Sashe 82
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*INDA RAI*
_................DA RABO_
*66*
Chaaa sukaima Hajiya Haule akai suna tambayarta daga ina take... Haule ta kasa amsasu sai nishi da take saki da k’yar sabida k’ahon zuciyarta dake mata tsananin zogi... D’aya yace “K’ila ‘yar lek’en asirice ma ‘yan hizba tinda makircin ‘yan unguwa ya gagara shine aka turo wannan matar...”
Gaba d’aya suka amsada tabbas maiyuwa hakan ne... “Mai muke jira, mu lakad’a mata na jaki ta yanda gobe zata kuma zuwa wani wajen lek’en asiri ba....” Kan Hajiya ta sami zarafin magana suka shiga sauk’e mata duka ta ko ina, basaji basa gani bugu kurum suke mata har saida hankulansu Sawwama yaje wajen... Ga mamakin Sawwama mahaifiyar Hafiz ake bugu, suka tambayeta ko tasan matar ne, Sawwama tace atafau itama bata santa ba da gaske ‘yar lek’en asirice... Sawwama ta basu go ahead suci gaba da bugun Hajiya...
Hajiya na magagi da mak’yark’yata take furta “Sawwama nice fah... Nice uwar mijinki fah...”
Sawwama ta tinstire da dariya tace “Kuji makira Wai itace uwar mijina... Toh idanma uwar mijina ne sai mai... Ko shi mijin ne ba tsira zaiyi a nan ba balle ke... Wani mijin ma da tuni na basa rasidi... Idan baki sani ba toh ki sani ni Sawwama na gama auren wannan matsiyacin d’an naki mai farin k’afa maza a k’ara gaba....!”
Hajiya ta d’aura hannaye bibbiyu aka tana furta “Wayyo! Wayyo!! Na shiga uku ni Haule... Na d’ibo ruwan dafa kaina... Amma wannan yarinya ke ba ‘yar halas bace... Nayi danasanin aurenki da Hafiz yayi... Matsiyaciya dangin fir’auna a nono kika sh....” Batakai was aya ba taji sauk’ar lafiyayyar mari a k’uncinta... Ta zaro idanu waje tana duban wacce tai marin ba kowa bace illa sirkarta Sawwama... Sawwama na huci taci gaba da fad’in “Ke har kin isa ki zagi mahaifiyata... Kinyi kad’an, kinada sauran azuzuwa kafin ki k’araso yanda nake a bariki...” Ta dubi sauran ‘yantashan nata tace “Kuci gaba da bugunta muddin bata tashi ta nemi hanyar tsira ma kanta ba...”
Haba nan kakeji didim dim dim, sautin bugun dake sauk’a jikin Hajiya Haule... Gashi ihunka banza ne don sautin kid’a dake tashi bazai bari mutan unguwa su jiyo su ceceta ba... Haka Hajiya ta dinga birgima wajen d’ankwali gefe zani gefe sai bugunta suke tamkar an aikosu, itako sai birgima take wajen tana ihu tana neman agaji...
Da k’yar Hajiya Haule ta samu ta arce a guje zani a hannu d’ankwali a hannu ga fuskarta da sumarta duk k’asa ya b’ata yanda tasha bugu... Yara kuwa suna hangota sai su arce a guje suna mata wak’an mahaukaciya, masu adaidaita ma idan ta tare basa tsayuwa don cewa suke mai tab’in hankaline....
Wani adaidaita ne ya nufo yanda take, tai maza ta haye saman kwalta d’in tana saka masa hannaye bibbiyu alamun ya tsaya... Daga mai adaidaitan har passengers d’in dake ciki wasu mata guda biyu, salati suka shigayi suna ambaton Allah, su kansu basu yarda cewa wannan matar ba mahaukaciya bace...
Atika ta zaro idanu waje tana buga siddin mai adaidaitan tana fad’in “Malam kayiwa Allah ka kaucewa mahaukaciyar nan mu bar wajen nan kafin ta mana duka don wannan daga gani tsohuwar kamu ce...” Zulfah kuwa zaune kurum tai cikin adaidaitan tamkar gunki tana kallon ikon Allah...
Hajiya tasa k’arfinta gaba d’aya ta rik’o adaidaitan ganin yana neman zille mata shima, lokaci guda take furta “Kayi wa Allah bawan Allah... Ka ceceni ka fitar dani a unguwar nan kafin su kasheni... Wllhi ni ba mahaukaciya bace... Kaga can gidan mahaukatan na ciki....”
Zulfa’u da hawaye ke kwaranyo mata a hankali ta furta “Hajiya..!!”
Haule tai saurin d’ago idanu tana duban fasinjar data ambato sunanta, ba kowa bace illa Zulfa’u tsohuwar matar d’anta Hafiz wacce ta making rayuwarta impossible a baya ta kuma sanya d’anta ya mata sakin wulak’anci...
Mai adaidaita da Atika har suna had’e baki wajen cewa “Kin santa ne...?”
Zulfa’u na hawaye take jinjina kai... Kan suyi wani aune Hajiya Haule ta fad’i k’asa sumammiya....
Suka shiga karanto innalillahi Zulfa’u na fad’iwa Atika ta taimaka mata su sanya Hajiya cikin napep d’in... Haka suka kwasheta zuwa asibiti....
****
Hankali kwance yake cin abincinsa yaransa na kewaye dashi suna hira cikin jin dad’i da raha idan ka d’auke matarsa da takega yaran tamkar dodanniya... Muhibbah tai tsaye daga can bayan dining table d’in tana duban yanda maigidan nata da yaranta, duk wannan walwala dake tattaredasu tasan tana zuwa wajen shikenan ya k’are, sannan ta lura da yawan jin radio da mijinta keyi wanda a baya ba d’abi’arsa bane, kuma ga dukkan alamu yawan sauraron radio d’in da yakeyi shi ya dad’a bada gudummawa wajen canzasa don dai tasan ba wai zamanta a gidan bane kurum yake jefa Engr cikin wannan farin ciki da annashuwa, shin meye gaminsa da radio..? Shin wane shiri yake yawan sauraro da har ya canzasa haka...? Lallai kuwa dole tai yanda zatai ta nemo wad’annan amsoshi nata...
Lokaci guda tasa kai ta isa dining area d’in...
Tana k’arasowa yaran suka mik’e suna shirin barin wajen....
Cikeda masifa tace “Kai kai ku dawo nan... Ina zaku..? Oh Wato kunga dodo koh... Shine daga zuwata kun wani mik’e zaku shige koh.... Salon munafunci ace ina maku wani abin koh...”
Irfaan babban cikin nasu mai shekaru goma yace “Karatu zanje nayi, monday zamu fara exams...” Bai jira cewarta ba yaron ya shige...
Ita kaw ta biyun cewa tai itama karatu zataje Yayanta ya koya mata... K’aramar ta uku tace wajen ‘yan uwanta zata itama..... Muhibbah ta rakasu da mugun kallo har suka shige kafin ta maidoda dubantaga mijinta wanda yabi bayan yaran da kallo har suka haye sama...
Sai faman kumburi take ta janyo kujera zata zauna.. Lokaci guda shima ya ije spoon d’in dake hannunsa ya d’auki tissues paper ya share bakinsa kana ya mik’e daga kujerar... Muhibbah ta saki baki tana dubansa... Cikin sauri ta mik’e tasha gabansa fuska a narke tace “Kaima tashi zakai ka barni....?”
Bai sami zarafin bata amsa ba wayarsa ta d’auki ruri... Ya d’aga kiran yana mai barin wajen... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya shige... Lokaci guda taji zuciyarta na mata wani irin zafi, taji babu abinda take bid’a tamkar ta shak’i garin hodar ibilis don shine kawai zai mantar da ita bak’in cikin da take ciki a nata tunanin... Allah ka mamu maganin musiban shan kayan maye data addabi al’umma, baga yara ba baga manya ba, baga matan aure ba baga ‘yammata ba... Allah ka kawo mana sauk’i ka kare al’umman musulmi ameen....
***
Farkawan da Hajiya zatai a gadon asibiti ta tsinci kanta, take abubuwan da suka faru suka shiga dawowa kwanyarta, ta tuna cewa tabbas Zulfah ta gani, Zulfa’u dai data tsana tak’i jininta itace ta taimaka mata, don ko shakka babu Zulfah ce ta kawota asibitin nan... Wani irin kuka mai cikeda nadama da kaicon rayuwa ya kufcewa Hajiya... Tinda take a rayuwarta bata tab’a jin nadamar abubuwa da kurakuran data tafka a rayuarta irinta yau ba... Nurse guda ce ta lek’o jin sautin kuka na tashi daga d’akinda Hajiya take... Tai saurin k’arasawa tana tambayarta ko lafiya ko akwai wani ciwo da takeji ta cikin jikinta kuma... Inaa Hajiya bata amsata ba sai ma k’aran sautin kukanta da tayi, nurse ta fice kiran likita da sauri....
Haka likitan ma ba sanar dashi Hajiya tai ba sai faman zabga uban kuka take, da k’yar ta iya saita kanta ta shiga tambayar likita ina yarinyar data kawota nan... Dr yace “A Gaskiya Inaga ‘yanmatan sun tafi, amma guda d’ayar tace tana dawowa don ina tsammani ta tafi sanarda iyalanki halinda kike ciki ne, bata bar nan wajen ba har saida muka tabbatar mata cewa babu wani rauni mai tsanani jikinki kuma nan bada jimawa ba zaki farfad’o...”
Nan ma rintse idanu Hajiya tayi sabbin hawayen takaici da kaico suna zubo mata, duk irin cin mutunci da wulak’anci da cin zarafin da tayiwa Zulfa’u batai tsammanin ko gawarta Zulfah ta gani saman kwalta a tagayyare zata taimaka mata ba, sai gashi ta taimaketa daga hannun matar da take tunanin itace daidai ga d’anta... Hak’ik’a ba Zulfa’u kurum ta zalunta ba harda d’anta Hafiz dake kwance gadon asibiti rai kwaikwai mutu kwaikwai... Ga kuma d’iyarta Sahariyya dake kwance gida tana jinyar karaya... Hajiya Haule ta kuma rintse idanunta tana furta “Wata irin rayuwa na jefa ahalina ciki ni Haule...”
Tana a haka ne Baba Alhaji yayi sallama....
Shi kansa saida ya razana da ganin yanda halittar Haule ya sauya Wai donma ya tadda anyi treating ciwukan nata an kuma d’an kintsa jikin nata ba kaman yanda su Zulfah suka kawota ba...
Zama yai daga gefe yana k’are mata kallo kana yace “Haule ki sanar dani gaskiya, mai kuma kikayi wannan karon...?”
Da gefen idanu ta dubesa kana tace “Ban gane mai kuma nayi ba... Shin ko tambayata jikina bakai ba kawai sai ka hau tambayata mai kuma nayi... Oho wato gani sarkin aikata sharri koh....?”
Huci Baba Alhaji keyi kana yace “Sanin haline da yafi sanin kama....”
K’uri Haule ta masa kana tace “Mai kake nufi....?”
Matsowa kusanta ya kumayi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake furta “Ma’aruf nake nufi... Kinfi kowa sanin nasan komai...”
Kauda kanta gefe tai kana ta kuma maidoda dubanta garesa tace “Haba ai biri yayi kama da mutum, na jima ina kokonton cewa kasan bak’in sirri na, amma ka kasan yin komai akai sabida kaima akwai b’oyeyyen sirrinka, bacin haka da tuni ka koreni daga gidanka da kuma rayuwar ‘ya’yanka.... Fad’a min mai ya faru shekarun can....?”
Shiru Baba Alhaji yayi yana muzurai ba tareda ya furta komai ba... Lokaci guda Haule ta soma murmusawa kana tace “Aminiyar Sirri.....”
Ya d’ago da sauri yana dubanta...
Haule ta kuma jinjina kai tace “Tabbas d’aurin gindi ta samu daga gareka ta fantsamo cikin rayuwarmu da taimakonka... Idan ban b’ata a lissafi ba itace wakiliyarka a wannan bak’in aikin da muka aikata....”
Katseta yayi cikin daka tsawa “Haule..!!!!”