← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 198

Sashe 14

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fujajan ta gyara d’aurin k’irjinta ta nufo waje don dama d’abi’arta kenan zama da d’aurin k’irji musamman lokacin zafi....

“Wllhi wllhi babu matar da ta isa ta shigo har cikin gidan ubana ta zagi uwata... Wllhi kinyi kad’an fitsararrun yaranki ma sunyi kad’an...!!”

Kafin Sahariyya takai aya Nabilah ta katsetsada fad’in “Fitsara har ya wuce wacce aka baku ita a matsayin tarbiya ai ya b’aci.... Wllhi kikayi gigin zagin Aunty gabana zan shayar dake mamakin da baki tab’a shansa ba rayuwarki gaba d’aya....!”

Sahariyya ta daka tsalle tana tafe hannaye had’ida kururuwa tana mai gyara d’aurin k’irjinta, lokaci guda take furta “Lallai Nabilah kin rik’a ni kike zagi kanki tsaye don ubanki tamkar wata sa’arki ce ni...”

“Badai ubana ba wllhi yafi k’arfin ki zagesa dukda kuskuren da ta tafka ya d’auki d’iya mai daraja sukutum ya baiwa wannan lusarin Yayan naku....”

Haba nan fah Sahariyya tayo kan Nabilah tana huci tuni Aunty B ta tsare tsakaninsu suna gogan k’irji itada Sahariyya take fad’in “Kika kuskura kika tab’a d’iyata zakiyi kwanan guardroom billahillazi.... Bari kiji na fad’a miki ba wajenki nazo ba don ke ba sa’ar yita bace wajen uwarki nazo idan kuma ban sameta ba zan baki sak’o ki bata kuma ki tabbata sak’ona ya isa gareta k’aramar marar kunya....” Ta k’arashe tana mai hankad’e Sahariyya da tuni ta zube k’asa....

Tsoro da firgici suka cika Raihana tuni ta rungume Kausar suka rakub’e gefe guda....

Yunk’urin da Sahariyya tayo zata tashi sallama da karauniyar su Hajiya ya gauraye gidan, shigowarsu da kad’an Zulfah ma ta shigo a birkice....

Haba nan fah Sahariyya ta shiga runtuma kururuwa tana fad’in “Wayyo Hajiya wayyo Hajiyata taron dangi sukamin, wayyo k’ashin bayana wayyo k’afata....”

Haba ai kankace mai Hajiya tayi jifa da k’ullin k’auri data samo a unguwa tayo kan Aunty B gadan gadan Najah kuwa tayi kan ‘yar uwarta Sahariyya tana taimaka mata, tuni Zulfah da Nabilah suka tare Auntyn su dukan da Hajiya ta kawo ya sauk’a kan Zulfah...

Kausar da taga an kaiwa mahaifiyarta jibga da saida ya kusan aikata k’asa wani irin kuka ta cilla mai tsananin k’aran gaske... A tamanin Raihanah ta fice da ita daga gidan a guje sam batasan sun iso bakin kwalta ba...

Gaba d’aya hankalinsa naga wayarsa ko zata kira, driving yake yana duban wayar alamun yana jiran kiranta amma shiru, k’iris ya rage baibi kan budurwar dake rungume da k’aramar yarinya ba... Wani irin birki Sameer ya danna lokaci guda had’ida kifa kansa yana mai ambato Allah....

Cikeda fargaban abinda ka iya faruwa ya d’ago fuskansa yana duban gaban motar nasa, ganin bai gansu ba yasa shi saurin bud’e marfin motar ya fito yana lek’en ina suka shige wani lungun suka shige.... Komai ya faru in a flash, tabbas yasan ya kusan buge mutane guda biyu amma ga tsananin mamakinsa bai gansu ba kuma baiga wani gidan suka shige ba bai kumaga wani lungun suka shige ba....

Tsananin horn da ake masa daga bayansa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....

Cikin tsananin huci Hafiz ke d’ago hannu yana fad’in “Dallah Malam ka wani zo ka tare hanya mutane zasu wuce... Sai kuzo da manyan motocinku na k’arya kuna k’ababawa mutane a kwalta....”

Tunda ya soma magan Sameer ke dubansa yanajin wani abin na tsargar masa, bai iya amsa shi ba sai bud’e mota da yayi ya shige had’ida tada motar ya kaucewa Hafiz ya shige bai daina bambami yana fad’in titi bana uban kowa bane....

Kwanan da Hafiz ya shige Sameer ya dinga kallo yanajin kwanyarsa da zuciyarsa suna yunk’urin tuno masa wani abin.... A hankali ya dafe goshinsa yana ambaton Allah kafin yaja motar ya wuce gida....

***

Duk k’ok’arin Zulfah taga tayi k’ok’arin raba wannan fad’a abu yaci tura a haka Hafiz ya shigo ya taddasu, aiko Hajiya na ganinsa ta zube k’asa tana kururuwa tana fad’in zasu kasheta Zulfa’u da danginta zasu karta....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_

*14*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Abu kaman had’in baki nan fah yaran Hajiya gaba d’aya suka cafe suna rantse rantse da kururuwan cewa kashe masu uwa za’ayi....

Tsananin mamaki ya hana Aunty B da Nabilah furta komai sun zubawa sarautar Allah idanu suna ganin makirci irin wacce basu tab’a gani ba wajen Hajiya da d’iyoyinta...

Hajiya taci gaba da fad’in “Wllhi tallahi saika saketa, wllhi ka gama zama aure da wannan matsiyaciyar....”

Hafiz da k’irjinsa ya bada wani irin sauti ba tareda sanin dalili ba saurin k’arasawa ga Hajiya yayi kana yace “Amma dai Hajiya kinsan Alhaji ba bari zaiyi na saketa ba koh, kuma ai biyayya nake masa...”

Bai kai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Biyayya..? Toh biyayyar taci uwarta, wllhi saika saketa wannan wataran ba saidai azo a samu gawata ba donma dai Allah ya kiyaye su Sahariyya na nan da wayasan abinda zasumin, kana gani dai ga ‘yar uwarka Shariyya tsaban bugu saida suka kwab’e mata riga suka kuma targad’ata a hannu... Wllhi Hafiz saika saketa idanma ubanta bazai karb’eta tabi bola ko tabi titi don na tabbata wannan tsiyar babu mai kuma kwasanta.....”

Aunty B ce ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a kana tace “Ai idan baki mance ba ba bola ko titi kika d’aukota ba, a mutunce aka dank’a mata ku don babu tsiya a tattareda ita, sannan da wannan watsettsen auren shika sai yafi komai dad’i wajenmu barikiji na fad’a miki, idan har d’anki ya cika d’an halak yau Zulfa’u ta gama zaman aurensa, idan har ya haifu ya bata takardan sakinta kaman yanda kike ikirari....”

Hajiya banda tsuma bata komai sai faman bin Bara’atu da kallo kurum take, takai dubantaga Hafiz da yayi tsuru gefe yana duban Aunty B ta yanda take shiga bata nan take fita ba kana tace “Ka daiji da kunnuwarka koh, toh ka sakar masu tsiyarsu idanba so kake nai maka baki ba, wllhi saika saki Zulfa’u....”

Zulfah kuwa cikin kuka ta rik’e hannun Aunty B tana fad’in “Aunty don Allah kiyi hak’uri kada ki bari ya sakeni, Hajiya kuyi hak’uri don Allah wllhi hakan bazata sake faruwa ba In sha Allah....”

“Ke dalla can rufe min baki, shegen rashin zuciya yawa kare ya tand’e.. Toh ya sakekin mana sai mai, kin wani b’are bakiwa mutane kina kuka wllhi sai ya sakeki ya gani idan bakida gata....”

Hajiya zatai magana Hafiz yayi saurin katseta da fad’in “Inace matatace kuma nike zaman hak’urin nan da ita, kuma ai iyayenmu suka had’a wannan aure don haka gaskiya ni bazan saketa yanzu ba, ba yanzu nayi niyyan rabuwa da ita ba......”

Baikai aya ba Hajiya ta fashe da kuka had’ida kamo bakin zani tana fad’in Zulfa’u da danginta sun shanye mata d’a, tuni yasa kai zai fice Sahariyya da Nabilah sukayi saurin shan gabansa a guje, Sahariyya na fad’in “Haba Yaya haba kan wannan abar zaka bari tsinuwar Hajiya ya kamaka ga mata bila adadi a gari wllhi ka sakar masu d’iyarsu ka huta....”

Nabilah ta cafe da fad’in “Ahtoh nima dai hakan na gani Ya Hafiz duda dai ba shiri muke ba amma banso tsinuwar Hajiya ta kamaka ai dai gwara ka saki Addah Zulfah kowama ya huta....”

Batakai aya ba ya soma kwab’e takalman k’afafunsa alamun zai kai masu bugu gaba d’aya, a d’ari suka arce kowa tayi bayan ‘yan uwanta.....

Kasa fita yayi daga gidan don tuni Hajiya ta rufe k’ofa tana fad’in “Babu yanda zaije bai saki Zulfah ba, k’wafa kurum Hafiz yayi ya koma parlorn Hajiya yayi zamansa sai faman tsuma yake....

Hajiya zata bisa parlorn Zulfah tayi saurin fincikan hannunta daga rik’onda Aunty B ta mata ta tafi ta sha gaban Hajiya had’ida durk’usawa ya hawaye dake bin k’uncinta take fad’in “Hajiya don Allah kiyi hak’uri, wllhi idan Ya Hafiz ya sakeni Abbah tsinemin zaiyi, Hajiya kiyi hak’uri ki yafeni don Allah, idan dai Kausar ce na bar miki ita duniya da lahira amma dan Allah kada ki rabani da mijina, na rok’i arzikinki....”

Tsananin takaicin Zulfah da ya rufe Aunty B da Nabila tamkar film haka suke duban lamarin suna mamakin wane irin rashin zuciyane wannan....

Itako Hajiya shewa ta buga tana k’arema Zulfah duba daga yanda take duk’e tana hawaye kana tace “Wllhi idan ni na haifi Hafiz Zulfa’u, idan ni na shayar dashi na tsawon watanni ashirin wllhi sai ya baki takardan saki yanzu basai anjima ba idan yaso Abban naki ya tsine miki kibi ‘ya’yan kaji dama yaya balle kin sami tsinuwar mahaifi ai saidai ki soma bin bola, cikani dalla dangin tsiya mai farin sawu....” Ta k’arashe tana fizgan bakin zaninta daga rik’onda Zulfah ta mata....

Juyowa Zulfah tayi cikin hawaye tana duban Aunty B dake tsaye tamkar gunki tana dubanta tama rasa takaici ko tausayin Zulfah takeji....

Jiki a sanyaye Aunty B ta isa ta kamo Zulfah ta mik’ar da ita tsaye had’ida rungumarta take kuwa wani sabon kukan ya kufcewa Zulfah, Rihanah dake tsaye gefe can rungumeda Kausar sai hawayene ke gangaro mata....

Nabilah kuwa tab’e baki tai tana duban kowa da idanu...

Basukaiga barin gidan ba saiga Hajiya da mik’akk’iyar takarda hannunta tana faman washe baki had’ida tafiya irinta tak’ama...

Dungurin Zulfah tai da takardan kana tace “Alhamdulillahi d’ana ya rabu da alk’ak’ai yanzu kasuwancinsa zai bunk’asa yanzu zaiga cigaba a rayuwarsa yanzu al’amra zasu soma tafiya masa yanda yake so... Maza a k’ara gaba akai farin sawu wani wajen...” Ta k’arashe tana dank’a mata takardan...

Take Zulfah taji hawayenta sun k’ame, ta kuma juya takardan hannunta na tsananin rawa, takai dubantaga Hajiya da yaranta dake faman shewa Sahariyya da Naja’atu kana ta maido da dubanta ga Aunty B da Nabila....

“Aunty Ya Hafiz bai sakeni ba ki bari na shiga na tambayeshi naji daga bakinshi Dan Allah....”

Girgiza mata kai Aunty B tayi kana ta amshi takardan ta rik’ota tace “Muje, muje Zulfa’u....”

Zulfah na hawaye take fad’in “Aunty Kausar.....”

Juyawa Aunty B tai ta hangi Kausar dake rungume hannun Raihana kana ta tafi zata amsota... Ai kan ta isa Hajiya ta isa ta fizge yarinyar tana fad’in “Wa aje da ita ina bayan ga ubanta mahaifinta nan a raye, yo ai ko mutuwa yayi ba k’arewan aure ba babu yanda zataje nan shine gidansu.... Ku dai ku tattara tsamin k’afafunku ku fice tinda anyi maku abinda kukeso....”
Chapter 14 · 0% Book details