Sashe 53
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kada ku ara kirana da irin wannan shirmen na ku" Nasir ya ce"Aji rasuwa fa aka yi? mutuwa ce fa" aramin tsaki ya ja kafin ya ce"ka bari in ka mutu in ta kirani ta min gaisuwa sai na ha a na yi mata a lokacin." Daga haka katse wayarsa ya bar Nasir da sakin baki, Kuma a daran ta turo masa sa o. Mamaki ya kama shi wato kenan sun ba ta lambar sa kenan. Goge sa on ya yi ya kuma auki lambar ya saka ta a blacklist duk abunda zai ha asa da abin da zai hana shi barci yana kokarin yin nesa da shi. Ko alama bai ji tausayinta domin wai ta rasa mahaifinta ba, shi a tunaninsa wannan in ya rasu ma abun murna an rage mugun iri a kasa ne, sauran ka an ya maida mata amsa da cewa Allah yasa kasa ta kara danne shi sai kuma ya fasa shuru ma ai amsa ce ga mai hankali. *BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KU IN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WA ANNAN LAMBOBIN.* *09069067488* *80032773332* an kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sau i, ku yi min magana ta wannan lambar* *09069067488* *NA GODE.* *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255 *Page 17* Kimanin sati uku kenan da rasuwar Major Kabir Sulaiman Dabo, zukata sun fara aukan dangana tuni baki na nesa da na kusa sun gama zaman makoki sun koma gidajen su. Ciki harda Dr. Sulaiman da iyalansa sai Madiha wanda daman mijinta ana yin bakwai ya koma da yara ita kuma sai da akayi kwana goma sannan ta koma. Khadija kuma sati biyu ta yi sannan itama ta koma, itama dai kamar mijin Madiha ranar bakwai mijinta ya koma tare da yara, sai a ka bar Mimi da Hajiya sai Inna Zainaba sai kuma Inna Ladidi wacce take autarsu mahaifiyar Mommy mai rasuwa ita ka ai ta rage musu a raye a akin su. Hatta iyalan Alhaji Hamza sun dawo Gombe Hajiya kuma da Mimi sai da aka yi sati uku sannan suka yi shirin dawowa saboda ita Mimi aikinta, ita kuma Hajiya saboda makota suna ta zuwa mata gaisuwa ba ta nan. Mommy dai ta auki dangana amman fa sai ana yi ana lallashi duk sanda ta tuna sai kuka rana ba ta ta a fitowa ta fa i ba tare da ta tuna da yau ta yi rashin miji ba. Ranar da su Hajiya su ka koma sai mutuwar ta dawo musu sabuwa Hajiya ta yi kuka, kukan da ba ta yi ba lokacin da aka yi mutuwar sai yanzu Mimi ma kamar ita ka ai aka yi ma mutuwar duk ta rame kamar ba ita ba, itama ta kasa gasgasta yau babu Abi gani take yi kamar in ta shiga Bedroom din Mommy za ta ganshi. Sai dai ina wanda ya mutu ba ya dawowa tafiya ce ta har abada sai dai fatan Allah ya ha amu a darussalam. Mommy ma ai ta ga kara daga abokan aikinta Saboda macece mai kirki da fara'a ita Mimi ta auko wajen fara'a da iya mu'amala. Haka su Hajiya suka dawo suka bar Mommy cikin kewa Allah yasa ma ga Inna Zainabu da Inna Ladidi, ita dai Inna Zainabu ana yin arba'in za ta koma kano Inna Ladidin ne za ta zauna da Mommy har ta fita takaba. Tun da suka dawo daga Abuja yan anguwa da makota su ka ji Labarin Hajiya ta dawo a ke ta shigowa yi mata gaisuwa daga bangaran abokan siyasar Daddy ma suna ta zuwa wa anda ba su samu zuwa can Abujan ba, har da yan'uwan su Anty da Mama da suma ba su samu zuwa can ba duk jin Hajiya ta dawo ya sa suke ta zuwa yi mata gaisuwa tare da yan'uwan mijin Yaddiko da sauran mazajen ya'yanta da ba su zuwa can Abuja ba, daman ita saboda ba ta jin da i kwana takwas ta yi ta biyo Alhaji Hamza suka dawo gida. Ita Mimi ana zuwa mata gaisuwa daga wajen aikinta harda wasu mutanen da ba ta ta a sani ba kiranta kawai a ke yi ace ta ba da address, ita kam ai ta ga kara kuma har acikin ranta taji da ii Rukayya kaf da iyayenta sun zo mata gaisuwa har Bibi sun zo tare da Usman kamar ta yi masa maganar Aji amman sai ta fasa. Saboda ta na da tabbacin ya ji labarin babu amfani ta ci gaba da bibiyar ya sani ko bai sani ba tunda ita da ta tura masa sako da hannunta tana da tabbacin ya sani. Tun da suka dawo ba ta koma ma wajen aiki ba so take yi sai ta samu yar natsuwa. A halin da ta ke jin zuciyarta a lokacin ba za ta iya samun wani sukunin komawa wajen aiki ba. Sai dai ta yi ta kwanciya a gida da kumburarrun idanuwana ba ta da aiki sai tunani Hajiya kuma kullum da carbi tana falo ita da Baaba Uwani, ita da ba ta nan ma aka yi rasuwar ta je kumo. Hajiya ce ta koma ma lallashin Mimi in ta ganta cikin damuwa ta kan ce ma ta"Binta ba kuka ko damuwa Kabiru ke bukata yanzu daga garemu ba, addu'armu ita ya fi bukata shi ya sa na ce gwara ki koma wajen aiki zai rage miki zaman ka aici da tunane tunanen rayuwa." Jin Hajiya kawai ta ke yi ai ita duniyarta cike take da abun tunani saboda haka ya zame mata dole ta yi kuka sannan kuma ta yi tunani. Ko bayan dawowarsu Mu'azzam ya sake kiranta ya yi mata gaisuwa sai take gaya masa sun baro Abuja suna gida ita da Hajiya, nan ya yi mata alkwarin zuwa ya yi mata gaisuwa in sha Allahu in ya shigo garin. Yadda ba ta yi ma Makama maganar Aji ba shima ba ta yi masa ba, ita a tunanin nutuwa ta kore komai, abin da ba ta sani ba mutuwa ba ta kore ko da kankanin tsanar da Aji ya yi ma mahaifinta ba. **** *Saturday 27 March, 2022* GRA. 11:16am. Yau gidan Hajiya na cike da baki an Yaddiko guda biyu mata da ans suka kara zuwa yi ma Hajiya haisuwa, sai kuma baki daga can kumo suma mota guda da suka zo yi ma Hajiya gaisuwa. Mimi na cikin aki tare da Rukky da ta zo azu daga wajen aiki Hajiya na falo tare da ba inta, kamar ita take yin takaban ko da yaushe da hijabi da carbi. A dai dai lokacin Inna Meri tare da Bintu da Walida sai yan biyun Bintu Hassan da Husaini suka shigo gidan, kuma har a ran Inna Meri sai da ta ce gidan ya na nan a yadda ta san shi sai dai ya samu gyare gyare da ba'a rasa ba. Da ya ke tun a baya ta san kan gidan ita ce a gaba suna bin ta a baya har cikin falon Hajiya da farko Hajiya ba ta gane Inna Meri ba saboda yanzu jikinta ba wahala tana samun hutu da jin da in rayuwa. Sai bayan da ta yi mata gaisuwa ta ga ba ta gane ta ba sai ta gyara zama tana mirmishi kafin ta ce"Ba ki gane ni ba ko Hajiya?. Hajiya ta kalli Inna Meri da kyau kafin ta yi salati ta dire tana fa in "Kai jama'a kada ki ce min Meri ce maman baban inna." Inna Meri na dariya ta ce"Ni ce Hajiya." Nan fa Hajiya ta rasa ina za ta saka kanta saboda farinciki, bakinta yaki rufuwa ta rike hannayen Inna Meri duka biyu tana fadin"Allah Sarki Meri ashe rai zai kara ganin rai? Ki yi hakuri Meri kunya da nauyi sun hanani na kara neman ki, ki yafeni" Ta fa a lokaci aya tana yi kamar ta fashe da kuka da sauri Inna Meri ta ce"Haba Hajiya bakomai, nima ki yafemin ai nima ban kara neman ki ba ookacin ina cikin ru u ne shi ya sa amman naji rasuwar a gidan tibi kuma jiya an Inna da muka yi waya yake fa amin kun dawo nace daman na yi alkwarin sai na zo na yi miki gaisuwa in sha Allahu" Hajiya ta ji da i har cikin ranta sai mirmishi take yi Walida da Binta da kalla kafin ta ce" Meri kada dai kice min yan matan nan naki ne suka girma haka? Bintu ce ta fara sakin dariya ta rufe fuska kafin ta ce"Hajiya Bintu ce fa, ga Walida." Ta fa a ta na nuna Walida Hajiya ta rike baki cikin mamaki kafin ta ce"Ikon Rabbi. Bintu ke ce haka? Sai kuma ta kalli Walida lokaci aya ta na fa in"Ba shakka shekarun da yawa Walida an zama yan mata, to wa annan yaran fa? Inna Meri ta tura mata su Husaaini gabanta tana fadin"Jikokin ki ne Hajiya, yaran wajen Bintu ne yan biyu ne ga su nan Hassan da Husaini." Hajiya ta ri esu kusa da ita ta na fa in"Ba shakka , yara nan Allah ya raya ku kun ji ko? Ta fada ta na shafa kawunan su duka biyu, su kuma suna ta kallonta. Kara gaisawa suka yi Inna Meri ta kara yi mata gaisuwa Hajiya ta ce"Uhm ke dai bari Meri Kabiru ashe ba'a de o da yawa ba." Inna Meri ta ce"Allah ya sa an huta Allah ya kyautata tamu bayan ta su.". Hajiya ta yi ta amsa da Amin Amin, ganin mutane sun