Sashe 58
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan suna biki a gidanu, ta yi murna da ta gansu sai ga shi ta kawo musu ruwa da zo o daman ta na saida wa. Ta zauna kusa da Yaya Amina tana fa in"ki ce yau a gida kika yini" Yaya Amina na shan ruwa ba ta amsa ta ba, sai Walida ne ta ce"E, ke ai kin gudu jiya." Bintu ta ce"Uhm na yi gudun gara ne Walida yau da safe Baban inna ya kirani a waya ya zazzageni Walida." Walida ta zaro ido Yaya Amina ka an ta ware da ruwa ta ago tana fa in"Kai! me ya ce miki kuma? Bintu ta yi tagumi kafin ta ce"Kawai da safe muna cikin karyawa da Bashir sai ga kiransa ni fa tunda na ga kiran Baban Inna nasan ba na alheri ba ne na tashi na yi ciki ina aukan waya ko gaisuwata bai amsa ba ya fara min masifa wai mu munafukai ne ni da Walida me ya sa da Inna ta ce ga inda za mu rakata ba mu kirasa a waya a oye mun fa a masa ba? da ina masa rantsuwan ni ma ban san inda za mu je ba ya dakamin tsawa yana fa in duk sai yaci ubanmu me ya sa da ta ce mu rakata ba mu ce ba za mu je ba? Kuma sannan mun yi masa arya da ya kira mu ka i gaya masa in da mu ka je, yace wlh wannan aryan da munafuncin da mu ka yi masa sai mun raina kanmu." Walida ta yi fiki fiki da ido ta kasa mgana Yaya Amina ta ce"To ke ba ki ba sa hakuri ba ne?. Bintu ta ce" Wani hakurin? Ya tsaya ne ma ina cikin mgana ya yi tsaki ya kashe wayarsa walh Baban Inna ya cika masifa" Yaya Amina ta ce"To ai jiya ma yazo zai yi ma Inna ta balbaleshi da masifa shi ne ya koma gida ya kira Mu'azzam ya sauke a kan shi." Bintu ta ce"Kai jqma'a shi ya yi hakuri da rayuwa mana, ni fa ban ga wani abu acikin zuwa gaisuwan da muka yi ba" Walida ta ce"To ni ma dai shi nagani." Yaya Amina ta ce"To shi gani zai yi ba kwa kishinsa ban da abunsa da mai rai ake fushi ba da wanda ya mutu ba." Nan su ka cigaba da tattaunawa Walida ta shantake ba ta je islamiyan ba Bintu na ba ma Amina labarin yadda Hajiya da Mimi da su ka yi ta rawan jiki da su ka gan su. Yaya Amina ta ce"Allah Sarki Itama kila har yanzu ta na son shi." Bintu tace"To daman mana, shi ma duk wannan kumfar bakin na Soyayar ne." Gaba aya suka saka dariya ba su suka baro gidan ba sai shidda saura na yamma. Suna komawa gida Inna ta ga Walida ta dawo da wuri cikin fa a ta ce" Amman dai ba ki je makarantan ba ko? Walida ta sosa kai ba ta yi magana ba Inna tace "Ya yi miki kyau." Yaya Amina ke labartama Inna yadda Baban Inna su ka yi da Bintu sai da Inna ta yi dariya amman ba ta ce komai ba acikin ranta tana son ganin yadda lamarin zai kasance. Shi dai kahaifin Mimi da ya fara ja Ubangiji ya kar i kayanshi sauran Baban Inna shi kuma sai ta tsaya ta ga ina wannan bakar zuciyar za ta kaisa. Kamar Inna ta sani yaji ya yi musu sai da ya kusan kwana goma sannan ya zo gidan Sun dai ji kabarin ya na kaduna sun je buga wasa daga bakin Mu'azzam shi tuni har sun shirya kansu. Sai da ya dawo ya zo gidan shima bai da e ba, Walida daman tana nemansa nan ta gaya masa an fara biyan Jamb ta na so ta biya nan ta ke ya ba ta ku in har da na abun hawa ya ce kuma in akwai wata matsalar ta kirashi ta wayar Inna ta gaya masa. Duk kuma wannan abun bai zauna ba ya na tsaye a kofar akin Inna Meri. Ita ko ta yi masa banza kamar ba ta gansa ba, har ya tafi kuma sai ya dawo ya kira Walida yana tambayanta ina Mariya? Ita ba za ta yi jamb in ba ne? Domin suna aji daya ne SS3 Kuma tare aka biya musu ku in jarabawar fita. Sai take fa a masa Mariya ta da e ba ta nan ta na gidan Yaya Zuwaira, Inna ya kalla kafin yavce"Inna me ta je yi can kuma? Inna na tanka en garin tuwo ta juyar da kai kafin Ta ce"Ina zan sani, shiga akin Magajiya sai ta fa a maka" Cikin Kallonta ya ce" Innarmu." Ko kara kallonsa ba ta yi ba sai kawai ya ka a kai ya fice bai kara magana ba ta bishi da kallon tausayi a ranta ta na masa fatan Allah ya yaye masa wannan bakar zuciyar. Da daddare Mu'azzam ya kira wayarta yana fa a mata Babanta ya kawo masa aranta. Tana mirmishi ta ce"Me kuma na yi an Inna? Ckin dariyan shima ya ce" Ya ce ya zo kin yi kamar baki gan shi ba ,yana mgana kika yi banza da shi sannan ko abinci bavki ba shi ba." Inna Meri ta ce"Ban ba shi ba sai ya zo ya wata, ko auransa na ke yi da zai zo ya tsaya a saman kaina yana min wani cin magani? an Inna rabani da Baban Inna ba na iyawa da fitinarsa." Cikin magiya ya ce"Haba Innarmu maganin kukan mu, a yi masa afuwa in kina fushi da shi ina zai saka kansa Inna? Ya fa a cikin wani yanayi sai ta ji tausayin duka ya'yan nata ya kamata amman ba ta huce ba cikin gatse ta ce"To shi ba shi da bakin da zai zo ya ce in yi hakurin ne? Mu'azzam sai da ya yi dariya kafin ya ce"Allah ya huci zuciyarki Inna" Ta amsa mai da Amin bayan sun yi sallama ba jimawa Baba anjuma ya shigo. Shima sai da ya yi mata mganar cikin Lallashi ya ce"Meri fushi da Baban Inna ba naki ba ne a wannan lokacin, ki yi hakuri ki fahimce sa don Allah." Inna ta gyara zama kafin ta ce"Au kai ma aran nawa ya kawo maka? Kai tsaye ya ce"Ko aya ni na fahimci yau ya na cikin bacin rai ya shigo gida ya fito ban gansa cikin yanayi mai da i ba, ki yi hakuri tunda har mu fahimcesa sai mu yi ma rayuwarsa uzuri kin ji ko? Ba za ta iya yi ma mallam gaddama ba sai ta amsa masa. Shi ya sa bayan kwana biyu da ya zo Innar ta sakar masa amman ba sosai ba da kanta ta kawo masa abinci ya zauna yaci sosai tausayinshi ya kama inna har sai da ta ji taruwan kwalla acikin kwarmin Idanuwanta. Bai yi wani doguwar mgana ba da zai ta fi ya ijiye mata ku i yana fa in "ki yi hakuri Inna." Daga haka bai kara cewa komai ba sai ta auki ku in tana saka albarka kafin ta ce"Ka leka ka duba Magajiya ba ta ji da i ba kwana biyu." Sai ya amsa mata da to, yana fita sai ya ganta nan kofar akinta kamar ta fito daga makewayi ne. Mariya na cikin aki ta dawo shekaranjiya ta na jin muryansa yana fa in" Magajiya ya jiki? Dakyar ta amsa shi kuma cikin yanayinsa ya ce"Allah ya kara lafiya" Bai ji ta amsa ba Mariya ce ta leko tana gaishe shi ya amsa yana kallonta har ya wuce sai ya sake dawowa yan fa in"Ke me ya sa kika tafi wani waje kika bar zuwa makaranta? Kafin ta yi mgana Magajiya ta yi zaraf ta ce"Ba wani waje ta je ba gidan ar'uwanta ne ko za ka hana ta ne? Ko bangaran magajiya bai kalla ba ya cigaba da fa in "Walida ta biya Jamb ke me ya sa ba za ki yi ba? Da sauri ta ce"Ina son na yi Yayanmu Baba ne ya ce ba shi da ku i Yaya Auwalu ma na yi masa mgana ya ce ba shi da kudi." Hararanta ya yi kafin ya ce"Daman su suka saba awaniyar makarantar ki? biyo ni ki karbi sa o a waje." Ya wuce cikin takunsa na gif gif Magajiya sai ta kasa mgana saboda ya lna mata warjini wani lokaci. Jiki na rawa mariya ta zari hijabin Magajiya da ke saman kofa ta bi bayanshi da mota ya zo sai da ya shiga ciki ya auko ku i ya bata na farko ya ce ta biya Jamb ta yi ma Walida magana ta rakata. Ta kar a da sauri tana godiya sai ya mika mata wani ku in yana fa in"Ki kaiwa Magajiya." Har sai da ta ramkwafa wajen amsa masa acikin zuciyarta ta na jin wani iri, gida ya ce ta shiga sai ta shige ta la e sai da ta ga shigarsa mota da tafiyarsa sannan ta koma tana dafe kirji ita fa tun ba ta gane ba har ta zo ta gane cewa tun tuni ashe son Yaya Mansoor take yi ba ta sani ba. Jiki na rawa ta je ta na nuna ma Magajiya ku in ta ba ta nata tana fa in "Ya ce in ba ki" Magajiya ta ta e baki ba ta ko kar i ku in ba ta shige cikin akinta lokaci aya tana fa in" Shi ne kike ta wani rawan jiki kamar ya ba ki wata duniya" Kuma acikin ranta ta ji da i bashi ake bin ta ko ta samu ta biya daman in ba shi ko Mu'azzamu ba ina take samun ku i? Sai dai fa ta i godema Allah. *Shafukan kyauta sun gabda arewa. Ku yi hanzarin biyan ku in karatun ku domin kar mu ata lokaci da zaran mun gama book1, mu ora da book 2and3 in sha Allahu* *BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KU IN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WA ANNAN LAMBOBIN.* *09069067488* *80032773332* an kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu