← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 198

Sashe 149

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibbah ta janyo hannun yaranta guda biyu suka nufi gidan sai wani yatsina fuska take tana mak’ale da hannayen yaranta, ko takan su Engr batabi ba.... Tana shiga cikin gidan Daula ta mik’e ta tarota tanai mata sannu da zuwa dashike sunsan juna, babu b’ata lokaci Daula ta shiga introducing Muhibbah masu Mamy su Ammah, su Zulfah dai suna daga can d’akin da aka sauk’i Zulfa’un, sun barbaje abinsu Atika nata faman basu dariya Nabilah na tayata saikace ba Amarya ba abinka da gwana wajen surutu... Ita dai Raihanah har yanzu bata dawo daidai ba tinanin abinda ya faru tsakaninta da Ya Ma’aruf a mota bai saketa ba, zata iya cewa har yanzu tana jin kaman sauk’an d’umin numfashinsa saman fuskanta sanda yazo zare mata seatbelt d’in... Allah ya gani dik yanda za’ai a komawa bazata yarda ta shiga gaban motarsa ba... Tana jin su Atika da Nabilah na kuma kwashewa Haule da Lami albarka Zulfa’u na kwab’arsu amma kaman ingizasu take....
Marliya silent crook ta shiga labarta masu yanda aka fasa auren Sahariyya da Ya Ma’aruf da irin kuka da ihun da Sahariyya ta dingayi da yanda su Amara suka tisata gaba da habaici da rashin daraja, dan Basma ta kawo mata labarin komai... Haba nan fah suka kuma samun abin yi sai dariya suke harda kwanciya saman gado, Nabilah tace inama tana wajen akai wannan drama a gidan Hajiya, Wayaga losers... Babun bad’inu, Sahariyya bata auri Ya Ma’aruf ba ga kuma Ya Hafiz bai Auri Zulfah ba.... Atika tace “Ai saidai ya hangomu cikin annakiyan BMW k’irar Jeep muna daga sama muna masa waving tsakaninmu dashi kenan...” Suka kuma tintsirewa da dariya yayinda Zulfah ta katsesu da fad’in “Ku dai haka babu kyau wllhi, never return evil with evil, kuyi masu fatan samun sauk’i cikin iftila’in da suka tsinci kansu ciki, duk fah yanda kukaje kukazo ‘yanuwanku ne kuma dik d’an adam ajizine... Babu fah wanda yafi k’arfin kuskure...”
Nabilah tace “Chapp! Ai duk kuskuren da za’a maimaitasa ba sau d’aya ba ba sau biyu ba sunansa ganganci da son zuciya... Wllhi abinda suka shuka ne suke girban kayansu... Yanzu ke har kin mance abinda wad’annan azzalumai suka maki keda Khausar... Wllhi ko tausayi basu bani ba, Aima basuga komai ba wllhi, sai Ya Hafiz da Addah Sahariyya sun koma ‘yan jagoran barawa Hajiya.....”
Atika tace “Gayamata Beels nawa shiyasa nake sonki...”
Zulfah ta tab’e baki tace “Da shike hali yazo d’aya ba ai dole ki sota...”
Atika ta kuma mik’ama Nabilah hannu suka tafe suna dariya...Zulfah dai girgiza kai kurum tai kana tace “Allah ya yaye maku..”
Atika na dariya tace “Ameen dai Akaramakiya matar Akr...” Tamakar wacce ta tuna wani abu haka ta kame bakinta da duka hanayenta biyu bata k’arasa ambato sunan Akram d’in ba....Zulfah ta aika mata harara kurum had’ida girgiza kai, idan kabi na Nabila da Atika sai su zautarka....A haka Aunty Bara’atu ta shigo ta taddasu ta sanar dasu maza su fito parlor suyi gaisuwa....
Kowaccensu ta mik’e tana neman mayafi, gaban Zulfah sai fad’uwa take yau zata gaisa da Mutallab....
Ganin ta fad’ad’a murmushinta yasa Atika janyota baya tai k’asa k’asa da murya tace “Nidai karkije kiyita Washe baki, kuma karkice Ke supporter d’insa ce ehe...”
Harara kurum Zulfah ta galla mata had’ida murmusawa....

Gaba d’aya suka nufo parlorn suka dudduk’a suna gaidasu d’aya bayan d’aya.... Sanda Nabilah take gaida Daddy ta saci kallon Khalid dake faman aika mata duban zamu gamu... Sai wani fuskewa yake shi a dole fushi yake da ita.... Daddy kaw da fari’a yaketa amsa masu gaisuwar nasu yana saka masu albarka.... Shiko Engr tinda ta fito idanunsa akanta suke... Ya kasa janyesu daga barin duban nata, dik yanda yake kissima kamanninta daga muryarta da yake saurare harta zarce masa nan, ita d’ince da gaske gabansa, shid’in ma’abocin sauraren muryarta ne, yau gata nan gabanshi cikin idanunshi masu muradin ganinta.... Tina cewa da yai ita d’in kuma matarsa ce sai ya saki wani sassanyar murmushi a hankali....K’uri yai mata yanda take sakin murmushin nan nata mai sanyaya zuciya ga duk wanda takema, he couldn’t believe this is happening.... Muhibbah tai masa k’uri tana karantarsa, ta kuma juyowa tana duban Zulfa’u dake magana da Aunty Daula kyakkyawan murmushi saman fuskarta, ita kanta saida ta raina kanta da ganin wannan mata, tayi kyau sosai cikin d’inki atampa ruwan shud’i had’ida mayafi ruwan shud’i shima, kana ganinta Kaga Amarya sabida wani annuri da fuskarta keyi... Muhibbah ta kuma duban Engr sai taga kaman kaya iri guda suka sa... Tana tsaka da tinanin wayarta ya d’auki ruri Shamzy ce mai kira, lokaci guda ta saci idanun jama’an dake wajen ta d’an fice tana amsa wayan....
Sai bayan ficewarta Zulfa’u ta waigo sashen da Engr yake, wani irin fad’uwan gaba ta tsinci kanta dashi... Gabanta yai wane irin bugawa ba tareda sanin dalili ba... Shid’inma ita yake duba, tai k’ok’arin saita kanta kana ta soma gaidashi... Saida ya saita kansa kafin ya iya amsa mata gaisuwan... Gani tai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta, gaba d’aya sai tajita a tsarge musamman sanin cewa da tai itafah matar aure ce yanzun.... K’arasowan yaransa ne ya ceci Zulfa’u daga irin duban da Engr Ma’aruf ke mata, gabanta sai faman bugawa yake da sauri da sauri harsaida ta tuhumi kanta meke faruwa da ita... Kiraye kirayen sallan zuhur da aka soma yasa mazan ficewa masallaci dan gabatar da nasu sallan, Irfaan na tsakaninsu rik’eda hannun Daddynsa suka nufi masallacin gaba d’ai...

A cikin gida kaw bayan wad’anda zasuyi sallah sun ida Mamy cewa tai dik su shige kitchen su taya Hajja shirya abinci... Aunty Daula tace “A’a Mamy akwai amare cikinsu da dai an bari nida sister ma taya Hajjah ta k’arashe tana duban Aunty B... Mamy tace “A’a, idan amaren ne fah...? Ince gidajen mazajensu zasu tafi... Maza maza kowa ta shige, division of labour Daula Ki d’ebe maki group d’in Zulfa’u Raihanah da Marliya kema Bara’atu Ki tasa naki team d’in gaba, Atika da Nabilah....”
Zulfah ta zaro ido tace “Mamy ai dai da baki had’e wad’annan fitinannun waje guda ba wllhi babu aikin da zasuyi...”
Mamy tace “Shisa na had’e su biyun k’ark’ashin Bara’atu daidansu....”
Gaba d’aya dan darawa sukai kafin Aunty B tace “An gama Hajiya Mamy....”
A parlor suka tadda matar Engr k’afafu d’aya bisa d’aya sai chatting d’inta take....
Aunty Daula tace “A’a Mummy Irfaan sorry mun barki Ke kad’ai mu k’arasa kitchen mana....”
D’an yatsina fuska tai kana tace “Um um Daula kinsan kitchen ba wajen zuwana da garaje bane, ni tafiya ma zanyi K’awata Shamzy na Emergency yanzu aka kirani, idan Excellency na yazo pls sai ki sanar dashi....” Ta k’arashe tana yafa mayafinta had’ida d’aukan handbag d’inta....
Nabilah da Atika yawa sun samu Tv haka suka bi matar nan da kallo, ko darajan sallama su Mamy basu samu ba balle Ya Abidah uwar mijin nata...Aunty B ta dubi Daula tace “Haka d’an uwan naki yake fama....”
Daula dai murmusawa kawai ta d’anyi kana tace “Ai a haka ta rage wasu abubuwan....”
Aunty B tace “Ni yaran ne ma abin tausayi....” Daula tace “Hm muje kedai na baki labari...”
Aiko babu musu Aunty B ta take mata baya....

Zulfah da k’arasowarta kenan ta taddasu Atika da Nabilah suna zancen matar Ya Ma’aruf Babba.... Girgiza kai kurum Zulfah tai kana tace “Ku dai ba’a rabaku da abin magana, yanzu itama wannan d’in daga had’uwarku rana guda har kun nemo makusarta, matarda ko saninta bakuyi ba... Ni dai ina fad’a maku ku dai yi a hankali kuma mata ne... Barin Ke Nabilah gidan sirakai zaki tafi, wllhi ku bi duniya a sannu....”
Nabilah ta b’ata fuska had’ida turo baki “Ni wllhi Addah Ke komai sai kince ba haka ba ba’ai dadai ba... Kuma bayan gaskiya kawai muke fad’i tinda ba shaidan zir mukai ba da idanunmu muka gani...”
Zulfah ta girgiza kai tace “Nidai bazan fasa fad’a maku gaskiya ba....”
Atika tace “Allah huci ran matar gwamna...!” Sai kuma tai saurin k’unshe bakinta sanda Zulfah ta kuma tambayarta “Matar wa kikace...?”
Atika na Washe baki tace “Matar aure nace....”
Zulfah tace “Ce miki akai banji abinda kika fad’i ba.. Wane gwamnan kike nufi...?” Batakaiga bata amsa ba Mamy ta katsesu da fad’in “Mai kuma kuka tsayayi wajen kunaji an fito daga nasallaci....” Ai bata kai aya ba suka shige gaba d’aya...
Sameer Mamy ta hanga ya shigo rik’eda hannun Irfaan d’an gidan Engr... Mamy ta tsaresa da tambayar ko ya lek’a Abbansa Kafin ya taho nan...
Sameer ya d’an numfasa yace “Mamy dama inaso muyi maganan...”
Mamy ta jinjina kai kana tace “Mu k’arasa daga can...”
Babu musu yabi bayan mahaifiyar tasa ya saki hannun Irfaan da tuni ya nufi wajen k’annensa da Kakarsu da suka santa a yau... Yaran sun baibayeta harda yaran Daula gaba d’aya sai zuba mata shirirta suke tana biyesu... Allah sarki rayuwa, wata irin rayuwa ce mai cikeda nishad’i Yaya Abidar Ke experiencing a halin yanzu wanda bata fatan abinda zai datse wannan Farin ciki da annashuwa da take ciki.... Hak’ik’a ba tarin dukiya bane jin dad’in rayuwa, Farin ciki da annashuwa wasu aba ne da dukiya bata iya sayensu...

Sosai Engr yasha mamaki sanda ya dawo ya tadda Wai Muhibbah ta tafi...
Zancen cewa k’awarta na emergency sam bai shiga kansa ba tinda tin suna mota ga ya fahimci take takenta...
A b’a gareni yaran kaw tafiyar mahaifiyar tasu baiko damesu ba saima cewa da sukai a barsu gidan Ammah su kwana koda d’aya ne, kakar tasu ma ta goyi bayan hakan dan tanason taji d’umin jikokinta wanda bata samu taji ba tsawon shekarun nan....

Wajajen la’asar Daddy yai masu sallama da niyyan washe gari idan Allah ya kai rai zai tafi Abuja akwai aikin da zai gudanar can kafin ya wuce Kaduna... Sukai sallama da matarsa Daula da yaransa dan cewa yai su bari kawai sa taho tareda Khalid da Nabilah tinda gobe take gama exams d’inta suma sai su samu time sosai da ‘yanuwansu.... Hakan sosai yaima Daula dad’i.... Bayan sun ida sallama da mijin nata Khalid ne ya mik’e yai masa rakiya zuwa mota....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*96*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 149 · 0% Book details