← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 198

Sashe 98

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***
K’arfe bakwai da rabi na dare ta shigo garin Kano, Allah ne kawai ya kiyaye mata hanya amma kam ita kanta tasan tayi rough driving yau d’in, wai donma tayi gamo da checkpoints da dama yau d’in a hanya amma da tuni ta tsufa garin Kano....
Kai tsaye unguwar nasu ta nufa, tana ganin gidan da Sameer ya kama masu da sunan nasu gidan ta tab’e baki ta nufi gidan da takeda tabbacin na sabbin iyayensa ne....
Koda ta ida parking saida ta tsaya tana k’arema gidan kallo fuska a yatsine, Wai yanzu nan shine mahaifar Partner d’inta, Wai yanzu wad’annan sune tushen partner... Kai haba Haba inaa da sakel, Wllhi alwashi ta d’auka duk yanda zatai saita raba Sameer da wad’annan mutanen... Lokaci guda ta fito daga cikin motar kana ta d’auki handbag d’inta dake bisa d’aya seat d’in, ga mayafin dama da ba wani na kirki bane an sab’asa bisa kafad’a.... Sai faman kad’a d’an makullin mota take, Aiko nan almajiran dake zama k’ofar gidan suka mata chaaa suna fad’in “Hajiya Allah ya kiyaye... Hajiya Allah ya kare.....” Sunayi suna kallonta tamkar a zuba masu ita a kwanon baran nasu sun cinyeta, wasu na faman shafa motar tata.....
Siyama kaman ta had’iyi rai don takaici... Sai faman toshe hanci take tana k’yank’yan da jikinta... Wani uban tsawa ta dararawa Almajiran nan tana fad’in “Kai ku matsa min a hanya kafin ku shafa min wani cutan....!!”
Tai maganar tana mai ci gaba da toshe hanci had’ida jan skirt d’inta sama ga takalaminta mai uban tsini da take taku dashi cikin k’warewa...
D’ayan Almajirin yace “Basaida na fad’a maku ba karkuje arniya ce gashi kun gani ai....”
Suka kwashe da dariya suna duban yanda Siyama ke taku sauran har suna kwaikwayon yanayin tafiyar tata.... D’aya da bai ida cin tuwo miyar kukan dake cikin kwanon baransa ba jikin farar benz d’in Siyama ya isa Aiko nan ya mata fenti da tuwo miyar kukan nan.... Yaran suka kuma tintsirewa da dariya kana suka bar wajen gudun kada a gansu..:

Ko darajan sallama basu samu daga Siyama ba, tana tsaye tsakiyar verandar Mamy sai faman yatsina fuska take tana kuma k’arema gidan kallo don wancan zuwan nata ana makokin Kausar sannan zuwan na Nabila ne shiyasa sam bata samu ta k’arema gidan kallo ba, hannu a kunkumi take kuma juya kai tana jinjina kai baki a tab’e take bin lungu da sak’o na gidan da kallo
“Tabb! I can’t believe this... Wai wannan gidan tantabarun shine gidansu Partner, wllhi sam bazata saku ba, dole na raba mijina da wad’annan matsiyatan...” Ta k’arashe tana mai kuma yamutsa fuska....

Fitowar Mamy kenan daga kitchen ta hangi mata tsaye k’ofar parlornta sai faman kalle kalle take....
Mamaki ya kama Mamy tana tunanin toh ko wace wannan..... Lokaci guda Mamy ta nufota tana mai furta “Sannu baiwar Allah.... Lafiya....? Daga ina....?”
A tare Mamy ta jefowa Siyama wad’annan tambayoyi...
Maimakon ta bata amsa ko ta sami darajan gaisuwa saima kaikaitowa da tai tana mai k’arema wacceke mata tambayoyin kallo daga sama har k’asa....
Hasken wutan lantarkin da ya gauraye cikin gidan shi ya baiwa Siyama daman ganin cikin k’wayar idanun Mamy wanda hakan ya bata tabbacin wannan matar tanada alak’a mai k’arfi da Sameer d’inta don ga tabbaci daga k’wayan idanunta wanda yake baisa maraba dana Sameer, cikin bak’in nasu bai cika bak’i sosai ba ya d’anyi kalan ruwan k’asa kad’an maimakon bak’i.... A hankali Siyama ta saki murmushi bayan ta ida duban Mamy daga sama zuwa k’asa kana tace “Mijina nazo nema....”

Karaf a kunnuwar Nabilah da fitowarta kenan daga parlor hannunta rik’eda plate d’in data ida cin abinci....
Aiko Nabilah ta saki murmushi sakamakon hango Siyama da tai, daga yanda take kafin Mamy ta sami zarafin baiwa Siyama amsa ta bud’e murya tace “Finally our unbearable sister in-law has arrived...” Tai maganar tana dariya lokaci guda ta iso gaban Siyama wacce k’irjinta ya soma bugu tinda ta sinkayo muryar Nabilah....
Mamy duban Nabilah dake murmusawa tana k’arewa Siyama kallo tai kana tace “Kin santa ne...?”
Nabilah ta kuma murmusawa kana ta dubi Siyama tace “A gidan nan mun girma da mutuntawa da daraja na sama dakai, but unfortunately Mamy Sirkarki ba haka take ba...!” Ta k’arashe maganar tana mai watsawa Siyama muguwar kallo...
Mamy da kanta gaba d’aya ya d’aure d’an bud’e murya tai taceda Nabilah “Wai meke faruwa ne... wacece wannan Nabilah...?”

Gyara tsayuwa Nabilah tai still idanunta naga Siyama da suke faman aikawa juna muguwar kallo tamkar su shak’e juna kana ta saki murmushi a hankali tana mai k’arewa Siyama kallo daga sama zuwa k’asa kana tace “Wannan ba kowa bace Mamy face sirkarki matar Yaya Ma’aruf d’anki...”
Allah sarki Mamy nan da nan murmushi ya cika fuskarta ta shiga d’aga labulen parlor tana fad’in “A a lale lale bismillah, Aiko Ma’aruf bai sanar damu zuwan naki ba, yi hak’uri da rashin fahimtar da na maki, ke Nabilah maza ki kirawo Auntyn ku.... Ta k’arashe tana gyarawa Siyama yanda zata zauna....
Nabilah kuwa dad’a matsowa kusan Siyama da tai tsaye tana hura hanci tai, murmushi saman fuskarta take kaiwa Siyama runguma lokaci guda take furta “Welcome to the Family Sister in-law...” Cikin sigan rad’a saitin kunnen Siyama take rad’a mata “I’ve got a lot of surprises for you Aunty Siyama... Get ready to receive them...” Tana ida fad’in haka ta saki plate d’in hannunta aiko sai jikin mayafin Siyama sauran miyan dake jikin plate d’in ya b’ata mayafin nata gaba d’aya.... Siyama ta d’ago idanunta da suka kad’a sukai jazir tana duban Nabilah dake ci gaba da murmushi, sai kuma ta zaro idanuwa waje tana fad’in “Aw sorry sorry, wayyo I’m too clumsy.... Gashi kuma bakicin miyar kuka na b’ata miki jiki dashi... I’m sorry... K’arasa ciki sirkarki na jiranki... Bara naje na kirawo sauran sirakan naki don ku gana da juna....” Tana ida fad’in haka ta tintsire da dariya kana tasa kai ta wuce tana wani kad’a jiki irin yanda takeyi idan ‘yan shak’iyancinta suna kusa....

Siyama data koma tamkar mutum mutumi shaye da tsananin mamaki take duban gyalenta da ya koma koriya koriya ga k’amshin kuka da daddawa dake tashi jikinta.....

Sai faman yatsine yastine take har saida Mamy ta kuma mata iso kafin ta shigo parlorn shima ba don taso ba sai don wani irin k’warjini da matar tai mata kuma wani ikon Allah ta nemi duk wani courage na watsawa matar rashin mutunci ta rasa musamman da taji Nabilah na cewa sirkartace....
Kan kace mai tuni Mamy ta cika gaban Siyama da kayan motsa baki wanda ko kallo basu ishi Siyamar ba....K’afafu d’aya bisa d’aya take ci gaba da yatsine yatsine tana faman k’yank’yan da jikinta tamkar wacce ke zaune cikin bola....

***

Tin tana karanta calendar dake manne jikin bangon Office d’in har dai ta soma gyangyad’awa, babu Sameer babu dalilinsa, har aka kirawo isha ta tashi tayi, nan yanda tai sallar ta d’an kishingid’a gyangyad’i na sand’arta....

***

A can gida kuwa sai tururwar zuwa ganin matar Ma’aruf ake, su matan Baffah Ado da yaransu, su Sakinah Basma Sadiya da sauransu, su Sakina iyalan gulma abin nema ya samu dama ana son ganin matar Ya Ma’aruf duk wannan gayu da ajin nasa, harda d’aukar takalminta sukai bakin k’ofa suna k’arema takalmin kallo harta lambar size d’in takalmin saida suka duba, Basma kaw har saka takalmin saida tai, Siyama dake hangosu daga cikin labulen parlorn tamkar ta d’aura hannu aka ta zunduma ihu haka taji, ina zata iya standing wad’Annan halittun da sunan dangin mijinta, ko a mafarki bata tab’a hasasho tsayuwa inuwa guda da irin wad’annan mutanen ba.... Muryar Aunty Lami da tun shigowarta ta kasa motsawa daga kusan Siyama ya dawoda Siyamar daga duniyar tunaninda ta tafi....
Saida ta murmusa ta kuma gyara zama had’ida waigawa gefe da gefe ta tabbata babu kowa a parlorn sai su biyu kana tace “Sirkarmu kenan... Ai na fad’a miki indai mutanen gidan nan ne saidai fah kiyi hak’uri don gaba d’aya haka suke, wasu irin mutane ne nima nan da kike gani da k’yar nai adopting zama dasu... Amma karki damu with time zaki saba zaibi jikinki and if you really loves Ma’aruf, then you’ve to put up with his family....”
Batakai aya ba Siyama dake faman watsa mata kallon k’ask’anci ta tari zancen da fad’in “I love him more than love itself, kuma mun riga mun tsara rayuwarmu babu ku cikin rayuwarmu and I assure you I’ll do everything in my power naga na rabashi da wannan rayuwar da ya jefa kansa ciki sabida he doesn’t belong here...” Ta k’arashe tana mai juya idanu cikin salo na harara....
Wani irin dad’i ne ya mamaye zuciyar Lami, suna neman hanyar kauda Ma’aruf a karo na biyu toh ga dama cikin sauk’i ya samesu, indai har shida wannan shed’aniyar matar tasa soyayyarsu mai k’arfi ne tsaf tayi imani zata rabashi da kowa nashi suyi nesa dasu....Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai duban Siyama da hankalinta yafi tafiya zuwa ga kiran da taketa dannawa a waya ba’a d’agawa, sai faman huci take tana hura hanci, ta kirasa yafi sau babu adadi bai d’agawa, kuma ita haka take idan tana son abu toh fa sai ta samu, dan haka ci gaba tai da kiran nasa...
Chapter 98 · 0% Book details