← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 208

Sashe 47

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kira wayar sojan sannan aka bu e musu get suka shiga cikin gida. Har da Yaddiko a ka zo sai ga su kowa ya yi zaman sanyi a cikin falon gidan Major Kabir, Inna Meri tana shan kuka lokaci aya tana ri e da hannun Mu'azzam, Mimi kuma ma na jikin Mami tana wani irin kuka mai ban tausayi. Hajiya kuwa girgiza jiki kawai take yi ta kasa mgana domin kunyar su Inna Meri take ji, tun bayan gaisawar da suka yi da Mommy ga shi an kawo musu ruwa da lemu amman zullumi ya hana kowa motsi. Hajiya ta kalli Alhaji Hamza lokaci aya tana fa in" Wai ba ka ga ya ma Kabiru har da ni aka zo ba ne?. Cikin ladabi ya ce" Na gaya masa Hajiya, ya ce ga shi nan tahowa." Sai kawai ta jinjina kai wani abu na taso mata acikin kirjinta. Murja ta kalla da ke rike da arta itama daga gani ta sha kuka ba ta cikin natsuwarta. Cikin tsausayi Hajiya ta ce" Murja har ke Kabiru bai saurare ki ba ko? Kuma ba ki san inda ya sa a ka kai yaron mutane ba ko? Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Ba irin rokon da ban yi masa ba Hajiya an uwansa ma yana kuka ya ro onsa amman bai saurare mu ba, bai sa an fita da shi ba ya na nan acikin Kurkunsa na cikin gida, ba wanda ya isa ya sa su fito da shi sai in har shi ne ya ba su umarni Hajiya." Yaddiko ta yi kasa e kafin ta ce"Kai jama'a kurkuku kuma ? Mommy ta gya a mata kai kafin ta ce"Eh ya na da wani aramin aki da bai wuce tsawon gajerun mutum ba, sannan ba shi da fa i kuma a asan yake, akan sanya mutum a ciki in ya yi wani laifi domin a yi masa horo." Gabadaya sai Inna Meri da Baba Danjuma su ka kara ru ewa, Yaddiko ta saka salati Hajiya ta karishe ma ta shi ko Alhaji Hamza kai ya girgiza kafin ya ce" To duk me ya yi zafi? Wannan lamarin da duk an bi shi a hankali da an warware komai cikin sau Inna Meri ta zube a kan kafafunta daga saman Kujera ta ha a hannayenta waje aya tana fa in"Don girman Allah Hajiya kin yi min rai ki saka a saki Baban Inna wlh na yi miki alkwarin ko hanyar gidan ki bazan kara kallo ba har abada,ni dai ku saka ya sake shi kuma shima in sha Allahu ba zai kara kusantar Inda ar ku take ba, laifin yaro ne tunaninsa ba ya ba su abu dai dai in da ace yayi tunanin shi kanshi ba zai janyo ma kansa rigimar da ta fi karfinsa ba.". Tana mgana tana kuka Mu'azzam na taya ta sai aka rasa mai lallashinta ballantana ya ce wani abu, Hajiya ke sharan kwalla a oye Mommy kuma na tausayin arta ne. Ana cikin wannan halin sai ga Major kabir ya shigo cikin kakinsa na aiki wani Soja na mara masa baya. Yana shigowa cikin takunsa na zafin nama na cikakkun mazan jiya, sai ya aga ma Sojan hannu fuskar nan ba rahama shi kuma sai ya juya ya fita bayan ya sara masa. Baba anjuma kallo aya ya yi masa shima tsoronsa ya kamasa sai ga shi shima zube kan kafafunsa kusa da Inn Meri ya na rawan jiki da na zuciya. Ya ga Hajiya a zaune amman bai nufe ta ba sai ya samu wata kujera mai zaman mutum aya ya zauna ya ora kafa aaya kan aya ya na are ma mutanen falon kallo har ya sauke kan Hajiya cikin yanayin maganarsa ta Sojoji ya ce" Hajiya duk wannan taron na menene.? da kun yi zaman ku yaro zai yi wasa da gidan Soja ne shi ne nake so na koya masa hankali nan gaba ko sunan Soja ya ji an ambata sai ya yi fitsarin jini acikin Wandonsa." Kafin Hajiya ta samu zarafin mgana Inna Meri ta rarrafa tsakiyar falon kamar ta kwanta masa, ita ko iya kallonsa ba ta yi saboda firgici cikin ro o kamar zai yi mata gafara ta fara fa in"Don Allah ka yi masa aikin gafara ka yi hakuri ka yafe masa yarinta ke damunsa amman ina wuyan Baban Inna ya yi karfin da zai ja da kai? Ka yi masa rai don Allah ka sake shi." Take fa a tana kuka har da majina, A kaikace Major ya kalleta cikin wani irin Murya ya ce"Wace ce ke? A razane ta ce"Ni ni mahaifiyarsa ce, ga mahaifinsa nan." Ta fa a ta na nuna Baba anjuma da shima ya ariso tsakiyar falon da jan gwiwa Mu'azzam ganin iyayensa duke kamar masu neman gafara ya sa shima ya rarrafa cikin jan gwiwa zuwa kusa da su ya durkusa ba zai bari kimar iyayensa ta zube ba, ko da ba shi da yarda zai yi gwara shima ya yi zaman neman gafaran tare da su. Sai da Major ya gama musu kallon wula anci sannan ya yi wata irin sariya kafin ya ce"Ke ce uwar da kika ki haifi mara kunyar yaron da zai ja da ni? Kai kuma kai ne uban da ke rikon Agolan dake neman ja da Soja? Ya karishe fa a yana nuna kansa bayan kuma daga karshe ya nuna su aya bayan aya jikinsu na rawa kansu na kasa kamar sun ga wani mala'ikan mutuwa, kuma kowa ya kasa mgana Hajiya bakinta ne ya yi nauyi? Me za ta ce? Ko ta yi mgana ba zai ta a Sauraranta ba tunda halinsa ne baya girmama maganarta a matsayinta na uwa a gare shi. Alhaji Hamza ne ya yi gyaran Murya ya fara mgana da cewa" Major.." Sai kawai ya aga masa hannu cikin kaushin Murya ya ce"Ya raina matsayina, yaron ya yi min tsurin ido bayan ya fara soyayyaa da ata ba tare da sanina ba, sannan ya zo har gidana ina mgana yana tsaye ina tsaye sannan wai ni zai nuna ma tsageranci? Sai ni kuma na nuna masa ba'a zuwa gidan Soja a yi taurin kai na ce su yi ta dukansa in har bai yi nadama ya ba da hakuri ba, ka da su barshi ko duka zai kashe shi" Mimi ta saka wani irin kara ta mi e tana fa in" Abi." "Ke sai na harbe ki, in kika kara mgana anan wajen nonsess kawai." Ya fa a cikin zafin nama har yana mi ewa da sauri Mommy ta mike da sauri ta ma ale arta a bayanta tana rawan jiki, Hajiya ta yi yun urin mikewa dai dai sanda Inna Meri ke dukar da kanta a kasa tana ha a Major Kabir Allah da Annabi ya saki Mansoor shi kuma ya ce ba yanzu ba sai ya san da wanda ya ke fa a. Cikin yanayin ba da umarni Hajiya ta ce"Kabiru ni a matsayina na Mahaifiyarka na ce ka saki yaron mutane ka sake shi." Cikin kallon Hajiya ya ce"Hajiya kinsan me ya yi min ne? Kama na kamar ni wannan yaron talakawan zai ja da ni?. arfi Hajiya ta ce"Ba na son ji komai, ka sa ka a saki yaron nan yanzun nan ban san zalunci." Ta fa a cikin bayyana bacin ranta har da hawayenta sai ya fara huci yana wani cijewa kamar zai kai duka. Sai Hajiya ta fara kokarin dukawa tana Fadin" Ko nima sai na duka ne?. Da sauri Alhaji Hamza ya mike ya isa ga Hajiya ya ri e ta yana Fa in" Haba Hajiya ai kin wuce haka a wajen Yaya zai yi abin da kike so yanzu ma kuwa" Major Kabir ya kallah kafin ya ce" Major ka sa a saki yaron nan don Allah, ka duba darajan Hajiya ga kukan da rokon da iyayen yaron ke yi maka, ka yi masa afuwa ka saka a sake shi." Yadikko ma ta saka baki, sai da Hajiya ta fashe da kuka tana Fadin"Shike nan kabiru kada ka sake shi. Wlh in har wani abu ya sami yaron mutane ba zan ta a yafe maka ba." Jin haka yasa Alhaji Hamza ya ce" Major ka sarrafa fushinka, Hajiya ke mgana da kai fa." Sai da ya fitar da iska daga bakinsa sannan ya aga waya ya kira aya daga cikin Sojojin ya ce a taho da wannan yaron zuwa falonsa ya na jiran su. Cikin lokaci ka an da bai gaza mintina goma ba sai ga shi sun shigo da shi kamar sun auko wani cuta suna zuwa tsakiyar falon suka sake shi ya fa i kasa warwas tunda ba shi wani kuzari, Kamar ma sun watsa masa ruwa ne ya farfa o tunda faran rigan jikinsa duk ya baci da jini, fuzkarsa ta kumbura idanuwansa sun shige ciki saboda tsabar duka bakinsa ya sumtuma da goshinsa. Bai iya kuma motsa hannunsa na dama da kafarsa ta hagu ba, kallo aya zaka yi masa ka san cewa ya bugu buguwa na sosai tunda har kammaninsa ya sauya. Da wani irin sauri da kuka Inna Meri da Baba anjuma suka nufi Mansoor Mu'azzam ya tarairayo sa jikinsa yana ta kiran sunan shi amman ko iya bu e ido ba ya yi saboda tsabar duka, yana so ma ya bude ido ko ya yi mgana ya kasa Allah ne ya yi kwanansa na gaba kwana suka yi suna dukanshi, shi kuma bakar zuciyarsa ta hana shi ya yi nadama. Inna Meri ta riko hannun da na dama da sauri ta ga ya janye hannu ya na cije le ensa da duk ya fashe saboda duka cikin kuka Mu'azzam ya ce"Inna bar ta a hannun kila ya samu gocewa ne." Baba anjuma yana share ma Mansoor jinin goshinsa da ha an rigansa lokaci aya yana kiran sunan shi"Baban Inna bu e idanuwan ka? Baban Inna, Baban inna" Haka yake ta kiran sunan shi yana jin su amman kuma ya kasa iya bu e idanuwansa. Mmi na le ensa ta bayan Mommy tana kuka ta san in ta ce za ta karisa sai Abi ya saka bindiga ya auke kanta Khadija ma tana falon amman itama ko motsi ta kasa, Hajiya kuwa sai kawai ta
Chapter 47 · 0% Book details