Sashe 142
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai ya gwammaci YA CIZA ya hura kafin ya ara aikata laifi mai kama da wanda ya aika miki a baya tabbas zai gane kuren shi duk wannan jin kan da bakar zuciyar da wani jin haushi sai ya sauke shi, shi in banza da Wofi tunda dai yana son mu ai kuma ya tashi aiki." Irin yadda Rukky ke mgana cikin warin gwiwa ya sa Mimi sai da ta yi dariya kafin ta jinjina kai tana fa in" Ru ayya ba irin su Aji ake yi ma haka ba, Da bakin shi fa ya ce ba ya sona alfarman rokon su Hajiya ya sa ya aureni, to a haka ne kike tunanin wai zo ya na ro o na? Rukky ba ki san Aji ba ne shi ya sa." Rukky ta kalli Miki cikin tausayawa kafin ta murmusa lokaci aya tana cewa" arya fa yake yi, duk kalaman da ya fa a miki karya ne, kuma zai aryata kansa da kansa a gabanki nan ba da jimawa ba." Mimi ta karkace kai kafin ta ce"Rukky ba na tunanin haka, ni nasan wanda nake aure Rukky" Rukky ta ce" Ki yarda da ni, ni kuma na yarda da kaina, amman kafin nan ya kamata ke ma kinsan kuskuren ki a kan wannan lamarin gaba aya." Mimi ta kalli Rukky amman ba ta yi mgana ba sai Rukky ta kama hannuwanta ta rike lokaci aya tana fa in"In har kin yarda dani to ina ba ki tabbacin Aji zai zo da kafarsa, sannan zai ta bulayin neman ki, zai iya yin komai saboda ke Mimi." Mimi ta yi shuru ta na kallon Rukky itama ta na kallonta na wani lokaci kafin Mimi ta Sauke ajiyar zuciya tana fa in" Shike nan na aminta dake, amman sai na k.. "Shii..., Ki yi shuru kawai, kawo kunnen ki ji." Rukky ta fa a dai dai tana jawo kunnen Mimi ta yi mata mgana na tsawon mintina goma sannan ta sake ta. Sannan lokaci aya suka koma suna kallon juna, Mimi ta age giranta sama kafin ta ce" Are u sure Ru ayya? Rukky ta amsa mata da ceewa"very very sure.." Hannu Mimi ta ba ta suka tafa lokaci aya tana in" Yoh have my word, zan yi gwargwadon abin da kika ce." Ita kuma Rukky sai ta aika mata da Jinjina tana dariya. Mimi ta sauke numfashi, kafin ta ce"Sai yanzu na ji na samu yar natsuwa, ina jin ki fa amin kuskurena, ni kaina nasan ai na yi gaggawa." Rukky ta gyara zama L lokaci aya tana fa in" kuskuren ki guda aya ne, na yadda ki ka nuna masa kina tsananin son shi, za ki iya komai saboda shi, kin nuna masa sai da shi za ki iya farinciki, r da wannan damar ya samu yana miki yadda ya ga dama, da wannan damar ya ke tunanin zai iya yi miki komai ki shanye, a tunaninsa saboda kina son shi zaki iya jure duk mganganun da zai ga ya miki, yana tunanin ko dukan ki yake yi ba za ki iya aga kai ba. Shi Namiji ba ka nuna masa ka mutu saboda Son shi, ko kana son shi sai ka koyi iya Sarrafa soyayyar ta yarda ba zai zama makamin da zai samu galaba a kan ki ba, amman ko a yanzu lokaci bai kure miki ba za ki iya gyara abin da ki ka ata tun farko." Mimi ta sauke numfashi kafin ta ce" Tabbas kin yi gaskiya, da wannan damar ya samu galaba a kaina ya ke tunanin ko ni ce ya yi ma ba dai dai ba sai dai na yi hakuri na bi shi tunda Ina son shi, to ya yi kuskure daga yanzu zai fahimci hasashensa ba gaskiya ba ne." Rukky ta ba ta hannu suka tafa lokaci aya tana fa in" Thats my Girl." Zuwan Rukky ba aramin garinciki ya kawo ma Mimi ba har su Hajiya na Jiyo hiransu da shewan su. Sai bayan isha'i Rukky ta tafi bayan ta ci abinci ta yi sallah Sannan su ka yi sallama da Mimi akan sai sun yi mgana ta waya su ka ai suka san irin muguntar da suka shiryama Bawan Allah Baban Inna. A baya ba ta cika barin wayarta na awa hu u a kunne ba amman yanzu da shawaran Rukky da ta ce ta daina kashe wayarta tun ba karya ta yi ba. Ta ri a barin wayarta a kunne amman kada ta amsa kiran yan koran Aji ta bari shi Ajin da kansa ya kawo kansa sannan. Shi ya sa har Mu'azzam da su Nasir ta rufe su ko sun kirata ba za su sameta ba a daran ma sai da su ka yi waya da Mommy itama abun ya ba ta haushi da Mimi ta ba ta tabbacin Mansoor bai kira ba kuma bai zo ba. Cikin acin rai ta ce"Na fara yarda da Maganar Alhaji Hamza, in bai kira ba kada ki kira shi in bai zo ba, ba za mu bi shi ba sannan ba za ki koma ba in watanni uku suka cika kotu zan kaisa ya sauwa e miki tunda bai san hallaci da mutumci ba." Kenan itama Mommy ta fara Dawowa daga rakiyarsa Hajiya dai yar cewa a bi komai a sannu. ******* Har aka shafe wajen sati biyu da komawar Mimi gidan Hajiya, Ba Mansoor ba eyarsa bai ara tako kafarsa gidan Inna Meri ba, ita kuma daman ta ce ta cire hannunta a kansa. Baba anjuma ne yaga rashin jankalin Mansoor ya yi yawa sai ya kira shi a waya yace duk abunda ya ke yi yau da daddare ya zo gida ya same shi. Sai ya amsa masa da toh, shi kuma daman Kunyar Inna meri yake ji, yana so sai ta fara hucewa sannan yana fargaba ya shigo gidan ba Mimi a cikin shi. Har gabansa faduwa yake yi in ya tuna bata nan bayan ganinta a cikin gidan ashin Inuwarsa Kuzarinsa har karuwa yake yi in ya shigo gidan ya ganta, yana so ya kirata amnan kuma yana tunanin in ya kirata kenan ta yi nasara shi ya sa yake iya sarrafa damuwarsa amman shi duk a tunaninsa Mimi za ta dawo domin kanta bai ta a tunanin za ta iya ba shi Wahala ba. Wajajen karfe tara ya zo anguwan a mashin in haya saboda motarsa sai an mata juye, mashin kuma duk ya yi kura tunda ya da e bai yi amfani da shi ba, Sai kawai ya hayo na haya ya zo a kofar gida ya iske Baban Danjuman na jiran shi, ya san akwai mgana aiko ya sha fa a kamar zai dake shi yana kuma nuna masa illar abin da ya aikata Mahaifiyarsa na fushi da shi amman ya nuna bai damu ba. Kansa na asa ya ce"Na damu mana Baba, kawai dai na ga ranta Inna ya aci sai na bari a an kwana biyu in ta ara hucewa sai na zo na bata hakuri." Baba kamar ya kai masa duka cikin takaicinsa ya ce" Haba Baban inna ina tunaninka yake ne? Ita uwa in ta yi fushi ba ta bukatar a bata lokaci Mansoor, a lokacin za ka yi kokarin kaga ka nemi gafaranta yanzu adadin kwanakin da ka ara adadin acin ranta a kanka, Maza mu je cikin gida ka duka ka nemi gafaranta." Kafa da kafa Baba anjuma ya tasa shi har falon Inna Meri ta na zaune tana kallon Tibi tunda akwai wutar nepa. Walida na kwance kan kujera tana game da wayar Inna. Sautin wa a kuma na tashi daga akin Matar Saddiqu haka take duk dare ta hana mutane sukuni. Bayan sun shigo Walida ta mike tana gaishe su Baba ka ai ya amsa ban da uban gayyar, Inna Meri ko mijinta ka ai ta yi ma sannu da zuwa Mansoor ko kallo bai isheta ba. Sun zauna kenan Shi Baba a saman kujera shi kuma Aji a assn cafet. "Daga ina wannan sautin ke fitowa? Baba ya fa a lokaci aya yana kallon Inna Meri wacce ta yi kamar ba ta ji ba,Junoir ne kan jikinta ya yi barci shi kawai ta gyara masa kwanciya ta cigaba da kallon shirin gata nan gatan nan ku da ake haskawa a Karamchi tibi. Walida ce da ta kawo musu ruwa ta ce"Baba akin Matar Yaya Saddiqu ce wlh tunda ta dawo wannan bangaren ba ta barin mu yi barci da saka kide ki e. Da Inna ta yi mgana sai cewa ta yi nan gidan Mijinta ne ba wanda ya isa ya takura mata." Mansoor ya ji ransa ya ba i sai dai bai yi mgana ba ganin Baba ya yi shuru kawai bai ce komai ba Domin magajiya ta fi karfinsa har barazana ya yi mata na saki amman ta nuna bata damu ba sannan Inna Meri ta ce kada ya hana natar Saddiqu tarewa domin Allah kar ya sake mgana shi kuma yana ganin darajan Inna shi ya sa ya yi shuru. "Je ki fa a mata ta in ji ni na ce ta kashe sautin nan, ko ba ta san dare ya yi ba ne? Baba ya fa a cikin nuna acin ransa, sai Walida ta amsa da toh, har za ta fita Inna Meri ta dago tana fa in" Walida dawo abun ki, kyaleta Mallam ai gaskiya ta fa a nan din gidan mijinta ne, ni ban isa na takura mata ba." "To Inna ke sa'arta ne da za ta gaya miki haka? Ko ba ki isa ki ce ta daina abin da take yi ba ne? Mansoor ya fa a ransa bace, Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" ta isa ne shi ya sa ta fa i haka, me ya sa zan damu? duk wa ya ja min? an da na haifa ne da cikina ya sa na koma abun cin mutumcin acikin gidan nan tunda ko shima bai auke ni wata aba mai daraja ba, to tunda an da na haifa bai ganni da daraja ba wa zai kake tunanin zai kalleni da daraja? Ta fa a cikin jin una a cikin ranta. "Ki yi ha uri Inna.." Ta yi masa shuru kamar ba ta jisa ba. Sai da