← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 208

Sashe 91

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata aya Manaja ya baki? Sai Mimi ta yi dariyan basarwa kafin ta ce" Ko aya, hutun Sati biyu ne na cinye Sati aya tun ina gida in sha Allahu Monday mai zuwa zan dawo aiki." Sai Lauratu ta ce" Ai ko ya kamata domin gidan ya yi kewarka, sannan Mutanenki su ganki ko za mu daina amsa tambayoyin su na Mimi ta daina aiki da ku ne? Gaba ayansu suka saka yar dariya, Mimi ta gyara zama tana fa in" Haba ina nan dawowa in sha Allahu." Aisha Farida ta yi karaf ta ce" To mu ka sani ko Ango ya hana ki aikin ne gaba aya." Mimi ba ta yi mgana ba sanin halin Farida ai awar Rukky ce, ko da bikinta da ta zo fa sai da ta isheta da mganar aikin nan kuma ta sanar da ita za ta cigaba da aikinta ba matsala amman ba ta yarda ba sai faman dawo da mgana baya take yi sai ta yi mata banza sai ta koma ta sauya harshe suna mgana da Debora. Rukky kuma sai faman mata bincike take yi acikin aki Mimi ta kalleta cikin ata rai kafin ta ce"Rukky wai kin bani Ajiya ne hala? Rukky ta ce" Eh mana ina tsaraban Angon ki? Kazan amarci na zo ci fa" Karamin tsaki Mimi ta ja kafin ta ce" sai ki yi ta nema ai." Rukky ba ta damu ba, ta cigaba da dubawa kamar ko ta sani ta na bu e fridge ta ga leda ta na dubawa sai ta ga kaza dangwalaye kaza kosassu manya manya har guda biyu ko ta asu ba'a yi ba Rukky ta saka Ihu tana fa in" Allah ya kama ki." Mimi na jinta ta yi mata shuru fito da ledan ta yi ta zo ta na nuna ma su Farida tana fa in" Muguwar ko cin kazan ma ba ta yi ba." Sai su ka fara dariya Lauratu har ta na fa in" ila dai ta ci ne, sauran ne ta rage mana" Ita dai ta na gefe kanzil ba ta ce musu Kazan ta ankanre da sanyi, kuma ga shi ba Wuta ballatana su yi warmimg in ta, gas kuma ba'a ha a ba duk yau Mommy ta ce za'a zo a ha a mata ganin suna so yasa ta le a ta kira walida ta ce su ba ta ta umama musu, aiko ita ta zafafa ta, tana kawowa su ka Rufu kanta su ka ci su ka yi nak ka an suka rage Mimi ta kalli Rukky kafin ta ce" Wa ku ka bar ma sauran? Wlh ku nanna e ta a leda ku tafi da kayan ku." Rukky na dariya tace" Ta kwana gidan sau i Hajiyata" Nan take kuwa ta juyo sauan a ledan, Mimi tace ta zuba ma kowa kayan fulawa, a leda su tafi da shi gida itama ta iban ma kanta da Mama, Rukky ta ce har da Bibi ma za ta iban ma wa, Mimi ta kalleta kafin ta ce" ki na son damuwa, ai ta san gidan ta zo ta amsa mana ai ya na nan, ni ba ci na ke yi ba kin sani." Sai Rukky ta ce shike nan, bayan an basu suna ta godiya saboda sai da Rukky ta cika ma kowacce leda, Lauratu ta ce" kada ku manta da Na misau ya ce wlh ya na jiran cincin in Amarya." Ba tare da damuwa ba Mimi ta ce duka ma'aikatanmu Rukky ta zuba musu ta aika ma wanda ya kamata, shiyasa su ka ata lokaci har Manaja sai da ta ce a iba ma wa da su peter tare da yan Inten insu. Leda ta zo ta are sai ta ce kawai Rukky ta iba a botiki ta je da shi gida ta kasa yadda kowa zai samu. Shi ya sa har sai da su ka yi sallar La'asar sannan su ka yi shirin Tafiya, Mimi ta saka mayafi za ta raka su sai ta ce su shiga akin Inna Meri su gaisheta kuma ta ji da i kwarai lokacin ma Bintu ta zo gidan, nan suka gaggaisa Mimi na zaune hannun kujeran da Bintu ke zaune ta ce" Inna abokan aikina ne dukkan su." Inna ta gya a kai kafin ta ce" Allah Sarki, sannan ku Allah ya saka da alheri mun gode, Allah ya bar zumunci, bangaren aikin ku kuma Allah ya baku sa'a." Su ka amsa da Amin ba su jima ba suka yi musu sallama suka fita Mimi ta fita rakasu amman iyakarta shashen magajiya ba ta fita har kofar gida ba. Magajiyar kuma na tsakar gida tana jajjage amman da su ka gaisheta yadda ta amsa ne da su ka yo gaba sai da Rukky ta yi ma Mimi ra a" Wannan matar fa? Ita kuma wace ce? Mimi ta ce" Abokiyar zaman Inna ce." Sai Rukky ta ta e baki kafin ta ce" To shine kamar tana jin haushin mu." Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce" Rukayya ni ban da e da zuwa gidan nan ba, ban ma san ko akwai mai jin haushi ko babu ba, harkokin gabana kawai na ke yi, iyakata bangaren Inna ban san abunda ki ke mgana a kai ba." Da haka sai bakin Rukky ya mutu daganan suka yi sallama su ka fita, ita kuma ta koma akin Inna Meri, domin tana jin ta kamar uwa a gareta sannan su Bintu kamar yan'uwa ta auke su tana da sakewa a acikin su sosai. Hira suke yi tsakanin Bintu da Walida Inna na saka baki jefi jefi, Shigowar wasu makota Allah ya sanya alheri yasa su ka tattara su ka koma akin Mimi suna cigaba da hiran su. Rabin labaran Bintu ke yin su tana ba su labarin irin artabun da suke bugawa ita da abokiyar zaman ta a gidan su. Mimi ta ri e baki tana fa in" Bintu ha kaki ke daman? Masu sunan mu fa ba ruwan su." Walida ta ce" kice Allah kin tuba Anty Mimi, Bintu ai tsiya ce da kafafunta ai Yaya Bashir na hakuri." Bintu ta karkace kai kafin ta ce" Kamar ya ha ura, zama daram in ji mai naguda." Mimi na ta dariya Walida na taya ta ita kuma Bintu har ta na juya ido kamar Bashir in ke gabanta. Bangaren su Rukky kuma suna fita, daman Debora ke da mota ita ta auko su, yanzu ma za ta ara aukan su zuwa can ma'aikata daga can kowa ya kama gaban shi, amman Rukky a saman hanya za ta sauka gida za ta wuce direct. Tsegemu ke cin bakin Aisha Farida har sun kama hanya sai kawai ta dafa kafa an Rukky domin dukkan su uku ne a gidan baya ita da faridan da Aisha sai a gidan gaba Grace sai Debora dake driving. "Ke na ta a ki da alheri Rukky, sai na ga Mimi a gidan da ban yi tsammani ba, kuma ai kin fa a min wallo za ta aura ko ba haka ba! Kuma ni abunda ya ba ni mamaki nasan an ce wallo na samun ku Aisha ta farida ta fa a tana kallon Rukky wacce ta ta e baki kafin ta ce" Ke da gidan shi fa, tsabar wulakanci ne ya sa ya ijiyeta gidan gado." Lauratu ta yi saurin cewa" Bangane ba? To me ya hana Mimin zama a gidan na shi? Rukky ta ce" Ra'ayi mana, ba ku san mijin nan na Mimi ba ne, mugun an ra'ayin ri au ne kamar an Salaf." Aisha Farida ta ce" Dan ari, kuma ta san da haka ta amince ta aure shi? Rukky ta rausayar da kai kafin ta ce" Tana son shi ne, shiyasa ta amince da duka sharu ansa, ai ta san da cewa ya ce tare da mahaifiyarsa za ta zauna kuma ta ji ta gani." Aisha Farida da sauri ta ce" Lalle Mimi ba ta da Tunani, soyayyar banza da arya? Har yaushe su ka ha u da take jin in bashi ba za ta iya rayuwa ba? Rukky ta ce"Soyayyar yarinta ce kin san ta na da zafi da wuyar mantawa, nan ta shiga fa a musu sharu dan da Aji ya saka kafin aure da yadda aka yi aure ko abunda ba'a so bai kawo ba." Rukky ta arishe da fa in" Ba shi da mutumci ni nan da na kira shi kan mganar biki har zagina ya yi, in na yi mgana kuma Mimi ta ji haushi na ba ta son laifin shi." Lauratu ta ce" Kan uban can, lalle fatima ta yi kuskure ai ba ka nuna ma Namiji in ba shi ba za ka iya rayuwa ba, kamar Mimi mace mai kyau da zati ne za ta yi aure kamar a wula an ce? Namiji ai ba ka nuna masa soyayyarka a fili da ya fahimci kana mutuwar son shi ka ta shi aiki." Aisha Farida ta sauke Ajiyar zuciya kafin ta ce" Ni na kasa mgana, mamaki duk ya kamani ban ta a jin wannan abun ba wlh, kuma iyayenta suka amince? Rukky ta ce" E, suna sonta kowa ba ya son acin ranta da cewa kafin Abin ta ya rasu yace a bata duk abunda take so." Kawai sai Aisha Farida ta ce" Ni ko zan so na ga wannnan Mijin na Mimi naga abunda ya ke ta ama da shi haka." Rukky na yar dariya ta ce" Ganin sa ba wani abu ne mai wahala ba, ai ya sanu a harkan wallon kafa ta garin nan ki shiga Goggle ki yi searching in sunan shi ko kuma ki saka Gombe United Captain za ki ga sun watso miki hotunan shi." Da sauri Aisha Farida ta bu e jakarta ta auko wayarta irar Infinix, jikin ta har rawa yake ta bu data Lauratu da Rukky na yi mata dariya su Debora kuma ba sa ma ta kansu hiran su ke yi cikin harshen turanci ita da Grace, cikin abunda bai gaza mintina goma ba sai ga Goggle ta watso ma Aisha Farida Hotunan Aji cikin kayan wallo ma su kara masa kyau da kwarjini. ara zooming in Hoton sa ta yi, wanda su ka ci kofi a Jos lokacin da su ka je buga wasa
Chapter 91 · 0% Book details