Sashe 155
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gefen ido amman bai nuna ba, wata Jarida ma ya ja anan gefe yana karantawa kamar yadda Daddy ya yi masa kwarjini haka shima Daddy ya ga warjinin Mansoor ya cika falon gaba aya. "Ka sha ruwan mana." Daddy ya katse shi lokaci aya yana kallon sa, sai Mansoor ya muskuta ya an mike ya isa ga wajen ruwa ya saka kofi ya tsiyaya Ka an ya sha sannan ya ijiye kofin sannan ya koma in da ya tashi ya zauna. Shuru ya sake wanzuwa na wani lokaci kafin Daddy ya sake katse shurun da cewa" Ya wajen aikin na ku? Kwanaki abokanka da aninka suka zo sun ce wasa gare ku masu yawa baka samun lokaci." Sai ya samu kansa da amsawa da E, shi kuma Daddy sai ya jinjina kai kafin yac e"Good! Allah ya saka albarka," Aji ya amsa da Amin cikin yanayin maganarsa amman muryansa ta yi kasa sosai. Gani ya yi Daddy ya yi kamar bai san dalilin zuwanshi ba, ya ma cigaba da karatun Jaridarsa lokaci aya kuma ya na amsa waya in an kira shi. Mansoor kuma na duke ya rasa ta in da zai fara dakyar ya iya kundunbalan agowa ya na kallon Daddy kafin lokaci aya ya fara da fa "Alhaji dama kan mganar Fatima ne.." Sai ya dakata shi kuma Daddy sai ya kalle shi kafin ya ce"E, ina jin ka, Mimi ba ai ta dawo mana nan cikin kuka, ta ce ka ce ba ka sonta sannan ta ce za ta tafi ka ce is better da ta tafi in, ni kuma da na ji haka sai na ce ai ba dole a cikin aure kuma in ka ga alaqa ta fara lalacewa gwara rabuwar shi ya fi alheri." Mansoor ya yi shuru kafin yac e" Alhaji ni ban ce ta tafin da gaske ba" "To me ya sa bayan ta taho a daran ko washegari ba ka biyo sahun ta ba, in ba ka nufin ta tafin ba? Kai tsaye Mansoor ya gyara zama yana fa in" Ina da dalilina Alhaji, saboda ka san su mata wani lokacin in ransu ya aci gwara ka yi nesa da su su huce, na ga ranta ya aci a lokaci to ba laifi ba ne domin ta dawo gida ta huta amman ba na nufin wai ta tafi saboda ba na sonta, in ba na sonta ai ba zan yarda na aureta ba. Kawai na bata lokaci ne ta huta sannan ta huce daga acin ran da take ciki." Magana aya bayan aya haka Manaoor ke fitar da ita, Daddy yana kallonsa amman yana mirmishi kafin ya gya a kai ya ce"Na ji dalilin ka, ta wani fannin kana da ar gaskiyar ka ta wani fannin kuma ba ka da shi, amman duk ba wannan ba babban abin shi ne ga rashin ba ka sonta sannan ta ce ka kasa manta abin da ya faru a shekarun baya sai ka ri a kallonta da abin, ka ga kuwa ai ba kyau irin haka ri o ba shi da amfani sannan tunda har da bakin ka ka ce ba ka so ai ba wanda zai yi maka dole da sai ka zauna da ita ko ba haka ba? Kan Mansoor Aji na asa ya ce"E, ta nan kam ina da laifi, amman na gane kuskurena Alhaji a yi hakuri in sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba." "Maganar rashin son fa? Ba zan ba ka bikon ata ba sai na ji gaskiyar mgana.* Ya fa a ya na an ha e rai. Sai Mansoor ya sadda kansa asa cikin jin nauyi kafin ya ce"Ita ce ko a da, a yanzun ma ita ce har gobe da jibi ma ita ce, acin rai ne ya sa na yi mata mganganu cikin fushi amman in sha Allahu hakan ba za ta ara faruwa ba." Sai Daddy ya saki fuska yana fa in" Alhamdulillah Allah ya sa na ji da in haka, ka burgeni yadda ka amshi laifukan ka sannan ka ce za ka gyara sannan na amince zan baka damar yin bikon matarka saboda dalilai guda biyu na farko ka yi laifi kuma ka amsa laifin ka, ka ba da hakuri sannan ka yi niyar gyara na biyu kuma na ji labarin ka je Abuja da kano ba ka samu ganinta ba hakam ma ya saka ni yarda da mganarka ta farko. Tabbas da farko da ta dawo gida da Koke koken cewa ita a raba auran ku in da ban yi zurfin tunani da duka rayuka sun aci amman sai na bata lokaci kamar yadda ka ce itama ta sauka daga fushinta na tabbata a yanzu ba za ta so rabuwar auran ku ba sai dai daman an tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Sannan ina son na yi maka nasiha shi ri o ba shi da amfani mu kasance ma su afuwa tunda Allah ma muma yi masa laifi, yana yafe mana kuma shi ya ce mu kasance masu afuwa, sannan shi kan shi Yaya Kabiru kafin rasuwarsa wallahi ya yi nadama kan abin da ya aikata maka kuma Hajiya da Brr. sun je sun yi mgana da kai sun kuma nema masa afuwarka sannan kafin rasuwarsa shi ya ce duk abin da Mimi take so a yi mata dalilin da ya saka aka yi auran ku bisa duk Shara un da ka saka ka ga ba wanda ma ya maida kansa, To me ya sa kai ba za ka yi hakuri ka manta baya ba? Sai ka bar abu na shekaru ya hana ka sukuni da zaman lafiya? Shi kan shi Yayan ina yake yau ? Ai ba shi a duniya ya ma manta shi ya ta a rayuwar duniya, ni ma ila ban sani ba nan kusa ne, wata ila kaima nan kusa ne duk ba mu san gawan fari ba, sai fatan Allah yasa mu dace sannan ka sani Allah ya yi ma masu Afuwa wani babban tanadi, Ina ba ka shawaran ka manta baya don Allah domin samar ma kan ka da zuciyarka salama." Gaba aya jikin Mansoor ya yi sanyi mganganun sun shiga zuciyarsa sosai daman kuma shi tuni ya saki wannan abun Sai ya ji kamar ana rage masa nauyin zuciya cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu komai ya wuce. na gode Alhaji Allah ya ara girma." Sai Daddy ya ji da i har ya nuna a saman fuskarsa ya kalli Aji Lokaci aya yana fa in" Na ji da in yadda ka saurare ni, da duka amincewata Mimi za ta koma akinta, zan kirata da kaina na ce ta dawo amman sai ka same ta ku tattauna wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga ba." Aji ya rankwafar da kai yana godiya Daddy yace"Ba laifi. Na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwa albarka Allah kuma ya ka e fitina a tsakanin ku." Aji ya amsa da Amin Amin kafin ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya zaro ku i bai san ko nawa ba ne ya ijiye a gaban Daddy sannan ya mi e yana yi masa sallama Daddy duk da yana da rufin asirin sa amman ya girmama wannan alherin ya mi e Lokaci aya y na aukan ku in kafin ya ce"Har da awainiya? To yau dai zan ce na ci ku wallo kenan." Mirmishi kawai mansoor ya yi ba tare da ya yi mgana ba Har haraban gidan Daddy ya rako shi, suka kara yin sallama shi ya koma cikin gidan shi kuma sai ya hau mashin insa ya bar gidan, yana tafe iska na ka a shi yana jinsa kamar ya na shawagi a sararin samaniya, sannan nauyin da ke zuciyarsa ya ji ya yaye, wani irin nisha i da farinciki ke shigar sa bai sani ba, Yana tafe yana Faman mirmishi shi ka Daddy kuma yana komawa cikin gida Mama daman na falo tana jiran shi ya na shigowa ta mi e tana fa in" Har ya tafi? Shi kuma bai ba ma tambayarta wani muhimmamci ba ya ce" E." Ya fa a lokaci aya ya na zama kan aya daga cikin kujerun falon gefensa ta koma ta zauna tana fa in" Allah sa dai ba ka ba shi fuska ba" Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce" wani fuskan kuma ? Na saurari bayaninsa na nuna masa Kuskuransa kuma ya kar a ya ce zai gyara na kuma bashi izinin in Mimi ta dawo ya je su zauna su daidai ta." Mama ta yi wani iri wanda har sai da rashin jin da in ya bayyana saman fuskarta. Cikin mamakinta Alhaji Hamza ya kalleta kafin ya ce"Sai na ga kamar ba ki ji da in jin hakan ba ko? Da sauri ta ce"Ba wai ban ji da i ba gani na yi yarinyar nan ita ta ce ta na so daga farko amman yanzu kuma ta ce ba ta so, kana ganin a tsaya sauraran shi ba ata lokaci ba ne? Sannan sam ba su dace da juna ba ji irin gidan da ya kai Mimi domin Allah fa." Mirmishi ya yi domin shi ya gama gano in da ta dosa amman gudun ka ora ma mutun zargi ya sa yac e" To ba ki san tsakanin mata da miji sai Allah ba kenan? Itama a lokacin acin rai ne amman tana son mijinta kuma ba za ta so rabuwarsu ba, mganar gida kuma ai ta san ra'ayin sa tun farko kuma ta ce ta ji ta gani, ba hurumun ba ne yanzu mu san abin da suka yanke ni dai na ce ya same ta su yi mgana abin d suka tattauna namu na saka albarka ne." "Amman ba dai wanman gidan na su za ta koma ba ko? Mama ta fa a cikin yanayin damuwa a muryanta kai tsaye ya ce"Ban sani ba,ko ma can ne ko wani gidan ne can tsakanin su dai." Sai Mama ta sauke ajiyar zuciya ba tare da ta yi mgana ba sai Daddy ne ya kalleta na wani ookaci kafin ya ce"Na san damuwarki kan Jaheed ne." Da Sauri ta juya gare shi tana fa in"Yallabai Yaron mu na son Mimi har yau ya kasa ba ma wata mace dama, bayan dawowan nan nata