← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 208

Sashe 124

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

garin kano amman za a samu aramar hukuma cem Sai kuma tuka tukan ruwan a kace za a yi su a garin Zariya tunda suna fama da matsalan ruwa. Mimi ba ta cika wani saka baki ba ta na can ta yi nisa acikin tunani sai da Khadi ta ta o ta sannan ta dawo wajen su. Dr ya kalleta cikin yar damuwa kafin ya ce" Me ke damunki ne? Kina yin lost haka ana mgana? Mimi ta sunkunyar da kai kafin ta ce" Bakomai Dr, ina ta tunanin Abi ne." Hajiya ta ce" Shi kuma addu'a ne tsakanin mu, damuwa ko kuka ba namu ba ne." "Ku wai a tunanin ku, kukan da Mimi take yi na Abi ne? Hmm ni fa nasan za'a zo wannan ga ar tunda ta zo gata nan kamar mara lafiya ina amfanin wannan antattaciyar rayuwar da Mimi ta je fa kanta? Na fa a zan ara fa a har gobe ba na ganin Abin da Abi ya aikata a baya a matsayin oaifi, abin da ya yi shi ne a dai dai da ko wani good father zai ya aikata." Madiha ta fa a kai tsaye ba ta kuma damu da mutanen dake falon ba ta cigaba da fa in" Yes!. Akwai tarin bambamci tsakanin talaka da mai arzi i, daga ganin Mimi ba ta farinciki a inda taie, Hajiya da Mommy suka goya mata baya ta yi shirme, Abu an yi shi tun tana da Kuruciya in ha uwar su Kuskure ne me zai saka kuma mu maida auran su kuskure? Just imaging fa Mimi ta yi aure amman ko posting ban iya yi a Hhndel ina na social media ba Saboda ina kunyar nuna wannan auran a matsayin auran kanwata, da inda daman talaka ya fara ganin ya an fara samun ku i sai ya ga kamar zai iya ha a Kafa a da mai arziki, kamar dai miji nan na Mimi shi ba an uban kowa ba sai girman kai da Isa nawa gare shi? me ya tare? Wa ya tsaya masa? Ko ganin ya na kwallon kafa shi ya sanu dole a bi shi? To a wallon ma a garin su wasu ba su san shi ba, kuma a hakan ya ri a kafa ma mutane dokoki, yanzu haka Mimi ta daina saka mayafi sai fama da hijabai duk ya dankwafar da ita ta koma kamar wata tsohuwa tana rayuwa a gidan da ba ta da sakewa da sunan SO, na bi son da gudu in ita ba ta da hankali Hajiya da Mommy kun fita sanin abin da ya dace da ita.." Ta karishe fa a tana ka a kafa falon ya yi shuru kowa ita yake kallo, Mommy ta yi shuru ta kasa magana Hajiya kuma a ranta ta ce" Kamar uba kamar ar domin abin da Madiha ta fa a, kamar maimaicin kalaman ubanta ne a baya." Khadi ma shuru ta yi ba ta yi mgana ba, Khalifa ne ya ta o Madiha sai ta kalle shi kafin ta ce" Ya! Is True ka bari na fa i gaskiya na tsamo anwata cikin Halin da ta ke ciki! Mimi kalleni? Ta fa a tana maida hankalinta kan Mimi, wacce take ta sharan kwalla a karon farko ta fahimci wata gaskiyan acikin Kalaman Madiha a yau. Sai ta ago tana kallonta alamun tana sauraranta kai tsaye Madiha ta ce" In har kin ga kina cutuwa a wannan auran ki yi mgana, ba abun kunya ba ne in kin nemi saki ya sake ki kin dawo gida. Ga jaheed na tabbata har gobe yana sonki, ga mustapha abokin Khalifa in yau kika kira shi zai zo domin ki, ni dai ki bar auran wannan mutumin kwata kwata baku dace da juna ba, zai ga kamar wuyan sa ya isa ne da zai iya ha a kafa a dake a rayuwa alhalin kuma kin fishi komai na gatan duniya, ke ba ajin sa ba ne" "Kin gan naki nan Madiha, ka ji min yar buhu da rabi" Hajiya ta fa a tana aika ma Madiha da dakuwa za ta yi mgana Hajiya ta tare ta da fa in" Saboda baki da tunani sai ki zauna kina cewa ar'uwarki ta kaso auranta ta zo gida ta zauna? Madiha ta tura baki kafin ta ce"To Hajiya ina amfanin wannan auran na Mimi? Ba cigaba kwata kwata tun bayan auran nata." Hajiya ta harare ta kafin ta ce" Eh mana ai ke ba za ki ga amfanin shi ba, amman ai kina ganin amfanin naki auran ko? Sai kallo ya koma kan Hajiya ita kuma ta ha e rai cikin fa a ta cigaba da fa in" Ke kina zaune da mijinki da anki ba wanda ya taba tunanin ya shiga rayuwar auran ki, kuma ba wai baki da matsalan ba ne, ba ma'auranta duniyan nan da za'a ce ba su da matsala wa ya takura miki? Ba ke da kanki ki ke warware matsalolin ki ba? Ko wani ya ta a cewa ki kashe auran ki? haka kurum ke kina da auran ki ita kuma sai ki kashe mata nata, kuma da kike mganar akwai masu sonta a da ne su ke son ta amman da zaran ta kashe auran ta fito wlh ba za su dawo ba sai kalilan, ke me yasa wani lokacin ba ki yin tunani kafin ki yi mgana? Hajiya ta arishe fa a ta na nuna Madiha da yatsa, wacce ke tura baki kafin ta ce' Ni Hajiya ina laifina daga fa in gaskiya sai ki faramin fa e gaskiyar ta ki, ba ma so ki ce ki yi tutiua da duk abin da kike ta ama da shi amman ki yale binta ta yi zaman auran ta, kibar ta ta ji da matsalolin gidan auran ta kamar kowacce mace, kema Allah ka ai yasan matsalar da kika ta a fuskantar tsakanin ki da mijin ki? wa ya ta a ji? Ko za ki ce baku ta a samun matsala ba ne? Ai sai Madiha ta kasa mgana Hajiya ta nuna kowa tace kowa na da matsalolinsa na Rayuwa kuma a Hlhankali muke warware su, itama Binta a barta ta warware duka matsalolimta tunda ita matar aure ce tana da Iyalanta ba dole sai mun yi katsalan ba. Sannan ta ce ma Madiha kar ta ara saka baki akan rayuwar auran Binta in kuma ta ara sai ta sa a mata. Madiha ta mi e tana kunkuni Hajiya ta rakata da fa in" Ko uban naki da kike koyi kafin mutuwarsa sai da ya yi nadama , to shi Allah ya so shi da rahama ya yi nadama kafin mutuwarsa, ke in baki yi wasa ba ranar nadamar taki ba za ta yi miki kyau ba, sannan da kike mganar me mijin Binta ya ke da shi? ba shi da komai amman ai bai zo maula wajen ki ba, sannan biyar in ki ba ki ta a bashi domin ya rike kansa ba kin ga keman ba ki da ikon kiran ba shi da komai, shi ko ke da komai tun da ya san darajan kansa sannan yana ishin kansa da na Iyayensa kin so ya zo nan yana muku maula, sai kuma kika ga akasin haka shi ya sa kike mana wata mganar banza." Sai Madiha ta fashe da kuka domin ran Hajiya ya aci, haka ta yi ta fa a dakyar Mommy ta lallasheta ta yi shuru. Khadi ma ba ta yi mgana ba saboda a mganganun Hajiya akwai gaskiya a ciki, Kowa fa da na shi matsalan auran sai dai na wani yafi na wani ko ita gabda tahowar su ne suka shirya da Muhammad, case ne suka yi ta yi kan yana soyayya da wata i'arsa abin haushin ma ba auran yarinyar zai yi ba amman yana soyayyar shan minti da ita ka an ya rage Khadi ba ta bar masa gidansa amman sai ga shi sun dai dai da kansu ba ma wanda ya ji. Ita kanta Madihan ba za ta fa i ba ne, amman itama akwai tarin matsaloli a auranta da khalifa ko ta bangaren dangin mijinta ba sa son ta, amman ba ta zencen da kowa amman duk gasan ta da suke yi ba ta ta a fitowa ta yi magana ba, wani abun na cikin aure barin shi a rufe ya fi alheri da bayyana shi Ita dai Mimi har aka ci aka su e ba ta yi mgana ba sai da ta koma aki ta ci kukanta ta koshi, da safe kuma sai ta tashi kamar ba ita ba, tare da Sara suka yi abun karyawa. Ta saki jikinta kamar ba ita ba kuma ko a fuska ba ta nuna wani abu ba, Madihan dai tana cin magani ta ga an yi banza da ita sosai ta ware. Su Dr daman suna ayan bangaren can suke kwana yunda gidan babba ne ranar Park su ka je su ka yini suka ci suka sha suka sha jotuna da sauran su, sai dare suka dawo gida washehari ma su ka fita da yara wajen wassani Hajiya dai ta ce ba za ta je ba ta ga ji da zrga zirga, tuni Mimi ta manta da damuwarta ta mori hutunta a garin Abuja. Kwanan su Khadi hu u dukkansu suka koma saboda ayyukan su, Mimi kuma ta ce sai sun yi sati, ba ta waya da Aji amman suna mgana da Inna da Walida. Sai ga Mimi ta share sama da sati a garin Abuja da Mommy ta yi mgans sai ta ce Mansoor ne ya ce ta yi sati biyu, Hajiya kuma daman ba ta da matsala sai suka share kafa a garin Abuja. Suna da kwana goma a garin Abuja mijin Yaya Amina ya samu ha ari, tare da Babban yaron Yaya Amina Sadiq shi Sadiq in nan take ya rasu. aurin auran kanin mijin Yaya Amina suka je Bauchi shi ne suka yi hatsari a hanyar su ta dawowa. Dalilin da ya sa Mimi ta yi shirin dawowa kenan, Tunda shi mijin Yaya Amina yana asibiti rai ga hanun Allah ga rashin kuma da aka yi hankula dai duk a tashe. Kwanan su goma sha biyu a Abuja Mimi da Hajiya suka biyo jirgi suka dawo
Chapter 124 · 0% Book details