← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 208

Sashe 107

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

son ranki yar Major kike gata sai dai ki ba ma wani labari." ganin Hibba a Motar ya sa ba ta yi mgana ba, sai ta kauda kanta. Ba ta so ganin wani na ta na rashin lafiya ballantana Hajiya da ba tsohuwa ce mai laulayin ciwo ba, ta da e ba ta ga ta yi ciwon da ya kwantar da ita irin haka ba shi ya sa ta damu, bayan sun koma gida Mimi akin ta yi kai tsaye shi kuma sai ya tsaya dakin Inna Shi da Hibba wacce bayan gaisawar da suka yi da Inna ta ce ya mai jiki? Ta ce ta ji sau i ta shige ciki ta iske Junior da Walida Barcinn su ma ya yi nisa, ita daman katifa take sakawa a asa ta kwanta Inna Meri kuma ba ta damuwa ita ko a asa ta na kwana kuma ga gado amman ba ta cika kwanciya a kai ba. Mansoor ya sanar da Inna mganar tafiyarsu gobe daganan ya sallame ta da kudi y na fa in" Inna ku ri e a hannun ki, ina ga kamar za mu kai kamar sati aya a can." Inna ta kar a ta na fa in" Allah ya ysare ka, Allah ya baku nasara duk in da ka sanya Kafa Allah ya sada ka da slherin sa Baban Inna." Ya ri a amsawa da Amin kafin ya ce" Baba ya shigo ne ko? Ko ya kwanta ne? Inna Meri ta ce" Eh yana cikin akin sa, amman ban yi tunanin ya kwanta ban da e da dawowa daga wajen sa ba." Sai ya ce bari in zai wuce zai shiga ya yi masa sallama. Shuru na wani lokaci Kafin Inna ta ce" Ka ta shi ka je ka yi ma matarka sallama tun da ka ce da asuba za ku tafi ko? Sai ya gya a mata kai kafin ya mi e yana fa in" Shike nan Inna zan tafi, sai mun yi magana." Inna ta raka shi da fatan Allah ya tsare su har ya fita ta walama masa kira ya dawo kai tsaye ta ce" Kana waya da Gwaggon ka Yalwa kuwa? da sauran babanin naka? Sai ya sosa kai kafin ya ce" Mun kwana biyu ba mu waya ba, amman ina na samu sarari in sha Allahu zan kira su." Inna Meri ta ce" Ya dai kama ta, ka ri an'uwan mahaifinka domin ba ka da wa anda su ka fi su a yanzu, azu bayan fitar ka mun yi waya da ita Yalwa take tambayata kai nace ka na nan, har ta ke fa a min Mumbashir an wajen Babanka Karimu ya yi hatsari a mashin ya samu karaya a Kafa da cinya ana ta wahala sai an gyara orin bai yi ba, Domin Allah Baban Inna in ka samu sarari ka kira su ka ji yadda ake ciki na taimakawa ka taimaka musu." Kai Tsaye ya ce" In sha Allahu, Allah ya ba shi lafiya." Inna ta amsa da Amin ta ora da fa in" Allah ya ba da iko, itama Bintar in ka samu sarari ko daga baya ne, sai ka tafi tare da ita ta ga sauran dangin ka za su ji da i, har Bauchi sai ku wuce wajen Babanka Kabiru" Shi dai na shi Toh ne, domin ba shi da abi'an gaddama. Daga akin Inna sai ya arisa akin Mimi sai da ya tura domin ta sakaya kofar, falon ba kowa tana ciki. Mimi na daga cikin bedroom ta fito wanka kenan ta ji kamar ana kiran ta. "Fatima.." "Mimi.." Sai kuma ta ji kamar muryan Aji abun sai ya ba ta mamaki daga ita sai towel ta manta da yanayin da tske ciki sai da ta fito falo ta ganshi tsaye yana jiran ta sai faman duba agogon fatan da ke hannunsa yake yi. Fararen kafafunta ya fara gani in da ace yasan abunda zai gani kenan ba zai yarda ya aga kansa ya ga abunda zai iya hana shi barci ba. Amman Ina idanuwansa ya rinjayesa, hatta saman irjin Mimi a waje ya ke, domin towel arami ne iyakarsa rabin cinyarta, ba ta fahimci a yanayin da ta fito ba sai da ta ga irin kallon da yake mata sannan ta ara bin kanta da kallo ai da sauri ta juya ta koma ciki ta sanyo hijabi sannan ta sake fitowa. Abun mamaki ta na fitowa har ya auko ku i ya ijiye a saman Kujera kai tsaye yana fa in" Gobe za mu tafi Ibadan buga wasa,kila za mu yi sati." Sai kuma ya dakata yana runtse ido sannan kuma ya bu e a lokaci aya domin kirjinsa ne ya ji yana toshewa. "Ki kula da kanki.." *Mimi" Ya fa i mganar a rarrabe, Mimi tana fa in" Allah ya kiyaye hanya, a dawo lafiya Allah kuma ya ba da nasara" A kofar akin ya ji karshen addu'an ta, ya amsa da mirmishi a saman le ensa, ya da e a tsaye sannan ya tura mata kofar ya rufe sai ya ke ji kamar ya je ya rumgumeta ko zuciyarsa za ta tsaya daga hargagin da take yi masa amman kuma ya kasa domin sai yake ganin kamar hakan ya yi kusa. Sai da ya kara lekawa akin Inna Meri ya yi mata sallama sannan ya wuce, da farko ya shiga akin Mimi da saka mata dokar kar ta ara fita sai ya dawo amman kuma har ya fito zuciyarsa ba ta rinjayi bakinsa wajen fa in haka ba. Bai shiga akin Baba anjuma ba, Saboda tun daga barowansa shashen Inna ya ke jin masifan Magajiya tana ta manganu, shi ya sa bai shiga ba ya tsaya daga waje ya yi sallama Baban ya amsa amman matar nan ba ta ji kunya ba taci gaba yi, kuma ko da ta ga Mansor in domin Baban ya ce ya shigo Kai tsaye bayan ya shiga akin ya zauna ya na gaida Baba ya amsa cikin fara'a itama Magajiya ya juya yana ce mata barka da dare ba ta amsa ba illah tsaki da ta ja tana fa in" Kana tafe tarairayan Agola nan da auran sa babu ne kawai ba ka ba da ba amman auran an ka na cikin ka komai akace sai kace baka da shi to da ikon Allah baza'a ga kunya ta a cikin gidan nan ba." Sai kawai ta fice a fusace har ta na ture Mansoor, shi dai ya yi shuru kansa na kasa. Baba anjuma ya girgiza kai kafin ya ce" Allah ya Sauwa Daga nan ya maida jankalinsa kan Mansoor su ka ara gaisawa, Mansoor ya yi masa sallama kan tafiyarsa. Baba danjuma ya ce" Ma sha Allah, to Allah ya tsare muku hanya, Allah ya sa aje lafiya a dawo lafiya cike da nasara." Mansoor ya amsa da Amin. Nan take shima ya ijiye masa kudi masu yawa yana fa in" Baba ga shi ba yawa ka ri e a hannun ka saboda hidima, mganar abincin sha'anin nan kuma mun yi mgana da Auwalu zan tura masa komai za'a yi Baba, sannan inkin da za ka je aurin aure Mu'azzam ya tura Ahmad ya inka zuwa gobe ko Jibi za'a sako a mota, ba na nan za'a yi aurin aure ina ga Allah ya sanya alheri." Baba anjuma sai kawai ya fara sharan wallah lokaci aya yana fa in" Allah Sarki, na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwarka albarka mansoor, Allah ya baka zuru'a ta gari Allah ya baka ma su share maka hawaye Allah ya ji an Mahaifin ka." Mansoor ya ce" Amin Baba ka daina kuka, Duk duniya ba ni da wani uban da ya fika, meye amfanin samu na in ban yi muku ba? Baba na sharen walla ya ce"Haka ne Na gode Allah ya yi muku albarka kai da an'uwan ka gaba aya" Nan dai su ka yi sallama Har kofar gida ya raka shi nan ya ga su Baba sani a tsaye suna jiran shi da na su orafi wai ba su da kayan zuwa auri aure alhalin suna yi musu kaya fa, hakanan ya cire sauran kuda en hannun shi ya ba su sannan su ka barshi ya tafi. Baba anjuma ya koma aki yana ta kukan farinciki yanzu nan bala'in da Magajiya ta gama yi wai bai ba da kudin Cefanen abincin biki ba cewar da ya yi ba shi da shi ne gori ya tashi wai nikin Agola babu ne kawai bai ba da ba, ita duk ba ta san nauyin su har da ita kanta na kan Mansoor da Mu'azzam ba ne Auwalu ma sune ke auke da shi. Da kansa ya tashi ya leka akin nata ya mi a mata ku in kuma ta amshe ko kunya. Shi kuma kawai sai ya ce mata" Agolan da ki ka tsana tare da shi Mu'azzam in da kike ganin an Miji ne ba an ki ba sune rufin asirina da na ki gaba aya Magajiya, gwara tun wuri ki shiga taitayin ki, domin kada watarana ki ji kunya" Daga haka ya wuce ya barta nan ta na raka shi tsaki kaafin ta ce" Eh in na ji, kuma ni dai ba su rne ufin asiri na ba, sai dai in daman kai ne ka kwanta zuciyarka ta mutu." Kuma tasan gaskiya amman hassada da yashi ya hana ta fuskantar gaskiya. Washegari tun asuba su Aji suka kama hanya shi da Yan team in sa tare da Couch in su, sannan sun tafi tare da wasu sauran ananun kungoyiyin wallon kafa na Cikin gari irin su Tudun wada United, sun tafi da manyan yan wasan su, Mimi ta kira Aji da safen wayarsa a kashe sai kawai ta tura mishi Sa "Safe Landeed Ajin Mimi..." Bai bu e wayarsa ba sai da su ka tsaya a janya suka yi salla da cin abinci sannan ya kunna wayarsa a lokacin ne ya ga sakon Mimi, sunan da ta kira shi da shi ne ya sa sai tsikar jikinsa ya ta shi, kamar zai maida mata amsa sai kawai ya fasa ya ce in suka sauka zai kira ta. Kuma sai cikin dare suka sauka a garin sun samu tarba daga Babban kungiyar wallon kafa na garin Ibada sannan sun
Chapter 107 · 0% Book details