← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 208

Sashe 201

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ina son ki, in na kalle ki kina burgeki sha'awan ki na kamani, amman ace abun hauahi da ba in ciki ni a matsayina na wanda Ubangiji ya yarje min ba ni da ikon kallon ki ni ka ai na yaba, da wanda ya dace da wanda bai dace ba, kowa kallon fuskarki yake yi ya na yabawa. Wallahi Tallahi ko aikin nan da kika ga na barki kina yi ba a son raina ba ne Fatima , ina da kishi kishin da ni ka ai na ke son na yi ta kallon ki ina yabawa. Amman ya zan yi? Yanzu ina hanaki wannan aiki sai ace ni mugu ne ba ni da adalci na ganki da aikin ki na aure ki kuma na rabaki da shi an'uwanki su zageni ke ma a ranki ko ba ki furta ba sai kin ce ni mugu ne ba ni da adalci." Cikin Mamakin kalamansa Mimi ta ce"Ni? Me ya sa zan kira mijina da suna mugu? Ka isa ne shi ya sa ka hanani saboda kai in mijina ne kuma shugabana, yan'uwana kuma ba su da abun cewa tunda ba suke aure na ba, na su sai dai shawara ne ko jin ta baki" Aji ya ciji leben bakinsa na asa kafin yacce"Ina son na hanaki, amman kuma gwara na yi miki adalci kema ki yi min,in na dawo za mu sake yin mgana" Ta san cewa akwai mgana tunda ya ce sai ya dawo za su arisa mgana, tun kafin ma ya ce bai amince ba mganganunsa sun nuna in da ya dosa yasa ta fa a mana Manaja Megidanta bai amince ba sannan ta ba da Shawaran tun da a shekaran a auki sabbin ma'aikata me zai hana su jaraba wata sabuwar fuska! Nan da nan ko a ka kar i shawaranta a ka fara shirye shiryen kaddamar da shirn tare da za o cikin sabbin ma'aikatan da a ka auka domin cire wacce ta fi chanchanta a ciki. Ko da suka yi waya da Rukky ta yi mata zencen itama sai da ta ce"Ke ma Mimi da son jan ma kanki fa a kike yi, wannan mijin naki mai shigen kishi ne zai amince? Aikin ma ai ba ason ranshi kike yi ba, da kin sani tun da Manaja ya tuntu eki kin datse abun da ba ta kawo ku da gabar haka ba." Mimi ta ce"Haka ne Rukky, ai na ce su nemi wata sabuwar fuskar mijina bai amince ba." ayya tace shike nan kuwa sai ki zauna lafiya. Saboda maganar na ranshi sati biyu tsakani ya dawo gida, amman sai da ya zaunar da ita yana gaya mata ba dole sai an ri a ganin fuskarta ba akwai ma'aikata da dama da suke aiki ta bayan fage fa ba'a son su ba, me zai hana itama a maida ta wannan bangaren? Mimi ta ce"Ba ni da za in bangaren da zan yi aiki, za i na kenan bangaren da na fi warewa broadcating, Kuma ni ban isa in ce ga in da za su ijiyeni ba sai dai in zan ijiye aikin gaba aya na dawo gida na zauna tunda haka kake so." Jin haka yasa bai ara mgana ba tunda ya ga idanuwanta sun ciko, ya san tana son aikinta kuma yanzu ya ce ta bari kamar bai yi mata adalci ba, ita ba wata sana'a take yi ba sannan shi kuma ba mazaunin gari ba sannan In har Inna ta ji labari sai ya raina kanshi shiyasa ya danne ma zuciyarsa bai ara mgana kan aikinta ba har ya gama kwanakin shi ya koma Abuja. Ya koma ba Da ewa Mimi ta samu wayar Mommy ta ce tana neman ta a Abuja, a she ba ita ka ai ba gaba aya yayan nata har da Dr tunda shi ne babba, kiran ya ba su mamaki amman su a tunanun ko maganar gidane, kuma dukkansu ta i ce musu komai a waya ta dai ce su nemi izini wajen mazajensu weekend in da zai shiga tana son ganin su gaba aya, Aji ma da ta gaya masa sai da ya ce" Topha! Allah ya sa lafiya." Mimi ta ce"Ina tunanin ba lafiya, dukkan mu fa ta kira har Dr, ni ba ka ce min ka je wancan satin ba? Ko ka fahinci wani abu ne? Aji ya ce"A'a lafiya lau take ba wata matsala, mun da e muna hira da ita, ba na jin ko akwai wani abu na damuwa sai dai in wata mganar ce ta dabam, ki kwantar da hankali hairan in sha Allahu." Da haka ya samu ta natsu amman ita duk ta damu, Abun da ya ara ba ta mamaki da ta je gida gaida Hajiya nan ta ke gaya mata ta saka Daddy ya nema musu jirgi ga adayansu har da shi za su tafi Murja na neman su. Sai Mimi ta saka a ranta ila kan mganar gida ne tunda ba'a raba gidan ba har yansu su sun ce sun barshi Mommy ta zauna har karshen rayuwanrta ne. Daga gidan Hajiya gidan Inna ta biya ta na gaya mata za su tafi Abuja tare da Hajiya da Daddy, Inna ma kanta sai da ta ce"Lafiya kuwa? Ko wani abun ne ya faru? Mimi ta ce"Lafiya alau Inna za mu je dai mu gaishe ta ne." Haka ta fa a ma Inna, saboda itama ba ta san dalilin kiran ba. Nan ta kai har mangariba saboda Aji baya nan ya sa ta koma da wuri kuma a motar ta ta zo, washegari kafin ta je aiki sai da ta kai Ummi asibiti ta kwana kuka ashe kunnenta ke ciwo a ka bata mgani. Daga asibitin ne ta wuce wajen aiki amman ba ta da e ba ta koma gida saboda Ummi, amman Alhamdulillah mganin da a ka bata ta iga mata sau uku shike nan ta samu sau i ta cigaba da walwalanta irin na su na yara. Tun ranar Jumma'a Khadi da Madiha suna Abuja, su Mimi kuma jirgin safe suka bi, wajen sha aya suna falon gidansu a Abuja, abun da ya ara ninka mamakinsu ganin har da Inna zainaba suka iske a gidan kenan mganar babba ce, a yinin dai ba'a yi wata nagana ba an ha u ana ta hira kowa sai mamakin ki an Ummi yake yi khadi ta dauketa ta na nishi lokaci aya tana fa in"Ka ga min burtuka, ke ubanki an firit uwar taki kuma ba ki a ba, to ina kika auko wannan jikin? Hajiya na dariya ta ce" ibar yara ce, taba fara girma za ta ragu, sannan ita kanta Binta haka Murja ta yo goyonta sai da ta fara girma sannan ta fara raguwa." Mommy na wajen ta ce kwarai haka ta yo goyon Mimi da wannan kibar kamar kazar turawa jiki su u su u kamar Ummi, Dr ya ce to ga in da ta yi gado nan wajen uwarta ana ta dariya har Madiha ta na saka baki ta ce Yarinyar na burgeta ta na son ganin yaro da kibarsa sannan da arsashinsa har aukanta ta yi, Allah ya ha a jininta da na Ummi duk ba ta damu da aukan yara ba, nata ma a hannun masu aiki suka yi wayau Har dare Mommy ba ta ce musu komai ba, Sun dai ga sun shige ciki ita da Daddy da Hajiya sun jima suna mgana sannan ya fito, shi a ranar ya koma daman ba kwana ya ce zai yi ba. Hankalinsu ya kwanta ganin Mommy lafiyanta alau ta na ta zirga zirganta suna da tabbacin ba ita ce wani abu ya same ta ba. Har Asma'u sun ma mgana ta ce itama ba ta sani ba, sannan sun yi ma Inna Zainaba mgana ta kalli Khadi da ita ce ta tsarete da tambayan abunda ya sa Mommy tace ta na son ganinsu." Inna Zainaba ta ce"Ban sani ba,ko jira ita uwar taku ai tunda ta kira ku za ku ji abin da ke faruwa." Sai suka yi shuru ba su kara mgana ba ko Dr da yake namiji bai damu ba. Harkan gabansa kawai yake yi sai su ne duk suka damu barin ma Khadi da Madiha. Madiha ba ta hakura bq sai da ta je har akin Mommy a daran ta ga ta na waya amman ta na ganinta sai ta ce"Zan kira, yanzu zan yi mgana da yaran nawa." Daga nan ta juya tana kallon Madiha cikin Mirmishi kafin ta ce" Madiha Kabir Dabo,." Haka ta kira sunanta sai itama ta yi mirmishi kafin ta ce" Barrister me ke faruwa ne? Kin kiramu kuma kin i ce mana komai? Kin san gobe zan koma ga Dr ma ya na da Tiyata jibi ya ce." Sai Mommy ta dafa kafa anta kafin ta ce"Ina sane da abin da nake yi, mu je akin da Hajiya ta sauka sai mu yi mganar gaba aya. Tare suka fito da Mommyn da Madiha Dr ya na akin da yake sauka Mommy ta kira shi a waya ta ce ya shigo cikin gida. Mimi kuma tana akinta suna waya da Aji, yana gaya mata gobe zai zo su ha u daman ya yi kewarta sosai, itama Khadi ta zo ta kira ta Ummi dqman tana goyo bayan Inna Zainaba ta na barci bayan mangariba ta fara rigima ana yi mata mata wanka sai ga shi ta yi barci bayan ta goyata. Gaba ayansu sun ha u a akin da Hajiya ta sauka amman kafin nan inna Zainaba ta fa i wata mgana da ya jefa su a duhu domin kallon Mommy ta yi kafin ta ce" Murja kina ba ni mamaki sai wani tare tare kike da yara? Ba fa sa on Allah za ki yi ba sannan ke ce wwarsu ba su ba, ballantana ki ce yardan su kike nema ai ya kamata daman tuntuni ki yi ma kanki fa a tunda zaman haka gare ki da sauran kuruciyarki ba zai miki kyau ba." Ga shi dai ba ta fa a kai tsaye ba amman dukkansu sun sha jinin jikinsu, ai ba su ara firgita ba sai da Mommy ta warware musu mgana ce ta aurenta ya ta so, wani Alkali a ya ganta ya na so tun
Chapter 201 · 0% Book details