mganar sun yi ta mamaki shi kuma Baba anjuma ya ce kaddara Allah ya kaddara ita in matar ce. Sai kaji mganganu na tashi cikin gida, sauran yaran Inna Meri daman sun sani Walida har gida ta je ta sanar da Bintu, Bintu ta yi uban shewa ta buga cinya kafin ta ce"Kai akwai shagali a gidan Wanzamai" Sai kuma ta kara bushewa da dariya kafin ta ce"Kai Baban Inna an bala'i ne, wai akin nan na lungun Inna anan zai saka wannan yar gayun? Sai ta ara saka dariya kafin ta ce" Lallai za'a ga zama a gidan Wanzamai." Yaya Halima kuma daman ta zo gidan Inna Meri ta fa a mata kowa ya ji sai ya yi mamaki, sai dai a cikin kasan ransu su san kanin na su yana nufin wani abu gaskiya. Mu'azzam kuwa bai yi gaggawar sanar da su Nasir ba ya bari sai sun je sun dawo tukunna, Baba anjuma bai yi gaban kanshi ba sai da ya kira Baba Yakubu suka yi mgana kan Mansoor su kuma su ka bashi dukkan wata dama a cewarsa ai shine uban Mansoor har abada alhakin neman auransa ai ya na hannunsa ne shiyasa ya nemi abokinsan Mallam Hashimu sai Baba Sani da anlami da Mu'azzam. Mansoor bai zo gidan ba sai da Mu'azzam ya zo gari yaje gidansa su ka kwana washegari jumma'a ya aukosa suka zo da daddare. Daman ya ciro ku i Dubu dari biyu ya ba ma Baba anjuma ya ce in sadakinta ya wuce haka su dawo bai ce a cika masa ba Inna Meri daman tuni ta daina mgana domin sanin Halin Baban inna kunyata mutum zai yi. Washegari 16 July 2022 ranar Asabar da Misalin karfe goma na safe suna gidan tsohon Sanata Alhaji Hamza kuma sun samu tarba mai kyau kwarai da gaske, da ga shi sai mijin Yaddiko da wani abokinsa Honorable Jamilu. Umarnin Hajiya ne shi yasa ba zai iya yin wani abu da ranta zai so su ba, amman bai wani saki fuska ba, ba Laifi sun gyara jikinsu su Baba Sani ne sai a hankali sai faman kalle kalle su ke yi suna taba juna an kosa a fita a yi gulma an gabatar da gaisuwa Baba anjuma ya mi aa ma Alhaji Hamza Hannu su ka yi musabaha su ka gaisa Baba anjuma ya ce" Alhaji ya hakuri kuma? Allah ya ji an sa da Rahama." Ya amsa da Amin Amin. Bayan kawo musu ruwa da Lemu ha e da abun ci irin su samosa da Cake sai aka fara mganar da suka taru domin shi. Sun nemi da Alhaji Hamza shi zai yanke musu Sadaki tare da saka rana amman suna ga ya masa aron ya ce ba ya son bikin ya wuce wata biyu shi kuma haushi ya kama shi tunda daman shi ya saka Shara insa sai kawai ya ce Sadaki dubu Hamsin mamaki ya kama su amman ba wanda ya yi mgana, su ka kirga suka ba da Alhaji Hamza ya ce an saka rana nan da wata biyu kamar yadda shi Mansoor ya bukata. Duka duka zaman bai gama cika mintina talatin ba taron ya ta shi Ko ruwa ba su sha ba Gwara Baba Sani da Baba Danlami sun sha ruwa sun kuma sha lemu sannan da za su tafi tunda a Motar Mu'azzam ne sai Alhaji Hamza ya saka a ka kwashe aka saka musu a mota. Suka rabu suna ma juna gdiya sai bayan Tafiyar su Mijin Yaddiko ya kalli Alhaji Hamza yana fa in " Wannan wani irin aure ne? ba goro ba minti? Alhaji Hamza ya ce' Irin shi suke so ayi shi ya sa." Daganan ya kama bakin shi, suma daga nan suka yi sallama shi ma kuma da ya shiga cikin gida bai yarda ya yi mganar da su Mama ba,gim ya yi da ransa ya sake shiri ya fita sai dare ya je gidan Hajiya ya kai mata Sadakin da kuma ranar da ya saka. auka ma Hajiya za ta ce Sadakin ya yi ka an sai ya ji ba ta yi mgana ba sai dai ta yi ta saka albarka ta ce ya ijiye sadakin a Hannunsa ai uban Binta ya ke bai yi gaddama ba ya ta fi da shi gida sai da ya koma ne ya yi ma Mama bayani an kawo sadaki dubu Hamsin an saka rana nan da wata biyu. Mama ta jinjina sadakin amman ba ta yi mgana ba, kada ta tofa ace tana jin haushi saboda Jaheed amman auran nan kamar ya zama askanci ga Mimi tafi karfin wannan sadakin duk da sadaki ba ya ka an kuma ba yawa amman in aka cika ba zai zama Laifi ba. Amman aure haka kai tsaye ba wani abu haba ai ba haka ake yi ba, sai dai bakinta anin kafanta ganin shi kan shi wanda ke matsayin Uban nata bai ja da mganar ba. Haka su Mu'azzam suka koma gida da Labarin abunda ya faru Mansoor kuma sa o Mu'azzam ya tura masa ya sanar da shi ko da su ka koma akin Inna Meri ya cika da anta da Jikokinta Bintu har Mp ta zo da shi Mu'azzam na shigowa da labarin an saka rana ta kure wakar kujeran Tsakar gida Inna Meri na a'a ba ta saurare ta ba, su Yaya Amina na zaune suna ta dariya Hibba ce mai conecting da wayarta ma,
Chapter 70 · 0% Book details