← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 198

Sashe 94

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Hafiz kuwa wajajen k’arfe taran dare ya shigo gidan mahaifinsa, wata sabuwa Baba Alhaji ya bijiro masa da zancen maida matarsa Sawwama d’akinta... Hafiz yana kumbure kumbure yake duban Hajiya kana yace “Amma dai Baba ka mance nima na kusan mutuwa kan munafukar yarinyar nan, Baba wllhi ba sona take ba, nayi imani kasheni kawai takeson yi... Haba haba saikace neman kai dani kuke... Kuda zakuyi yak’in dawo mun da farin cikina Zulfa’u kunje kuna yunk’urin dawo min da ajalina... Nidai wllhi gaskiya Baba...”
Dakatar dashi Baba Alhaji yai da fad’in “Kai rufemin baki... Shikenan kai duk wacce ka aura saika rabu da ita, so kake da k’anan shekarunka a soma k’irga maka aure... Ni nace zan dawo maka da Zulfa’u ince....?”
Hafiz ya d’ago da sauri yana washe baki yace “Allah da gaske Baba....?”
Baba Alhaji ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa nai maka alk’awarin dawo maka da matarka Zulfa’u gareka amma da sharad’i....”
Cikin zumud’i da k’osawa yace “Mecece sharad’in Baba...?”
Baba Alhaji ya murmusa kana yace “Alhamdulillah abinda nakeson ji kenan.... Sharad’in itace zaka maida matarka Sawwama d’akinta, ka mance komai ka maidata....”
Saida ya zabura da jin batun mahaifin nasa...
D’an girgiza kai ya soma yana fad’in “Haba Baba Dan Allah... Wllhi ni yanzu ko a k’afa aka d’auramin Sawwama zan kwance na gudu...”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Idan kanason Zulfa’u zaka maido Sawwama gobe gobe d’akinta... Na gama magana...” Daga haka mik’ewa yayi ya shige d’aki yabar Hafiz zaune wajen yana sak’e sak’e da zullumi...

Hajiya kaw salallami kawai tana salati tana furta zama bai ganta ba
***

Washe gari Khalid yai shirinsa ya nufi Kaduna dukda sanin cewa zasu kwashi ‘yan kallo musamman da mahaifiyarsa, gashi sam sun kasa samunsa a waya, fitowarsa kenan dashike gidan Sameer ya sauk’a a nan unguwar ya hangeta tafe ta nufi babban kwalta da alama makaranta ta nufa..... Saida ya sak’i sassanyar murmushi don dama yana tunani idan ta riga ta tafi makaranta ba lallai su samu suyi sallama ba....
Ya gefenta ya rab’o had’ida rage glass d’in motar yana sakar mata sassanyar murmushinsa yake furta sallama...
Murmushin itama ta sakar masa wannan karon had’ida amsa masa...
Khalid yaji dad’in murmushin da ya gani saman fuskarta kana yace “Is a good thing I found you here, da ban fito da wuri ba maybe da ko sallama bazamu samu muyi ba....”
Ta d’an dubesa da alaman tambaya... Jinjina mata kai yai kana yace “Kan hayata nake zan koma Kaduna yanzu....”
Nabilah ta d’an sadda kanta k’asa kana tace “Toh Allah shi kiyaye hanya ya kaika lafiya....”
Khalid ya amsada Ameen kana ya k’arada “Shiga muje na ajiyeki a school d’in....” Yayi maganar yana bud’e security lock....
D’an dubansa tai kana tace “Karka damu yanzu zan sami adaidaita, kaje kawai kar kayi rana kasan yanayin yanda hanya suka koma yanzu....”
Yana murmushi yake furta “Tsoro kike kar a sace miki ni....?”
Ta d’an fito da idanunta waje had’ida murmusawa kana tace “Nidai bance ba...”
“Toh idanba tsoro kike ba ki shigo nai dropping d’inki....”
Zata kuma magana yace “No more excuse shige muje....”Ya k’arashe yana mai bud’e mata frontseat
Saida ta d’an juya idnunta kafin ta k’arasa ta shige.... Wani sassanyar k’amshine da ya gaurayu da sanyin AC sukai mata sallama cikin motar tasa, wani ikon Allah tin jiya dataji Yayanta Ma’aruf da Mamy suna tattaunawa kan batunsu da Khalid d’in sai ta tsinci kanta tana mai tsananin jin nauyinsa, gaba d’aya saiji tai ta kasa sakewa cikin motar ma.... Shi kansa Khalid d’in ya kula da canjin nata, wannan kallon rainin da take masa sam yau batai masa ba saima avoiding k’wayar idanunsa da takeyi.... tsakiyar motar ta hangi had’edd’en cappuccino cikin disposable cup da blueberry cookies da alama breakfast d’insa kenan.... Bai bari ta d’aga idanunta ba yace “Bismillah...”
D’an tab’e baki tai kana tace “Aaa wannan ai saiku, ni ina wannan zai k’osheni, nasan iyakacin karin kumallon naka kenan...”
Khalid ya murmusa yana karyan kwana yake furta “Seems like kin fara sanin mijinki tun yanzu....”
Ai baikai aya ba ta kuwa watso masa muguwar kallon mai firgitasa... Ya kuma sakin murmushi yana mai ayynawa cikin ransa ai saidai ba Nabila ba... Khalid yaci gaba da fad’in “Bakida labarin Sameer da Mamy harmada Mamani sun bani...?”
Wannan karon kauda kai tai daga barin duban nasa had’ida tab’e baki kana tace “Ai basukeda alhakin badani ba, Abbah na ne kawai zai haka, kuma a iyakacin sanina aurenka da Yesmin ya kusa....”
Bai kuma cewa komai ba jin ta ambato Yesmin har saida ta d’an kaikaito da fuska ta dubesa, sai yau ta k’are masa kallo, ashe kullum kallon tsoro take masa.... Khalid yakai mak’ura wajen had’uwa, ba laifin Yesmin bane data nace masa, irin mutanen nan ne da duba d’aya zaka masu kaji sun shige ranka.... Kaman yasan dubansa take aiko yana juyowa suka had’a idanu, tai saurin d’auke idanunta daga barin dubansa, babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu har suka iso cikin babban jami’ar....
Yusrah da dandatson ‘yan ajinsu ana cike k’ofar lecture hall ko ba’ace ba isowar malami ake jira hamshak’iyar BMW d’in nasa tai parking, kowa sai santin motar yake ga kalan ja dama da d’aukan idanu....
Ta kama handle zata fice kenan tajiyo muryarsa yana fad’in “teddy bear zan tafi yak’in neman aurenmu kimin addu’a.....”
Juyowa tai tana dubansa sai kuma ta sadda idanunta k’asa sakamakon yanayin data hangi fuskar nasa ciki....
Kasa cewa komai tai har saida Khalid yace “Bakida abinda zakicemin ne...?”
A hankali ta furta “Toh ni mai zance....?”
K’uri ya mata gaba d’aya ta daburce kana yace “You pray for me, for us....”
Ta d’an dubesa harda wani jinjina mata kai alamun tabbatarwa....
Duban dandatson ‘yan ajinsu tai kana ta hango k’awarta Yusra daga can gefe tana duban motar tana murmushi kana tace “Em... Allah kaika lafiya, drive safe....” Ta kama marfin motar zata bud’e taji tak’i bud’uwa..... Juyowa tai tanai masa duban tuhuma...
Ya d’an d’aga giransa kana yace “What..?”
Shaye da mamaki take dubansa kana tace “Ka bud’e min na fice kafin malaminmu ya k’araso....”
Sai sannan ya saki murmushi kana yace “Oh Aw sorry na mance k’ofar nan ta sami matsala bata bud’ewa ta ciki saita waje... Wait barin bud’e miki....”
Nabilah ta bisa da kallo sanda ya fice ya zagayo bud’e mata marfin motar itada sam bataso ya fito ba balle a ganshi yana bud’e mata k’ofar mota....
Aiko mai motar har sai yafi kashe dandatson mutanen fiyeda motar kanta....
Kunya ya cika Nabilah sanda Khalid ya bud’e mata marfin mota, a d’arare ta fito don ko ba’a ce tasan illahirin mutanen dake wajen su suke kallo, Khalid ya rank’wafo saitin kunnenta kana yace “You take care, and kar na sake ganinki da wad’ancan yara mazan....”
Harara ta galla masa kana ta d’an saita kanta tace a hankali itama “Thanks for the ride, and safe trip...” Daga haka tasa kai ta shige kaman zata kifa don ji taima kaman k’afafunta hard’ewa suke.... Khalid ya bita da kallo har ta shige kafin ya koma motarsa ya wuce shima...
Aiko Nabila na k’arasowa Yussy ta janyo hannunta suka shige tana fad’in kalan burgewar da sukai itada Khalid....

***

Wajajen shabiyun rana ya masa a Kaduna, yana isowa gidan kai tsaye sashensa ya wuce kafin wanima yasan ya dawo gidan, Aiko Kubura ta hango giftawansa, ta saki bokatin da take shanya kana ta nufi sashen Ammi a guje tana rangad’a mata kira.... Siyama da tashinta kenan daga bacci ta sauk’o k’asa tana neman abin kari taci karoda Kubura tamkar wacce aka jefota....
“Ke ke meye haka.. Lafiya?” Siyama ta dakatar da Kubura....
Kubura na haki take nunida waje....
Siyama da takaici ya cikata tsaki tai kana tace “Mutanen nakine suka motsa kokuwa....?”
Kubura taci gaba da haki tamkar wacce abin gudu ya biyota kana tace “Aunty Siyama ya dawo....”
Siyama ta yatsina fuska kana tace “Shi wane....?”
Kubura tace “Saifu mana Aunty Siyama... amma fah shi kad’ai babu abokiyar tafiyarsa babyn dank’on da aka lik’a masa....”

Harara Siyama ta galla mata kana tace “Ke banson sakarcin banza....”
Kubura tace “Wllhi gaskiya nake fad‘I maki Aunty gayacan ya shige sashensa.....”
Siyama ta jinjina kai kana tace “Maza haura sama ki fad’iwa Ammi....”
Daga haka ta fice sashen Khalid kaman zata tashi sama...

Khalid yana k’ok’arin kwab’e riga da niyyan shiga watsa ruwa Siyama ta banko k’ofar d’akin ta shigo....
Fasa cire rigar yayi sai tsaki dayaja a hankali lokaci guda yake furta “The next time you coming into my room, would you bother to knock... Dear Sis...” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gabanta....
Siyama na huci furta “Kai yanzu abinda kayi ya maka daidai Khalid.... Rashin mutuncin da kayi ka kyauta kenan...?”
D’aga mata hannu yayi kana yace “Wait wait, hold your lectures Siyama, as you can see I just got home... Fice min a d’aki.....” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa...
Muryar Ammi ne daki dodon kunnuwarsa “Bazata fice ba, ka mareta kawai sai nasan ka cika....”Hannayensa dafe da kunkumi ya d’an kauda kai gefe yana k’ok’arin calming kansa.... Juyowa ya d’anyi kana yace “Ammi ina yini....”
Dakatarshi tai ta hanyar d’aga masa hannu kana tace “Bazan amsa ba... Cikakke, aidai kaji dad’i ka aikata abinda kakeso ka watsaman k’asa a idanu... Sai ka sanar dani da baka kai Yesmin d’in Abujan ba gidan uwar wa ka tafi....”
Karaf Siyama tace “Har sai kin tambaya Ammi, wajen watsetsiyar can ya tafi ya gama watsewa...”
Izuwa lokacin zuciyar Khalid ta gama tafarfasa, shi kad’ai sai murza hannunsa dake k’ok’arin kaima Siyama mari yake... Badon Allah ya kiyaye ba tabbas data kwashi tsaraban maruka....
“You watch your mouth....” Ya fad’i idanunsa akan Siyama wanda suka gama komawa jazir....
Ammi ta shiga tafe hannaye tana fad’in “Lallai na yarda basu barka haka ba.... Shin uwar mai suka jik’a suka baka Khalid.... Ka fad’a min... !!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya
Chapter 94 · 0% Book details