Sashe 1
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Normal Table No List Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Kq138XLB8DD4nRAQ5EnNLO *DAGA MARUBUCIYAR.* *GIDANMU* *TA FITA ZAKKA.* *KANA NAKA* *TSAKA MAI WUYA* *JANAFTY* *AREWABOOKS:Jamilaumarjanafty* *WATTPAD: JamilaUmar315* ANO DAGA LITTAFIN IDAN AN CIZA.* Gani take yi kamar a mafarki yau ita ce a gaban Aji tana kallon shi yana kallonta. Yau ita ce ga ta ga shi wanda tazaran dake tsakaninsu bai wuce taku biyu ba, sannan yau ita ce take fitar da numfaashi tare da jin umin numfashin Mansoor a cikin nata numfashin. Farinciki ne ya saka ta kuka yau kimanin shekaru goma rabon da ta saka shi a idanuwanta irin haka. Sai dai ta hango shi a hoto daman ya ce ta yi nisa da ganinsa shima zai yi nesa da jinta da ganinta na har abada. Da i ne ya cika mata zuciya da ya sa har ta kasa iya rike kanta sai kuka hawaye suna ta faman sintiti saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya mai kayatarwa. Shi kuma so yake yi ya hana idanuwansa kallonta amman sun i bashi ha in kai kamar an manne masa idanuwansa daga kallonta ,ga shi kuma kishi ne da wani irin ba inciki ke yunkuro masa, in da ya binne tasirin soyayyarta ke kokarin taso masa ya hana tasirin haka bayyana, acikin kirjinsa ya ke jin wani irin zafi zafi iskar wajen ta fara masa ka an domin ya ji hucin zafin na fita daga cikin wuyansa zuwa cikin bakinsa, jiyoyin kansa sun mike ra au kirjinsa na sama da kasa alamun bacin ransa da yanayin da yake ciki ya kai makuran kololiya. Bakinsa ya yi wani irin nauyin da ya kasa mgana duk a kokarinsa ya cira kafarsa da sauri ya bar wajen tun kafin sirrin dake cikin zuciyarsa a kulle a wani bangaren ya fallasa kansa. Yana okarin auke kafarsa daga gabanta ya ra a ta gefenta ya wuce ya ji maganarta cikin za in muryanta da tun asali wannan muryan ce ke kwantar masa da hankali. Sannan ganin mai murya na saka shi cikin farincikin da bai san iyaka ba, amman sanadin abunda ya faru yanzu jin za in muryan yake yi kamar saukar dalma acikin zuciyarsa sannan ganinta na sanya sa bakinciki yana guje ma ganinta ne kamar mutuwarsa. "Aji Nah.." Ta ara kiransa cikin rawan murya sai kawai ya yi kamar bai ji ba, ya aga kafarsa da sauri zai wuceta ita kuma da azama ta riko gefen hannun rigansa domin ba za ta ta a bari ya subuce ma ganinta ba, yadda ta rikesa ne yasa ya tsaya dole hannunta zara zara da yaji kunshi baki da ja ya bi da kallo rike da gefen hannun rigansa na hagu sannan ya sauke saman fuskarta kallon da ya yi mata ne yasa dole ta sake shi wasu hawayen na kara yi mata ambaliya a saman fuskarta. Tana sakin shi ya fara takunsa cikin sassarfa da gifi gif in sa kamar wani sadauki a fagen ya i ji yake yi in bai bar shakan numfashi tare da wannan yarinyar ba za a iya samun matsala. Kuma cikin su Mu'azzam an rasa mai karisowa kowa ya har e hannu a kirji yana kallon ikon Allah. Hatta Rukkaya dake gefe ta kasa karisawa. Tsabar mamaki da al'ajabi ya hana ta magana ballantana ta karisa wajen tambayoyi biyu ne acikin ranta. "A ina Mimi ta san wannan ba in mutumin mai bakin rai haka? "Me ya sa take kuka saboda ta gan shi? Wata zuciyar daga can gefen ta fa a mata" ko dai ko dai shi ne? Shi ne wannan in nan? Sai ta kara kallonsu tana nazarin wani abu dai dai lokacin da Mimi ta kara tattare riganta ta sha gaban Aji a karo na biyu, wannan karon da karfinta ta tare masa gabansa ta kuma saka hannayenta guda biyu ta tare hanyar tana fa i da arfi. "Ba za ka bar nan wajen ba har sai ka yi min mgana, ni ce fa Mimin ka Mansoor?. Ta fa a kuka na son wace mata, Mimin ka ce? Kalmar ta fi ata masa rai da ya sa a fusace ya kalleta cikin kakkausan murya ya ce"Ni na san ki ne? kin sanni ne? Ya fa a yana nuna kansa, jikin Mimi ya fara rawa, ta fara nuna kanta tana rawan baki ta ce" Ni ce fa? ba ka gane ni ba ne? Kai tsaye ya ce"Ba maganar ganewa ba ne, ban san ki ba, ban kuma ta ganinki ba kada ki kara ganina ko a hanya irin haka ki ce kin sanni in ba haka ba zan saka rayuwarki a uku, ni kinga na yi miki kama da sakaran namijin da ya san shashashan mata irin ku? Iyayena talakawa ne har yanzu muna lalla a rayuwarmu ne a inda Allah ya ijyemu ba zamu fa inda ya fi karfin mu ba." arishe fa a ya na nuna ta da babban yatsan da ke hannunsa zuwa lokacin tuni su Rukkaya sun umgume wajen dai dai lokacin da Mimi ta fashe da kuka tana fa in"Ko ba domin soyayyarmu ba, na ci arzikin kaunar da ta ha amu ka tsaya mu yi gaisuwan mutumci Aji." Kamar ta yarfa masa ruwan zafi haka ya saka hannu da karfi ya ture hannunta cikin tsautsayi ta yi gefe har sai da ta fa i bai juyo ba cikin aga murya ya ce" Har abada babu sauran mutumcin da ya rage tsakanina da ke Fatima Kabir Sulaiman Dabo, har abada kuwa saboda haka kada ma ki yaudari kanki." Daga haka ya taka jelan riganta zai wuce ita kuma ta yunkura da niyar tashi kawai sai ji kake keeeeee! Rigar jikinta ta yage ta wajen kugunta da aka saka raga raga a wajen saboda ya taka ita kuma ta ja sai ya yage ana ganin aurin cikinta a waje. Ya ji karan yagan abu sai ya an juya ka an yaga kaurin cikinta a waje wani irin hayaki yaji kamar idanuwansa na fita na zafin kishi, yanzu maza nawa ne a wannan wajen? In suka kalle mata jiki fa? Kawai sai ya ji kamar ya mutu. Ita kuma Mimi kuka ta fashe da shi cikin raunin murya take fa in "Don Allah don Allah Mansoor." Rukkaya ce ta ariso wajenta da gudu ta riketa ranta ya baci cikin masifa ta ce"Mimi me ye haka? ta ya ya zaki zauna wani wanda bai isa ba yana wulakanta ki haka?. Ya ji ta saboda har ya fara takawa zuwa wajen motar Mu'azzam sai kuma ya fasa ya dawo da zafin namansa lokacin Rukkaya da wata awar Bibi sun ta da Mimi tsaye sai ya ga ana ganin jikinta, tuni idanuwansa suka rufe yana tafiya kamar ya ji ya tashi sama. tsabar kishi da ya rufe masa ido yasa bai san lokacin da ya daka mata wani irin tsawa ba. "Ki tsaya anan, kar ki sake ki kara taku ko aya FATIMA.." Ya kira ta da sunanta da ba kowa ke kiranta da shi ba. Jikinta na rawa ta juya tana kallonsa kowa kuma sai ya koma yana kallonsa baki sake hatta ko su Mu'azzam Nasir har sai da ya murmusa shi fa daman yasan har gobe Aji bai daina son Mimi ba, kuma a kishinta kamar mahaukaci haka ya ke jin kansa. Wajensu ya nuga yana zuwa ya cilla ma Mu'azzam key in motarsa ya ca da sauri, shi kuma sai ya mika ma Ahmad hannunsa da sauri ya ora masa key in motarsa ya juya kamar wani namijin zaki ya wuce wajen motarsa shi duk saurinsa kar Mimi ta juya baya wajen maza su ga jikinta in hakan ta faru ai sai ya kusa mutuwa saboda ba inciki. Rukkaya kuma haushi wannan mulkin mallakan ya kamata a fusace ta ce"Dilla mu tafi yanzu ya gama wulakantaki sai kuma ya dawo yana ba ki umarni? waye shi Mimi na hawaye ga kuka cikin sauri ta ce"Umarninsa kamar dole ne a gare ni na bi Rukkayya" Rukky ta saki baki galala tana kallon Mimi dai lokacin da Aji ya dawo da wata bakar jaket tana da tsawo nashi ne ta jima acikin motarsa ashe za ta yi masa amfani. A gif gif in sa ya dawo gabansu ya saita rigan ya saka a jikin Mimi bai samu salama ba sai da yaga jaket din ta sauko har ta rufe in da ya yagen sannan ya sakar mata rigan. Bai kalleta ba duk nacin kallon da take yi masa , ga hawaye a saman fuskanta lokaci aya da wani irin mirmishin da ta jima ba ta yi kamar sa ba. Kamar walkiya ya bar wajen har ya shiga motarsa Rukkaya ta saka hannu za ta warce rigan jikin Mimi tana fa in"Ba za ki saka ba, ya damu da ke ya ture ki, kika fa i a gaban jama'u? gam ko Mimi ta rike rigan idanuwanta da hankalinta na kan Aji da ya shiga cikin mota. Duk da motar ba in gilasai ne jikinta na ba ta ita yake kallo, kamkame rigar tayi cikin mirmishin dake tafe da hawaye Ta ce"Ki bar min Rukky a kallah bayan tsawon wasu shekaru na kara samun tabbacin matsayina bai sauya ba, yana sona har gobe tunda bai daina kishin wasu mazan su ga jikina a bu e ba" Rukky ta bi ta da kallo kamar mai ta hankali sakinta ta yi ta so ne ta isa wajen motarsa ta zage shi sai dai kafin ta karisa ya fige motar da gudu ya fice daga haraban wajen Rukky ta aga murya tana fa an wulakanci kawai zaka ha u da dai dai da kai a gaba, kana ba in mutum sai fa in rai da nuna isa aikin banza kawai.". Ranta ya baci ganin gaba aya ya ata musu biki tana juyawa ta nufi wajen su Usman da kamar an da sa su. Bibi kuma da sauran awayenta sun rufe Mimi suna yi mata sannu. Cikin masifa Rukky ta ce" Usman wannan an wula anci daga ina? A gabanku ya ci zarafin awata waye shi? Kai tsaye Nasir ya ce"Aji.. MANSOOR IBRAHIM AJI. Gombe State United Captain" A fusace ta wurga ma Nasir harara kafin ta ce"Aikin banza shi ne me?