Sashe 15
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace zata auki nauyi." Mimi ta gya a kafin ta ce"Good! Allah ya nuna mana ookacin da rai da lafiya." Rukky ta jima har sai da aka kira wayarta sannan ta bar wajen Itama Mimi bata jima ba ta kwashi tarkacenta ta shiga office in manajansu ta kai masa takardun hannunta suka yi mganar da za su yi ta ce mai ita ta tashi sai gobe da yammah tunda sai karfe bakwai din gobe take da karanta labarai amman zata shigo zuwa la'asar. Daga nan ta fito ta yi sallama da sauran ma'aikantan bangaren su. Ta fita zuwa babban falon da ke ma'aikan ana mata mgana ta na amsawa da sakin fuska. Na Misau ta hanga yana ta hira da wani an siyasa acikin shirin Nageria a siyan ce. Daga masa hannu ta yi ta cikin gilashin da ya raba wajen shi kuma sai ya jinjina mata kai. Ko bangaren su Rukky ba ta biya ta fita zuwa haraban wajen ta kunna motarta bayan ta ijiye jakarta a kujeran mai zaman banza ta zagaya ta shiga bangaren direba ta zauna da bismillah a bakinta. Sannan ta yi ma motar key ta juya ta fice daga gidan talabijin in megadi na fa in a sauka lafiya Hajiya." Itama sai ta aga masa hannu cikin fara'an da ke saman fuskarta. Bata da chanji ne acikin jakarta sai dai gobe in ta dawo. Mimi mai kyauta ce abun hannunta baya rufe mata ido in tana da shi ta ba ka in bata da shi ta ba ka hakuri. Gida ta koma ta iske Hajiya ta yi barci sai Baaba Uwani ka ai a gida tana ta zirga zirga sannu da gida ta yi mata sannan itama ta shige cikin akinta. Kaya ta sauya zuwa masu sauki na gida sannan ta haye gado ta kwanta ta na motsa jikinta domin tana jin jikinta duk gajiya ya saukar mata. Har ta kwanta sai kuma ta mike ta isa kan Dressing mirror in da ke akin ta bu e jakarta ookaci aya ta ciro wayarta ta koma ta kwanta. Faceebook ta shiga ta sauya Account in ta na Asali na Fatima Kabir sulaimam Dabo(Mimi).Zuwa wanda ta bu e na sirri da suna MIAJ Kuma account bai da suna ko wani bayanan da za'a iya gane ko wani jinsi ne. Da oyayyen account take bibiyan Aji kuma da shi ne ta tura masa friend request tun shekaru hu u da suka gabata kuma ya kar eta sannan tana following in GOMBE UNITED nan t ke ganin wasu abubuwan Tun da shi ba chart yake yi ba, ta sha masa sallama bai ta a bu ewa ba ballantana ya amsa ta ba, sai dai ta na bibiyan shi ta hanyar club in sa. A nan ne ma ta samu hoton sa da ta kai aka yi ma babban elegerment, anan take ganin in suna da wasa da garin da suka je anan kuma take ganin irin cigaban da ya samu bayan rabuwar su. Ba za ta ta a manta lokacin tana Kano tana Master inta ba , ta ta a ha uwa da aya daga cikin abokansa mai suna Nasir. A bakin shi ta fara jin Aji yanzu wallo yake yi, ta da e ta na mamaki sai da ta gani sannan ta tabbatar. Shiga ta rika yi hotunan da Club ke orawa yawanci na yan wasan su ne, har akwai hoton da aka auka da Aji tare da Coach in su ookacin da ya yi singing contract da su. A nan take samun ganin rabin ranta ta kuma kalle shi son ranta, komai nashi na nan a yadda ta san shi sai dai yanzu ya rage fara'a sannan fuskar nan a kimtse kamar wanda ke cikin bacin rai, ya kara dai girma tunda shekaru sun ja, wani hoto da ya yi mata kyau sai da ta auke shi. A Studion ne aka auki hoton yana sanye a blue din kayan kwallo a jikinsa ya duka kamar zai taso daga sujjuda zufa duk ya cika fuskarsa a wannan hoton ta ga dariyan shi. Har ga fararen hakoransa nan sun bayyana. Kamar kuma a wani gari ne da suka je kwallo, sai da ta duba rubutun asan Hoton ta ga an saka. Kaduna da date din sannan an Rubuta Captain Aji baka dariya sai ka kada masu gida. Itama sai da ta murmmusa a sanin da ta masa a baya yana dariya. Sai dai ta san masifaffe ne, abu ka aan sai ya harzu a sa ya fara masifa. Ga zuciya da kafiya in ya kafe akan abu baya sauya ra'ayi. Tana kai hoton da ta auka wajen da take adana hotunan sirinta ta furta a fili" Ko yanzu ya daina fa a? Ko wasu hallayansa ne suka sauya bayan mun rabu? Sai ta kasa ba ma kanta wannan amsar, sai kawai ta kashe data, ta sauka daga kan Account din ta kashe wayarta ta sauke a gefenta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi. Ya jima ta na ta tunane tunane kafin barci ya kwasheta. Ba ta tashi ba sai da Hajiya ta shigo tana buga mata kafa da cewa an yi azahar. Sannan ta iya tashi a kasalance ta shiga tiolet tayi alwala ta zo ta yi sallah sannan ta fita fallo ta iske Baaba Uwani da Hajiya suna hira. Kirchen ta nufa tana fa in "Baaba me kika girka mana yau? Baaba Uwani ta ce"Alala Hajiya ta ce tana jin ci yau, shi na yi." Mimi ta daka yar tsalle kafin ta ce"Kai Hajiyata Allah ya saka ki a gidan Aljannah, kamar kin shiga raina daman na ce sai weekend na zauna nayi Alala na kwana biyu ban ci ba." Ta fa a tana shiga kitchen in cikin farinciki. Hajiya na mirmishi ta ce"Daman nasan kina so, rashin samun zama ya sa ba ki yi mana mun ci ba, da Uwani take tambayata abin da za a dafa na ce ta yi mana Alala kawai." Ta na jin maganar Hajiya daga cikin madafin , miyanta har tsinkewa yake yi sanda ta ga alalan gwangwani da manja. filet ta samu ta zubo guda hu u ta saka yaji ka an mai da i da Yaddiko da aiko ma da Hajiya ta kuma tsiyayi soyayyan manja a gefe. Ko da ta fito falo mirmishi kawai take yi cikinta na wani yamutsawa. Gefe ta samu ta zauna kan cafet ta yi bismillah ta fara ci loma daya biyu ta ago tana kallon Hajiya dake kallonta kafin ta ce"Hajiya ke ba za ki ci ba ne? Hajiya na yar dariya ta ce"Sai ya sha iska zan ci kar na ci da zafi ya lalatamin ciki." Mimi ta ce"Hmm hajiya da zafi ya fi da Baaba Uwani ta saka dariya tana fa in" Binta ko na saka waigi ne? Mimi ta jinjina kai kafin ta ce"Baaba na manta kafin ki saka waigin ha omin da ruwa wayyo da i Hajiya." Ta ke fa a tana cin alalanta tana santi Hajiya da Baaba Uwani na yi mata dariya. Baaba Uwani ta tashi ta auko mata ruwa mai sanyi da kofi ta kawo mata. Mimi na ta buga santi suna ta mata dariya tas ta Cinye ta sha ruwa kafin ta ce"Baaba Uwani Allah ya yi albarka ya sa a gama da duniya lafiya." Baaba Uwani na dariya ta ce"Amin Binta." ta mike auke da filet in hannunta tana fa in"Baaba Uwani cikin Albashina na wannan watan kina da dubu goma cash tukwaicin Bintan Hajiya ne." Baaba Uwani ta aga hanci ta ranga a gu a kafin ta ce"Ina godiya uwar akina Allah ya saka da alheri Allah ya tsare gaban ki da bayan ki Allah ya rabaki da sharrin makiya da mahassada, Allah kuma ya bama babanki lafiya." Mimi na gabda shiga madafi ta ce"Amin Amin Baaba Uwani da kika yi min addu'an Allah ya ba ma Abi lafiya kamar na ce na ara miki wata duban goman"" Ta fa a ta na yar dariya Baaba Uwani ta kara karkacewa ta yanka wata gu aa kafin ta ce"Gaba salamun baya salamun yar lelen Hajiya da ba kamarta Allah ya kara arziki da wadata Na gode kwarai" Hajiya na gefe da cashaba a hannunta tana ja cikin mirmishi ta ce"Da kin kara da addu'an Allah ya kawo ranar auran Binta da wuri wuri da na cike miki kudin sun zama dubu hamsim"Baaba Uwani na jin haka ta yi zaman dirshan gaban Hajiya tana fa in"Allahu Akbar Uwar marayu, kin goya na gida kin goya bare, ai ban gama addu'an ba, tana tafe Allah ya nuna mana auran Binta Allah ya bata miji nagari kyakyawan kamarta mai kyan hali da mutumci kamar ita.." Hajiya na dariya ta ce"duk da kin makara na dai ara miki dubu goma." Baaba Uwani ta aaga hannu alamun jinjina kafin ta ce"Allah ya kara nisan kwana Hajiya, Allah yasa ki dade a duniya kina goya marayu irin mu." Hajiya ta ce"Uwani ai duk sona da duniya sai na mutu na barta ballantana ai bazan iya rama shekaruna na baya a duniya ba, ke dai Allah yasa mu cika da kyau da Imani." Uwani ta amsa mata da Amin Mimi ta fito ta na ta a cikinta lokaci daya tana fa " Hajiya mu bar tafiyar mu gidan Daddy sai anjuma lokacin cikina ya sassa Hajiya ta ka a kai kafin ta ce"Daman ai sai rana ta yi sanyi." Baaba uwani na gefe ta ce"Hajiya nima ina son zuwa na duba mai jikin." Hajiya ta ce"Ba matsala duk sai mu tafi tare. tashi ki zubomin alala ya kara wucewa kafin na gama lazimi." Baaba Uwani ta mike ta na fa in "Angama Uwar marayu." Mimi kuma dakin Hajiya ta shige ta je ta kunna talabijin. Tunda bayan falo akwai wani talabijin in a akin Hajiya. Mbc Bollywood ta saka sai ta ga a wani Film in da ta ke matukar so mai suna HIKCHI FiLM in Rani murkarji ne. Cikin jin da ta gyara zama ta cigaba da kallo. Ba su samu tafiya gidan Daddy ba sai bayan la'asar, gidansa na anguwan Abubakar Habu Hashidu Estate ne, Hajiya na gidan gaba Mimi na driving Baaba uwani na gidan Baya. Sanda suka je gidan sun iske Jaheed ya zo garin tunda