← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 198

Sashe 195

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Raihanah ta kifa kanta hawaye na gangaro mata, shin ta yaya zata mance halaccin Siyama a gareta, matar data bud’e mata k’ofofin alkhairai na gianta, matar data zamto sanadin cikan burinta da farin cikinta.... Tabbas Siyama ta cika matar kirki da ba kowata mace zata iya jarumta da sadaukarwan da tai ba.... Da ace bawa zai iya fatan cuta ya k’aura daga jikin wani d’an uwansa Bawan ya dawo kansa tabbas da tayi addu’a ciwon Siyama ya tashi daga kan Siyama ya dawo kanta.... Siyama ta cika abokiyar zama da ko wata mace zatai fatan dacewa da abokiyar zama irinta, Ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen na kuma gangaro mata... Mummy ce ta umarce Raihanah data ja Ijlaal zuwa d’an waje Ta lallasheta... Raihanah ta masa cikeda kulawa kana ta janyo hannun Ijlaal tana fad’in “Muje Princess, Aunty Siyama would get better in sha Allah...!”

Mummy Ta maidoda dubantaga a Sameer kana tace “Bazaka saka wani abu a cikinka ba Son... Ga fruits a nan ko shi bazaka tab’a ba...?”

Sameer ya girgiza kai yana fad’in “Mummy na k’oshi, I’m not hungry, Dr nake jira yazo muji sakamakon gwajin ya sanar damu wani stage ciwon yake... Mummy I can’t lose partner...Mummy I can’t lose Siyama...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya....
Mummy ta rungume kansa cikeda tausayinsu gaba d’aga hawaye na kuma gangaro mata...
A haka Ammi ta k’arasa ta dafe hannun Siyama guda tamkar zatai mata addu’a sai kuma kuka ya b’alle mata...
Allah sarki wannan kayan tausayi da yawa yake... Harta Mummy kasa lallashin Ammi tai dole ta k’yaleta tai kukanta... A haka su Daddy Aunty Daula Khalid da kuma Nabilah suka turo k’ofar d’akin suka shigo....

*Toh Mai Karatu mu had’u a shafin k’arshe na wannan dogon labari da ya d’aukemu dogon zango... Da izinin Allah a shafi na gaba kuma shafi na k’arshe zamuji yanda wannan labari zata kaya....*

*Taku har kullum Sameena Aleeyou😍🤝*

Sameena Aleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*_(2019)_*

*113*

K’ARSHE.....

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

D’aya bayan d’aya Dr d’in Ke dubansu kaman bazaice komai ba sai kuma ya buk’aci ganin Sameer da Daddy a can Office d’insa... Babu musu Sameer da Daddy suka take masa baya...
Suna isa Office d’in Sameer ya mik’e daga zaunen da sukai saman kujera yana fad’in “Talk... Kai magana Dr, tell me wani stage yake...? Talk mana... Ka min magana mana..!!”
Gaba d’aya ya kirice, kana ganinsa kasan a daburce yake dole ya baka tausayi.....
D’an dafa kafad’arsa Daddy yai kana yace “Take it easy Sameer, ka kwantar da hankalinka kaji...”
Duban Daddy kad’an Sameer yai ba tareda ya iya cewa komai ba, lokaci guda Dr AT(SHAK’UWA CE) ya sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya yana mai mik’awa Sameer file d’in Siyama gabansa sanin cewa Sameer d’inma likita ne....
Cikin rawar hannu Sameer Ke tab’a file d’in kaman wanda aka sanya masa shokin, lokaci guda ya ture file d’in ya d’ago kansa kad’an yana duban Daddy kana yace “Daddy I can’t, bazan iya karantawa ba... I just can’t...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Duban Dr AT da ya dafe kumatunsa da yatsarsa guda yana duban Sameer cikeda tausayawa Daddy yai kana yace “Dr please, just go ahead and explain everything.... Sanar damu matakin da ciwon nata yake...!”

AT ya jinjina kai a hankali kana yace “Alhaji, ciwon Siyama yana early stage ne, but a yanda takwarana likita Sameer ya susuce gaba d’aya hakan yasa na rasa ta yanda zan masa bayani.... Alhamdulillahi an gano da wuri, yanzu abinda ya kamata ai shine, zata undergoing therapy session kaman na zuwa watanni uku haka....”

Daddy ya jinjina kai yana duban Dr AT dake ci gaba da zayyano masa bayani.... Kana yace “Toh Dr idan anyi wannan therapy sessions d’in shikenan hakan na nufin an k’one ciwon...?”

Dr AT ya d’an girgiza kai yana mai kuma gyara zamansa saman kujerarsa kana yace “Hakan zai bamu dama ne to understand it’s behavior sannan kuma mu k’one k’arfin ciwon kafin yayi yad’o cikin jijiyoyin jini, and... Abu na gaba bamuda sauran zab’i da ya wuce mu cire mahaifar gaba d’aya....!”

Daddy da jikinsa yai sanyi sosai a hankali ya furta “Does that mean bazata tab’a haihuwa ba kenan....?”
AT ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an yana mai zare farar gilashi na k’arin k’arfin ganin daga idanunsa kana yaci gaba da fad’in “A halin yanzu ceton rayuwarta yafi komai mahimmanci... Chances na rayuwarta baida yawa dikda cewa musan rayuwa da mutuwa duka suna hannun Allah ne...”
Dafa hannun Daddy Sameer yai kana yace “Daddy lafiyar Siyama shine gaba da komai a halin yanzu... Ban damu ko zata haihu ko bazata haihu ba... It is her that I love Daddy...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Dafasa Daddy yai cikeda jin dad’in yanda yake k’aunar d’iyarsa, tausayinsu gaba d’aya ya kuma kama Daddy... Lokaci guda Daddy ke goge hawayen da ya mak’ale masa a ido yana d’an bubbuga kafad’an Sameer...

***
Bayan watanni uku akaima Siyama aiki kuma Alhamdulillahi anyi nasara.... Kwance take saman gadonta na marassa lafiya idanunta a lumshe sai sautin na’urorin bature dake tashi lokaci zuwa lokaci....

A hankalin ta soma Ware idanunta da sukai tsananin mata nauyi....Tar ta k’arashi bud’esu tana kallon pop dake bisa kanta... ta d’an kaikaito a hankali tana duban Sameer dako shakka babu a nan gefen nata ya kwana, hannunsa guda cikin nata, kansa kwance gefenta... Ta saki murmushi a hankali sanda siraran hawaye suka zubo mata....
“Partner...!” Ta fad’i da k’yar.... Bai tashi tashi ba, da alama baiji ba har saida ta d’an sake bud’e murya kad’an ta fad’i....”Partner..!!”
Kaman a mafarki haka ya sinkayo muryar nata, yai saurin ware idanunsa yana mai mik’ewa zaune.... Lokaci guda yake kuma rik’o hannun nata yana dubanta yake fad’in “Partner... You’re awake... Thank Goodness... You’re finally awake Partner...!!” Ya k’arashe yana mai kwantar da kansa saman kafad’arta kad’an hawaye na gangaro masa.... Jinjina masa kai take itama tana hawaye... Lokaci guda Sameer ya d’ago yana kuma dubanta had’ida shafa fuskarta yake fad’in “I thought I was going to lose you Partner.... Please don’t leave me kinji....!” Ya k’arashe yana mai sunbatar hannunta....
Murmushi ta sakar masa ba tareda ta iya furta komai ba, saima hannunta guda da takai saman cikinta tana shafawa a hankali.... K’walla suka kuma ciko idanunta, sanda suka gangaro Sameer yaji d’umin sauk’arsu saman hannayensu da ya had’e waje guda yana mai dafe fuskar nata da hannayen nasu.... D’agowa yai yana duban yanda hawayen Ke gangaro mata.....
Ya kuma matsowa cikeda kulawa yana fad’in “Partner.... Akwai yanda Ke maki ciwo ne... Tell me kinajin wani abu ne...?” Dik a d’an rikice yake maganar....
Girgiza masa kai tai a hankali kana tace “Partner this is the consequences of my actions, this is my punishment, I can’t bear a child....now I can never see my child... I can never give you a child partner...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka....
Kuma rik’o hannayenta Sameer yai yana fad’in “Don’t say that Partner... Godiya ma Allah ya kamata muyi da ya baki lafiya ya kuma tasheki... Ni Ke d’in nake so Siyama... Haihuwa kyautace Daga ubangiji ya baiwa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba dan komai ba sai dan ya jarabci bayinsa, wasu da lafiyar da komai bazasu haihu ba sabida Allah bai k’addari zasu haihun ba, wasu idan sun haihun ma yaran su zamto fitina a garesu ko wani abu mai kama da haka.... And one thing da ya zamto mana darasi a wannan rayuwar shine basai ka haifi d’a ya zamto Naka ba, just like me and my Mummy, mummy ba ita ta haifeni ba but I’m her son, sannan Mamani da Abbah... Mamani ba ita ta haifi Abbah ba but Abbah is her son.... So as you and Ijlaal, Ijlaaal is your daughter Siyama, she’s our first daughter...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai kuma k’arfafa mata gwiwa....

Murmushin itama tai tana mai jinjina masa kai wasu hawayen na kuma gangaro mata kana ta d’an d’aura fuskarta saman hannunsa tana mai sakin murmushi a hankalin wasu hawayen na kuma gangaro mata... A haka Ijlaal da Raihanah suka turo k’ofar suka shigo rik’eda basket na abinci...
Chapter 195 · 0% Book details