← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 198

Sashe 64

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakai dubansaga Khalid da kansa ke duk’e k’asa kana yace “Khalid inaso ka maido min da duk wani abinda na mallaka maka na jin dad’in rayuwa sannan ka tashi ka fice min daga gida kar ka dawo har sai ranar daka amince da buk’atarmu...”

Khalid ya d’ago a firgice yana duban mahaifinsa cikin rashin yarda da abinda kunnuwansa ke jiyo masa...
Baki na rawa yace “Daddy.....”

Dad ya kuma dakatar dashi da fad’in “Ka tashi ka fice mun a gida ka aje mabud’an section d’inka da na office d’inka.... I believe you can provide for yourself... Now..!!” Ya k’arashe cikin d’aga murya....

A hankali jiki babu laka ya mik’e ya nufi k’ofa.... Kubura dake lab’e bayan k’ofa hawaye suka shiga gangaro mata ji take kaman ta isa a guje ta rungumesa , ita kanta Yesmin d’in dake lab’e mab’oyarta sai taji babu dad’i ita ba haka taso ba bata zaci Daddy zai iya koran Khalid daga gidansa ba, ji tayi kaman ta ruga cikin parlorn tacewa Daddy duk abinda suka fad’i akan Nabila k’aryace.... Ta rintse idanunta tana hawaye... Tana ganin sanda Khalid ya dawo parlorn rik’esa keys a hannunsa da kuma suitcases d’insa biyedashi.... A hankali ya isa ya aje keys d’in gaban Daddy....
Siyama da Ammi mamaki ya cikasu ganin Khalid ya zab’i ya tafi akan yayi rantsuwa ya rabu da wancan yarinyar lallai da alama da gaske shanyesa tayi, jikin Ammi ya soma yin sanyin ganin Daddy da Khalid babu mai fasa k’udirinsa....

Har yasa kai zai juya Dad yace “Your car keys ajiyesu tinda suma ta dalilina ka samu....”
Khalid ya kuma duban mahaifinsa cikeda mamaki, lokaci guda ya sadda kai k’asa ya cirosu a aljihu ya aje saman center table... Dad ya kuma fad’in “Your master cards ajesu suma....”
A hankali Khalid ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya ciro wallet d’insa ya cire ATM cards d’insa ya ajesu saman table d’in....
Dad yace “Kar na sake ganinka k’ofar gidana balle k’ofar kampanina... Get out....!” Ya k’arashe yana mai nuna masa k’ofa....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*52*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

D’ago kai Khalid yai yana duban mahaifan nasa kaman zai magana sai kuma yai shiru baice komai ba, a hankali ya juya ya janye da suitcases d’insa, cikin wani irin yanayi yake d’aga k’afafunsa...
Zuciyar Ammi ta shiga tsinkewa ganin da gaske Khalid fita zai a gidan, tasan d’an nata da mugun zuciya amma batai zaton zai iya tsallake conditions d’in da mahaifinsa ya kafa masa ba ya fice....
Cikin inina takeceda mijin nata.... “Daddyn Siyaam don’t you think you’re going too far, kaga fah ficewa zaiyi, ina zaije shi, mai zaici..? Dan Allah kai hak’uri ka rangwanta masa....”

Wani mugun kallo Daddy ya watsa mata kana yace “Khalid baida muhalli a gidana until he’s learned his lessons...”

Ammi ta kuma kai dubantaga Khalid da har ya kusan ficewa daga parlorn, cikin sauri ta kuma duban mijin nata kana tace “Idan bazaka masa afuwa ba ko credit cards d’insa ka taimaka ka bashi mai zaici ina zaije....?”

A hasale Daddy ya kuma cewa “Nace maki har sai ya gane kuskurensa, babu abu guda a nan da zan basa sabida komai a nan ta dalilina ya samu, so idan har bazaiyi abinda ni nake so ba ya fice ya nema nasa da kansa yaji yanda ake nema da gumi....”

Duk maganganun da suke cak Khalid yai tsaye yana saurarensu zuciyarsa na kuma masa zafi... Cikin sauri yasa kai ya fice tamkar zai kifa k’asa....
Kubura tabi bayansa da kallo had’ida d’aura hannu bibbiyu aka tana kuka tana fad’in ta shiga uku...

Daddy bai kuma bin takan su Ammi da Siyama ba yai ficewarsa.... Harta Siyama saida ta sha jinin jikinta, ita kanta batai zaton abin zai kai nan ba, Daddy ya kori Khalid kuma Khalid baida niyyan janye ra’ayinsa, lallai abin ya girma....
Yesmin ne ta fito daga mab’oyarta a guje tana hawaye take fad’iwa Ammi “Aunt please talk to Daddy, he can’t send him away... Toh ina zaije shi.... Dan Allah ki masa magana”

Harara Ammi ta watsa mata ba tareda tace komai ba ta haye sama zuciyarta na mata zafi sosai.... Yesmin jiki a sanyaye ta maido da dubantaga Siyama murya har na rawa take fad’in “Cousin this can’t be, we must do something....”

D’an dubanta Siyama tai kana tace “Nima kaina abin ya dameni, amma karki damu don na tabbata Khalid bazai iya ba he would definitely give up, zai dawo ne sannan wannan shine kad’ai chance d’inki da zaku kasance tare, we should just keep an eye on Khalid, na tabbata Khalid baida abokin da ya wuce Baffah so definitely wajen Baffah zaje shi....”
Yesmin ta goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Shikenan hakan yayi, but I don’t want him to hate me even more...”

Siyama tace “Kedai nace miki ki bar komai hannu na a k’arashe Khalid baida zab’in da ya wuce ya yarda da duk wani condition da Dad ya kafa masa ciki kaw harda aurenki, so just chill kinji koh...” Ta k’arashe tana buga kafad’unta had’ida hayewa sama wajen mahaifiyarta....

Kubura ta fito daga mab’oyarta fuska duk hawaye yayinda ta hangi Yesmin itama fuskar tata jik’e yake da hawaye, nan sukai cirko cirko kowa tana aikawa juna muguwar kallo, tsuka Yesmin tai zata haye sama nan ta sinkayo muryar Kubura tana fad’in “Aikin banza wai harara a duhu, tusa kai babu k’warjini kuwa yawa ne, wllhi iska dai na wahal da mai kayan kara, mutum yace baya so baya so ko an tab’a soyayya dole ne... Billahillazi duk abinda ya samu Saifulllah mutum zaiji ne daga gareni....”

Cak Yesmin ta tsaya ta daina taka matakalan ta kaikaito shaye da mamaki tana duban Kubura, batasan sanda dariya ya kufce mata ba tace “I don’t have your time, you filthy made....!” Lokaci guda ta haye sama kaman zata tashi sama....

Kubura ta kuma yin k’wafa ta goge hawayenta ta fita ta nufi gate a guje ko zata hango Khalid.....

****

Ba shi ya koma gidan ba sai ana kiraye kirayen sallan isha....
Sawwama na zaune saman kujera tana kallon gidan talabijin na bollywood taji motsin shigowarsa, tana ganin sanda ya zube a veranda had’ida kifa kansa saman gwiwoyinsa, batace uffan ba bata tankasa ba saima tab’e baki da tai taci gaba da girgiza k’afafu d’aya bisa d’aya tana kallonta...
Tana jin sanda Hafiz ya busting cikin tsananin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare amma ko gizau Sawwama batai ba, saida aka kwashe kusan mintoci kaman biyar a haka kafin ta juya idanunta had’ida sakin gajeran tsuka ta mik’e ta isa gareshi tana faman tauna chewing gum tana wani jujjya idanu had’ida aika masa harara, ta kwashi dak’ik’ai a hakan kana ta d’an rank’wafo had’ida sassauta murya tace “Hafizi lafiya...? Meke faruwa na ganka haka cikin irin wannan tashin hankali...?”
A wahalce Hafiz ya d’ago yana dubanta, bai iya cewa komai ba sai rungumeta da yayi very tied yana kuma sakin kuka sosai tamkar wani k’aramin yaro, Sawwama ta rausayar idanu tana mai jin takaicin kukan nasa har cikin zuciyarta....
Cikin muryar kuka yake furta “Kausar Kausar babu Sawwama.... Kausar ta tafi ta barni.... Na rasa tilon d’iyata Sawwama....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai ban tausayi....
Cikin zuciyarta banda tsuka bata komai, a fili kuwa tsan tsan damuwa ta nuna ta shiga salallami da kururuwa wanda kai kace gaskiyane har cikin zuciyarta ne...
“Allah sarki Kausar yarinyar nan ashe ba mai zama bace, badon Allah ya k’addara hakan ba da tana nan abinta a nan, ai banci ta zamaba Hafizina bara na shirya na tafi makoki...” Ta ida maganar tana maici gaba kuruwa....
Bai iya furta koda kalma ba sai zubewa k’asa gijif da yayi yana mai kuma dafe kansa....
A haka ta d’auko mayafi ta taddashi nan zaune wajen yanda ta barsa, ta tab’e baki tana kuma aika masa harara, lokaci guda ta saki murmushin mugunta kana tace “Hafizina ai hak’uri ai mata addu’a ni na wuce don bai kamata ana can ana makoki ba ni ina nan.....”
Nan ma Hafiz bai iya tankata ba har tayi ficewarta, shi kad’ai yasan abinda yakeji cikin zuciyarsa saiko mahaliccinsa....
Sawwama tana ficewa ta tari mai adaidaita tana kiran Alhajinta a waya....

***

A can asibiti wajen Raihana kuwa Mamani tayi zaune ta rapka uban tagumi tana kallon yarinyar, tsananin tausayinta na kuma ratsa zuciyarta, k’aunar yarinyar take har cikin zuciyarta, Bata tab’a zaton zata k’aunaci d’aya daga cikin jikokinta mata irin hakan ba, sai gashi Allah ya jefa mata k’aunan Raihanah cikin zuciyarta.... Tana a haka Dr Awwab yai sallama ya shigo nurses biyu biyeda bayanshi...
Mamani tana ganinshi ta soma sakin murmushi tana fad’in “Datta an shigo...”
Awwab murmushi kwance saman fuskarsa yace “Eh Baaba ya jikin jikar taki...?”

Mamani fuska sake tace “Toh Alhamdulillahi zamuce an auna arziki tinda da ranta...”

Awwab yace “Hakane Baaba... Emm nace ko zaki d’an jiramu waje munaso za’ai dressing...”

Mamani tace “Na’am d’an nan za ai mai kace...”

Nurse guda dake kwance drip tace “Baaba ciwon jikar taki za’a wanke...”

Mamani ta yab’e baki tace “Yo na ganki a nan ai amma na tambayeshi....”
Nurse tace “Allah baki hak’uri Baaba...”

Mamani ta tareta da fad’in “Amin hak’urin ta kawomu yanda muke yanzu... Kajimin kilibibi irinta yaran zamani....”
Dr Awwab ya k’unshe dariyarsa ya shiga baiwa Mamani baki lokaci guda ya shiga janta da barkwanci da shike gwani ne wajen barkwancin....
“Hajiya Baaba mu k’arasa daga waje mu barsu suyi aikinsu, banida round muje nai miki hira...”
Mamani ta d’an dara cikeda jin dad’i don tuni ta sake da Awwab ko don barkwanci irin tasa....
Suna tafe take tambayarsa “Niko nace ina abokin aikin naka shi wancan likitan...”
Awwab yace “Aw Sameer, ai shi aikin nasa da safe ne shiyasa ya tafi....”
Mamani ta d’anyi shiru tana mai son tambayan Awwab abubuwa da dama gameda wancan likitan, haka kurum takejin babban al’amari a tattereda shi tun sanda ta soma arba dashi...

Awwab zai kuma fad’in Baaba tace kirani Mamani kaji d’an nan...
Yai murmushi yace toh Mamaninmu
***

KADUNA
Chapter 64 · 0% Book details