Sashe 24
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nema a wajen ka." Sai ya juyo ya na kallonsa bai yi mgana ba Makama ya gyara zama yana fadin"Ba ku yi mgana da Mu'azzam ko Nasir ba? Sai ya girgiza kansa kafin ya ce"Ina Studio a gida na bar wayata ban sani ba ko sun kirani.". Ya fa aa kai tsaye yana wani tsuke fuska shi fa baya son takura Allah yasa ba wani abu za su ce zai yi a bikin nan ba. Allah ma ya sani shi har addu'a ya ri a yi Allah yasa ranar ma suna da wasa a wani garin ya bar garin sai bayan bikin sai ya dawo. Sai dai addu'arsa ba ta kar u ba sai ma watan gobe su ke da wasa kuma Kano pillars ne za ta zo wasan cikin gida za a buga, yana wannan tunanin ya ji makama na fa in " Dama alfarman wajen kwana nake nema akwai abokai na ko na ce yan'uwa ne daga Zariya za su zo sh ine zan sauke su a gidanka sai sauran dai abokan mu na nan ai duk kasan su." Mansoor ya kallesa a karkace kafin ya ce"Ban san su ba." Daga haka ya cigaba da fa in "Su nawa ne? Kasan ba na son takura kuma duk wanda zai zauna a gidana ina da dokoki." Makama ya ce" Ba za mu wuce mu goma ba." Mansoor ya kallesa cikin mamaki kafin ya ce"Ba ni da katifa, kuma akin da nake kwana ne ka ai a gyare" Makama ya ce"Bakomai ga falo tunda akwai cafet sai ayi amfani da barguna., Ni da kai da Nasir da Ahmad da Mu'azzam sai mu yi amfani da cikin akin naka." "Wani akin kenan? Har Mansoor na sauri wajen tambaya Makama ya nuna masa akin da hannu kafin ya ce"Nan ciki mana ai muma gobe duk nan zamu kwana Aji." Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba yana jin Makama na sanar da shi Ahmad ma gobe zai shigo garin cikin zolaya ya ce"Gobe akwai kwanan hira za mu tuna baya ne Aji." Kallon Makama kawai yake yi ya ma kasa magana sai dakyar ya bu e baki yace" Ni da Mu'azzam ka ai zan kwana, ku sai dai ku kwana a falo." Ya fa kai tsaye kuma da gaske yake yi Makama ya kallesa kafin ya ce"Ba ka isa ba, kai ko da yaushe sai ka nuna son kai wato Mu'azzam anin ka ko? Ba ka isa ba Allah tare duk zamu kwana sai dai ka koremu in mu baka son ganin mu.". Ya karishe fa a a kufule, Mansoor ya yi masa banza bai tanka sa ba sai cewar da ya yi" Ahmad da Nasir suna da mata fa to miye haka na wani zuwa su kwana a gida na? Mu fa ba yara ba ne mun girma Makama mu rika abu na masu Aji mana." Makama ya fashe da dariya har ya na dafa kafa an Aji kafin ya ce"Aji Aji! Aji namu ba zaka ta a sauyawa ba kai komai sai kace an yi abu na rashin Aji, Ahmad ai ya tafi da matarsa kaduna in da ya ke inki Nasir kuma ya ce gamu za mu kwana waje aya ba zai ware kansa ba" Mansoor ya yi aramin tsaki ya sauke hannun Makama daga kan kafa arsa yana fa in " Ka ji ba, to shi yaro ne? Makama sai faman dariya ya ke yi, Mansoor kuma haushi duk ya kama shi, yaushe ne su Nasir za su girma su daina aikin yara ne?miye wani abun zuwa a caku i a kwana waje aya sai kace masu shiga itfikafi. e rai ya yi ba halin ya ce kada su zo ya san su mayu ne domin su kure shi ma Nasir sai ya ce su zo, kuma ya na da tabbacin Mu'azzam ya kasa gaya masa ne ya sa ya ce makaman ya zo da kansa. A rayuwarsa ta yanzu ya fi son ya zauna shi ka ai ta fi yi masa da i in ka ganshi da mutane yan Club insu ne ko wani taro na buga wasa ko abin da ya danganci haka. Ko a baya da yake da sakin jiki da son mutane bai yi aikin yaran da su Nasir ke yi yanzu ba. Sama sama ya ji Makama na fa in"To yanzu dai ka amince mu zo ni da ba ina ko? Mansoor ya kallesa kafin ya ce"Ba na son mata a gidana, ko shaye shaye kai ko sigari na kama mutum na busamin sai na koresa, sannan 9pm nake rufe gidana in suna yawon dare ka fa a musu su kiyaye sannan kwana nawa za su yi ne? Makama ya bu e baki cikin mamaki kafin ya ce"Wa anan dokikin kamar na shiga Villa? Mansoor yace" Gidan Aji ya fi Villa martaba da matsayi." Makama ya jinjina kai kafin ya ce" Ba shakka kar ka damu iyakarsu kwana uku, kuma duk abin da ka zayyano ba sa mu'amala da ko aya mu kuma ka san mu tun muna matasan mu in ma muna da wani halin banza za ka fi kowa sani." Kamar magana ce ya gaya masa, shi kuma bai damu ba sai ma kafa a da ya aga masa ma'ana is better. Makama bai ara wasu mintina ba, ya ma Aji sallama ya wuce gida saboda ya san ko ya zauna ba biye masa zai yi su tattauna ba tunda yasan hali, shi ko Mansoor Makama na tafiya ya auko wayarsa ya kira Mu'azzam. Yana auka ya fara masifa ta in da yake shiga ba ta nan ya ke fita ba. i yake yi" kai ne ka ce su zo su kwana a gidana ko Mu'azzam? ka san me ka jawo ko? Mu'azzanm dai sai cewa ya ke yi"Ni fa ba ruwana ya yi min mgana ne na ce ya je ya same ka ya ji ta bakin ka." A Fusace Mansoor ya ce" Mu'azzam ka fara zama mara jin magana yanzu ko? Yaushe ka zama haka? To ka guji ha uwarmu sai na sa a maka." Daga haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam da dafe kansa dagacan bangaren. Hibba na gefensa daman suna cin abinci ne kuma a wayar akwai kara taji fa an da Mijinta ya sha. Cikin kwantar da murya tace"Ka ta o Baban Inna yau." Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ce" Na rasa me ya sa ya ke gudun mutane yanzu? Alhalin a baya ba haka Dan'uwana yake ba." Ya fad'a kamar zai yi kuka, Kansa take shafawa kafin ta ce"Ka yi hakuri mu cigaba da gayama Allah In sha Allahu komai zai wuce" Huci kawai ya saki ta baki wani abu na sukan ranshi. Hibba ita ta yi ta lallaahinsa har ya samu ya saki ranshi. Shifa Nasir ne ya matsa masa amman yasan haka za ta faru bayan shi Mansoor ba ya son ra ar kowa ciki harda abokan da suka taso tare tun suna yara. A bangaren Mansoor kuwa kwana ya yi ya na sakawa yana warwara, kamar ya gudu ya je Camp in su ya kwana sai dai kuma ba ma evining training gare su gobe ba Morning ne haka kurum y ji baya son wannan ha uwar, ha uwar tana nufin tuna wasu abubuwan da suka shu e a baya. Da ace kafin ya sauya rayuwarsa ne ya san zai fi kowa murnan ganin sa a waje aya tare da makama , da Ahmad da Nasir, saboda abokansa ne tun lokacin da Inna Meri aure ya kawo ta Gombe a kuma anguwan Arawa su ya fara sani bayan Mu'azzam. Har gari ya waye bai samu mafita ba hakanan ya shirya ya tafi Studio din su yana shiga wajen daman shi ka ai ke jira sai ji kawai kake yi " Barka da safiya Captain" shi kuma yana aga musu hannu dukkansu suna sanye da yellow din riga da annanun wanduna takalman kafarsu ma mai ruwan kwai ne, suna shirye waje aya a layi dukkansu kowa ya har e hannayensa a bayan hannunsa sun kame waje aya. Wajen Cauch in su ya nufa shima yana Shirye da irin kayansu hannun ya bashi suka yi musabaha. Cikin yanayin maganarsa ya ce"Barka da safiya Coach." Shima ya amsa masa da cewa" Barka da safiya Captain." Nan da nan aka hura usir members suka fara gudanar da training in su. A gida ya bar wayarsa saboda ya san za a yi ta kiransa a waya sai wajen sha biyu ya koma gida ya yi wanka ya an kwanta kafin azahar sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga an kira shi da yawa harda Mu'azzam sai Nasir. Kiran Mu'azzam ya bi, bayan ya dauka sun gaisa yace gashi ya iso yanzu ba da jimawa ba. Shi kuma sai ya ce yana gida zai huta sai zuwa bayan la'asar zai shigo anguwan, ko kiran Nasir bai bi takai ba ya share shi saboda tun a zamanin baya sun fi yawan samun sa ani da Nasir. Nasir akwai da a mgana ko kaji haushi ko ta yi maka da shi kuma Mansoor saurin hasala da zuciya da masifa ko magana za ka iya yi ya ce da shi kake shi ya sa suke saurin samun matsala da Nasir ko a baya. Bai yarda barci ya daukesa ba sai da ya je ya yi sallar azahar sannan ya dawo ya kwanta kuma ya samu barci sai uku da rabi ya tashi. Ya ji kuma zuciyarsa ta rage nauyi tunda daman ya da e ba ya samun barcin dare sosai. Wanka ya sake yi ya shirya cikin wata Riga ta kwallo ce an saka MESSI a jikin rigar saboda shi Mansoor allon waikwayonsa a kwallo tun a zamanin baya Messi ne har kuma yanzu da yake cikin kwallon dumu dumu bai sauya gwani ba, sai ya saka bakin wando mai kamawa ta kasa ka an ya yi zanzanro sannan ya saka wani bakin takalmi mai rufi ya kuma gyara gashin kansa da ya tara sai ya ora P.Cap saboda ba ya so Inna ko Baba su gani su yi masa fa an rashin aski. Ranar har da fesa turare abon da ya jima bai yi ba. Key din mota ya auka da ita yau ya ke fita