← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 208

Sashe 43

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma ta manta waye Kabiru ta auka haihuwarsa da ta yi ya isa ya sa ya bi abin da take so. Major Kabiru bai san halin da ake ciki ba, Brr Murjanatu ka ai ta sani tunda ita macece kuma yaran sun fi sabawa da ita shi kullum fuska ba fara'a tsoro tsoron sa ma suke ji, kuma Mimi in ta zo hutu daga baya nan tana yawan kamata suna waya da wannan yaron da ta ce Mimi ta bar maganan sa, ta yi ma Hajiya orafi Hajiya ta ce ta kyaleta tunda har Binta na son wannan yaron to sai a zauna a ga abunda Ubangiji ya tsara, ita ba wai talauci ko yanayin rayuwa ba aaya ba, abu daya take dubawa sun yi yarinta da yawa da maganar aure, sannan ta san waye mahaifin Mimi ba shi da tsarin aurar da ita yanzu to ko Madiha karatu take yi bai saka maganar auranta ba, ballantana Mimi da ta ke just 19 tabbas ta san akwai kura. Ita Hajiya ta fara kira akan maganar Saboda suna da kyakyawan alaqa na mutuntawa a matsayinta na surukarta, Mommy ta ji tsoron da Hajiya ta ce ta fara tuntu ar Major da mganar cikin firgici ta ce"Hajiya wlh ba zan iya ba, kina ganin ko madiha wani yaron yayata na sonta da Major ya ji ba ki ji yadda yake ta masifa ba ya ce ba yanzu zai aurar da ita ba sai ta gama karatu ta fara aiki." Hajiya ta yi tsaki kafin ta ce"To ai wannan tsarinsa ne ba tsarin Ubangiji ba, karatun ya fi auren daraja a wajensa ne? ya bar yara sun zama manya bai aurar da su ba da an yi magana sai ya ce ba yanzu ba shi Sulaimanu ai ya na can cikin jajayen fata har yanzu bai dawo kasar ba." Mommy ta ce" Hajiya karatun likitanci yake yi, sai nan da shekaru biyu zai dawo in sha Allahu." Hajiya tace"To dama dama shi tunda namiji ne amman matan ne ya le neman kashe musu rayuwa da tsatauran ra'ayinsa na banza, zan kirasa da kaina na yi masa mganar." Ranar a tsure Mommy ta dawo daga wajen aiki, fargaban ta aya ta san komai ya je ya dawo ita zai sauke ma bala'in zai ce tana sane da komai bata gaya masa ba sai da abu ya yi girma. A ranar da dadadde bayan ya dawo daga office Khadija na akinta tunda ita a nan Abujan ta ke karatu Madiha ce ke BUK kano ta na karatun ta acan, Mommy duk jikinta ba da i Sai fama take da fa uwan gaba tana Allah Allah ta ji ya ce Hajiya ta kirashi sai ta ji har sun gama cin abinci bai ce haka ba sai ta samu yar salama. Sai dai bayan sun koma falo suna hutawa yake ce mata Mimi zata dawo nan ta yi jarabawa so ya ke yi ta ta fi Jami'a mai kyau ta yi karatun likitanci akan abin da ya Shafi mata tunda Sulaiman ya na karantar fannin zuciya, Mommy ta kasa magana sai zufa ke yanko mata duk ko da sanyin Ac dake falon. Kallonta ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Honey lafiya? Ko baki da lafiya ne? Da sauri ta ce"No am fine." Saboda ya ga duk ta firgice sai ya yi dariyan basawa kafin ya ce" ko case in dake hanunki ne ya ba ki tsoro.? Dakyar ta yi ya e ta kasa mgana. Ta fi kowa sanin waye Major ba shi da kyau ko ya yi wanka ko acikin Sojojin shi mugu ne sannan ba shi da uzuri ballantana ragowa ga ra'ayin ri au ne da shi ita fa yanzu haka ba ta isa ta yi ba dai dai ba sai ya ce da gangan ta yi da farko ba haka yake ba daga baya lamarinsa ya kara ta'azzara. Daman can halinsa ne sai kuma ya zo ya ha e da kakin dake jikinsa sai takamarsa ta yi yawa. Daman shi fa ya tsani ace za'a ha ansa da komai, yadda yake kaunar an to kila sai aikinsa ne za su iya gogawa. kuma ya ci burin akan su da sai ya gina su zai aurar da su ga wanda ya dace in ya ji wannan labarin na Mimi ai sai ya harbeta daga ita har Mimin. "Kin ga ko na manta Ina Office Hajiya ta kirani ta na son yi mgana dani, na ce ma ta sai na koma gida, mi o min wayata na kirata in har ma akan Mimi ne sai dai ta yi hakuri zan kar bazan iya kara barin ta a garin nan ba yanzu." Can a sama Mommy ta ji Abi na mgana duk sai ta kara ru ewa, ba ta tashin ba sai da ya ara mata mgana sannan ta mike ta auko masa wayar wajen rawan jikin wayar ta fa asa haka ta duka Jiki na rawa ta tattaro masa wayar ta mika masa ya kar a lokaci aya yana fa in" Murja are u ok? Sai ta gya a mai kai, kasa tsayawa ta yi da sauri ta shige aki ya bi ta da kallo, bai auka wani abu ba sanin shi da ita akwai ta da saka dmuwar Case in dai ya na hannunta acikin ranta. Lambar Hajiya ya lalubo ya kirata, bayan ta auka sun gaisa ya ce"Hajiya ban jima da dawowa ba, ina fatan lafiya? Hajiya ta gyara zama tana fa " Lafiya alau, daman akan maganar Binta ne? Kai tsaye ya ce" Eh daman ina shirin miki maganarta nan zata dawo ta yi jarabawa so nake Bintar taki ta zama likitan mata Hajiya." Ya fa a cikin yar dariya Hajiya ta ha a rai kamar yana ganinta kafin ta ce" Eh to za ta iya zama likita amman daga baya yanzu dai aure take so." auka wasa Hajiya take yi sai da ya yi dariya kafin ya ce"Haba Hajiya aure kuma? Mimi ai ba ta san me ake kira aure ba." Hajiya ta ce"Ai ba jaririya ba ce shekaranta sha tara da gaske nake yi Akwai wani yaro an wajen Meri dake min aikace aikace sun shaku da Binta kuma yana sonta da gaske itama Bintar na son shi.." "Wait Hajiya kika ce yaron waye? Ya katse Hajiya cikin mamaki shi fa gani ya ke yi kamar ta tsuniya Hajiya ke karanta masa Hajiya tace"Eh yaron Meri ne matar dake taya ni zama." Mamaki ya hana shi magana Hajiya na son gayamasa wai yaron an wajen mai aikinta ne ke son Mimi, Shi haka ya yi sakacin da arsa ta za ma a arha da wani yaron talakawa zai ganta ya ce ya na so. Ai bai gama mamaki ba sai da ya ji Hajiya na fa a masa Mimi na son yaron kuma ta yarda ta aure shi kuma yaron iya sakandiri ya gama ya na son ya zama Soja to shi ya taimaka masa ya samu sojan daga baya komai menene sai ayi. Huci kawai ya ke yi ya kasa mgana, daman Hajiya ta matsa ya bar mata Mimi ne saboda ta bari wani yaron talakawa mara tarbiya su hore ma arsa kunne lalle ko idon sa idon yaron nan sai ya harbe shi. Kuma sai ya taka wuyan Mimi da har da bakinta take fa in za ta iya auran wani banzan yaron da bai da wata makomai mai kyau nan gaba. Kawai amsa ma Hajiya ya yi da Toh ko gama mganar ma ba ta yi ba ya katse wayar Hajiya da sauri ya kira an uwansa Alhaji Hamza. Cikin masifa ya fara gayamasa yana garin har ahaka ya faru wai Mimi ke fa in tana son auran wani yaron talakawa? Alhaji Hamza ya ce bai sani ba nan Major ya sanar dashi abin dHajiya ta ce ya kara da cewa"Hamza ka je ka samu Hajiya ina bukatar sanin tarihin yaron nan tun daga farko har arshe, sai na ji waye mai wannan tsautsayin da zai hure ma ata kunni." Daga haka ya kashe wayarsa ya mi e a fusace kamar ya yi bindiga tun daga falo ya ke walama Mommy kira. "Murja.." "Murja.." Khadija na akinta tana karatu sanda ta ji wannan kiran sai da hantar cikinta ya ka a domin a muryan Abi ta fahimci yau akwai bala'i a gidan nan, Mommy kuma tana jin yana kiranta tasan rufa rufa kuma ai ta kare. Shi ya sa ta sadakar ta fito da sauri tana gyara aurin ankwalinta lokaci aya tana in"Ga ni nan Habib...' "Da sanin ki Mimi ta fara soyayya da wani banza yaron talakawa? da sanin ki Murja Mimi take son ta bijirema tunanina? da sanin ki na ce.? Ya fa a a fusace kamar ya kai mata duka sai ta kauce cikin rawan jiki ta ce,"Ban ban sani.." "Sai na harbe shi, ko waye wlh sai na ga da abin da yake takama da shi. Ko madiha ban saka maganar auranta a kaina ba, sai Mimi? Mimi fa? Hajiya ba ta kyautamin ba wlh zan yi abin da zukata ba za su ji da i ba.". Ya ke fa a ya na huci cikin ara daka wata tsawa ya hau kiran sunan Khadija. "Khadija.." "Khadija.." Mommy jikinta na rawa ta ce"Khadija ba ta san komai ba Habibi." "Murja zan miki tijara na ce, arya kike yi kin san komai, Hajiya zata gaya miki kuma Mimi yarki ce kina sane da abin da ke faruwa, Wlh tallahi in har da saka hannun ki a abin da ke faruwa zan iya sakin ki a kan haka." Khadija ta ora hannu akanta san da ta fito ta ji maganar Abi Mommy kuma sai kawai ta juya tana kuka ta shige akinta acikin zuciyarta tana fadin" Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un.." Khadija ya kallah da ke tsaye tsuru tsuru, tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ke ma kin fara soyayya ne? za ku tsallake umarnina ne? Jikin Khadija na rawa ta duka tana fa in "Abi karatun ka ce za mu yi kuma shi nake yi, wlh ban ta a soyyayya da kowa ba." Yana faman sakin huci ya saka kafa ya daki tuberin gabansa kayan ciki suka watse da karfi yake taku zuwa cikin akinsa Khadija ta zura
Chapter 43 · 0% Book details