← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 208

Sashe 88

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai aran fanka kawai a ke ji tare da saukan numfaashin su a hankali. "Zan iya komawa ciki na kwanta? Mimi ta fa a tana kallon gefe, kamar ba da shi ta ke yi ba shima bai kalleta ba ya ce" Ban gama mgana dake ba malama" Acikin ranta ta ce ya illahi, kafin ta ora wani tunani ta ji ya fara fa in" ba na son hul ar da awaye, in abokan hira kike nema ina da kanne da Yayye ga Bintu nan kusa damu take, in ta kama ne sai ta zo nan wajen ki, kema in ta kama zan iya miki izini ki je wajenta, sannan akwai Yaya Amina da Yaya Halima duk anan garin suke aure, su ma za ki iya neman su ba matsala domin na yarda da su, ba zan hana ki hul a da yan'uwanki da dangin ki ba, amman ki sani ki yi hul ar iya wanda addini yace a yi, in kika wuce gona da iri zan iya datse alaqar gaba aya, so ki kiyaye duk abunda na ga ya miki saboda tsira da martaban auran ki." Baki ta bu e tana kallon shi, kuma ya ga kalamansa sun ba ta mamaki gudun wata mgana ya sa ya gyara zama sai gani kawai ta yi ya kwanta lokaci aya yana fa in"Za ki iya tafiya na sallame ki." Daga haka kawai ta ga ya yi matashi da hannayensa ko filolin Kujera bai auka ba, abunda ya bata mamaki anan zai kwana? Kuma da wa anan kayan na jikin shi? Sai dai yadda ya yi in bai ba ta ikon sake wata mgana ba kawai sai ta mi e ta wuce cikin akin ta lokaci aya ta na fa in" Sai da Safe" ba ta san ko ya amsa ba ita dai ta shige ciki ta maida kofa ta rufe tana jin wani iri a asan ranta. Anya har yanzu Aji na sonta kuwa? Sai ta ke ganin shi yana wani abu kamar wani ba o a wajenta. Ita sai kalamansa na arshe ya ba ta dariya wato ya yarda da an'uwansa ta yi hul ar da su amman na ta an'uwan ne bai amince da su, lalle ne ma ya na da arfin hali, mganar awaye kuma ita ba ta da su awarta aya ne Rukky kuma akwai aminci mai karfi a tsakaninsu. Watsar da tunanin shi ta yi acikin ranta, ta kwa e kayan jikinta ta fa a tiolet wanka ta yi har yanzu ba ta fara sallah ba domin wajen kwana tara ta ke yin jinin al'adanta, bayan ta fito wanka ta gyara jikinta ta saka wata yar doguwar rigar barcinta sabuwa mai hannun Vest sai ta saka wata hularta ta barci mai taushi asaman kanta, har ta kwanta sai ta ji ta kasa kwanciyar saboda ba ta kashe hasken akin ba, sai da ta mi e ta je ta kashe wutar sai ta bu e kofar akin ka an ta leka falon amman sai taga ba ta ganin kowa sai dubu alamun kamar ya kashe hasken falon, shuru falon sai aran fanka da gudunta ta da e tsaye kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida kofar ta rufe gam sannan ta kashe hasken akin ta koma ta haye gadonta ta yi addu'an barci ta ja bargo ta rufe kafarta da shi, ta so ko blanket in ta kai masa falo, amman ganin ba fuska sai ta fasa ila baya jin sanyi ne. Shi ko ya na kwance saman kujera har lokacin da ta ri a le ensa daga kofar akin ta na ciki ya na ganinta, Saboda akwai haske daga cikin akin da haka ya samu damar gane ta na le owa cikin falon bai yi wani motsi ba har ta gaji ta maida Kofar ta rufe, shi kuma sai da ya tabbatar da ta kwanta sannan ya mi e ya cire rigar jikinsa har da farar vest in da ke jikinsa ya kwanta daga shi sai dogon wando ba i saboda ya saba bai iya kwana da kaya a jikin sa. Ya da e bai yi barci ba yana tunanin Yadda Rlrayuwa za ta ara kaisa baya kar an wannan auran da ya yi. A tsarin shi ba tsarin zama a gidan nan tare da Mimi sai dai kuma ya manta wacece Inna Meri, za ta kula da dukkan motsin sa ne tare da Mimi acikin gidan nan, komawar sa can gidan da kwana ba zai yu yu ba saboda ranar da Inna ta san ba ya kwana a gidan akwai matsala, shi kuma a wannan yanayin bai shirya zama ko rayuwa waje aya da Mimi tukunna dai, ko da ya na son ma ya zauna da ita abunda ya faru a shekarun ba zai bar shi ya zauna da ita cikin salama ba. Ya da e bai yi barci ba har gabanin arfe 3pm na dare sannan barci ya kwashe shi, bai farka ba sai da ya ji kiran sallar Assalatu a tsakar kansa kamar a mafarki sannan ya iya mi ewa ya lalubi wayarsa ya na dubawa sai ya ga biyar na asuba ta gota da Mintina ashirin, duk yadda ake ciki ana gabda ta da sallah sai ya yi hanzarin mi ewa ya saka rigar shi sannan ya bu e kofa ya fita, a kofar akin Inna ya ga silafas in ta da alamun ruwa a jikin takalmi sai ya ba shi tabbacin Innar ta tashi tun azu, Kuma sai ya samu tabbaci da ganin hasken wuta a cikin akin ta, bai shiga ciki ba sai ya zura takalmin ya auki buta anan bakin katon roban ruwan inna ya zuba ruwa ya zagaya makewayin sa na waje ya kama ruwa bayan ya fito ya duka nan ya yi alwala sannan a gurguje ya fita zuwaa masallaci jin har an tada sallah. Sai da aka sallame salla sannan su ka ha u da Baba ya bashi hannu suka yi musabaha kamar yadda su ka saba. "Baban inna jiya na ri ga ka shigowa gidan ina jin ko? Kansa na asa ya ce"Eh na shigo Inna ta ce har ka shiga ciki." Sai ya amsa da cewa jiya nan ya gaji yana shiga shima ya kwanta, tare su ka fito daga masallaci nan su ka ha u da su Baba Sani, ya yi musu irin gaisuwar da ya saba suka amsa suna kallonsa a karkace, har Baba anlami na ara fa in" Ai jiya Halima ta shigo da matar tacka da daddare mu ka ce ba mu ganta dakyau ba, itama ai ko a hanya ba za ta shaida mu ba gwara a kawo ta ido na ganin ido ko ba haka ba Sani? Baba Sani ya gyara tsayuwa ya na fa in" warai da gaske anlami." Daga Baba anjuma har Mansoor ba wanda ya kula su, har su ka ariso gida su ka rabe su suka fa a bangaren su, suma su ka shiga kofar bangaren su, a gefen akin Saddiqu Mansoor daman ya kafe mashi in sa tun jiya da daddare suna shiga gidan su ka iske Mariya na alwala nan bakin rariya ta na ganinsu sai ta fara sunkuyar da kai, domin har gari ya fara haske shidda na Safe ta gota. "Baba ina kwana? Yaya Mansoor barka da Safiya? Baba anjuma ya amsa mata kai tsaye shi gogan ne sai da ya ce"Me ya sa ba ki yi sallah ba sai yanzu? Sai ta fara sosai kai kafin ta ce"Magajiya ce ba ta tashe ni ba." Kamar zai yi mgana sai ya fasa Baba anjuma kuma har zai wuce akin sa sai ya fasa ya juya ya na kallon Mansoor lokaci aya yana fa in" Baban Inna le a min akin nan ka gane min ko yaron man Saddiqu ya ta shi? Ba na ganin sa a duka sallolin nan Allah yasa ma ya na yin sallar" Dai dai Mansoor ya juya zuwa akin ita kuma magajiya tana fitowa daga cikin akin ta auke da mgana a bakinta. "Allah ya sa ma ya na yin sallar? me kake nufi da maganar ka ne anjuma? Ta fa a a kausashe kamar yadda muryanta take a sama, kuma cikin gadara, ba Mariya ka ai ta ji wani iri da sunan Baba da Magajiya ta kira gatsal ba, har Mansoor sai da ya tsaya da tafiya ya juya ya kalleta ita kuma sai ta ri e kugu tana ara fa in'" Na ce me kake nufi da maganar ka anjuma? Sanin da ya yi ba abunda ya shafe shi ba ne ya sa ya ka a kai ya wuce akin Saddiqu ya leka sa ya na kwance ya baje yana barci kamar gawa. Daga kofar akin ya ri a kwalamai kira amman bai tashi ba sai da ya taka ya shiga har cikin akin ya duka yana girgiza kafarsa sannan ya iya Motsawa. "kai wani irin barci ka ke yi kamar wani gawa? Mansoor ya ce ma Saddiqu bayan ya bu e ido ya ci karo da shi a saman kansa, mutsike ido ya yi yana ko arin ya koma barcin ne Mansoor ya yi saurin cewa" kasan arfe nawa yanzu? Ka ta shi ka yi salla gari ya fara haske." Sai Saddiqu ya ce"To ai shike nan aie Ta fa a cikin katuwar muryansa da ta ara girma saboda barci ya bar Mansoor na nazarin sa, ya na fatan Allah ya sa Saddiqu bai lalace a can Lagos da shaye shaye ba saboda yanayin sai a hankali. Har ya juya zai fita sai ya juyo yana kalloonsa lokaci aya yana fa in" ka ri okarin ta shi a kan Lokaci saboda ba girman ka ba ne da sai rana ta aga za ka ri a yin sallah, Sannan ka sani cikar magidanci ne shine yin sallar Khamsilsalawatu cikin jam'i, in kana son kyakyawan shaida ka daina bari salla cikin Jam'i tana wuce ka" Daga haka ya bar akin, har ya kariso kofar akin magajiya sai ya ji tana ta fada tana habaici" Ai ni ana acikin gidan nan an banza ne, ba a na gari ba ne. Sai an meri da kuma Agolan da zo mana shi yafi masu gida ma iko da gadara." Tana gama fa ar haka sai suka ha a ido
Chapter 88 · 0% Book details