← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 198

Sashe 166

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lami ta kuma sab’a jaka kana tace “Zuwa nai na miki sallama zan koma can garin mahaifina, zaman garin nan ya gagareni Haule... Kunyar idanun Mariya da Alhaji Usman bazai barni naci gaba da zama k’ark’ashin alfarmarsu ba... Haule zan tafi can garin mahaifina na zauna a k’auyen tukuf dan ya fiyemin wala’alla na sami sauk’in azaban zogin da zuciyata kemin.... Ko jiya da naje gidan Kawu Liti a nan Unguwar rijiyar zaki Zo kiga yanda matarsa da yaransa sukai min cin kashi cewa bazasu amsheni gidansu ba dan labarin abinda mukai ya karad’e ko ina cikin gari... Koran k’are sukai min cewa na tattari makirci na na k’ara gaba ba a gidansu ba.. Kuma banga laifinsu ba Haule tabbas sunyi gaskiya...!”

Haule ta jinjina kai tana mai kuma matsan k’walla tace “Shikenan Lami Allah yaso saduwarmu... Ni kaina banida k’arfin halin fuskantar Mariya da mijinta....Dan bamu cancanci yafiya ba saidai rahamar Ubangiji....!” Lokaci guda suka rungume juna suna kukan nadama wanda basu tab’a irinsa ba...

****

KADUNA

Mamaki ya kuma cikasa, shida yazo shan cikin Sameer yaji ko yanda labarin accident d’in Daddyn Siyama sai ga wani babban surprise da ya tadda daga abokin nasa.... Lallai shi d’in mai sa’a ne... Yanzu kam ya gama samun makamin da zai datse auren Siyama da Sameer rabuwa ta har abada....

Sultan ya kuma gyara zama had’ida aje glass cup d’in dake hannunsa kana yace cikeda mamaki “A’a Wai Sameer haka abotan namu ya koma ne...? Yanzu da ace ban kiraka ba da bazan san Kana nan Kaduna ba kuma da bazan san Daddy ya dawo daga jinya ba, sannan ga babban abin mamaki Wai kaine da mata biyu Sameer... Come on Sameer mai zumunci ya zama ne dan Allah....?”

Sameer ya d’an murmusa kad’an yana mai aje cup d’in hannunsa saman center table shima kana yace “Sultan, everything happened so fast... Wllhi nima daka ganni ban zauna ba, kuma dan dai Mummy ta turo Raihanah ta kawo mana drinks ne.....”
“Da bazan san kayi aure ba ma...!” Sultan ya tari numfashin Sameer d’in da fad’in haka....

Sameer ya d’an murmusa kad’an kana yace “Abokina kenan... Dik yanda zan maka bayanin yanda abubuwa suka kasance bazaka fahimta ba... Amma tashi muje daga waje sai mu tattauna...!”

Sultan ya mik’e cikeda k’osawa yana fad’in “Then you make me understand... Dan ni gaba d’aya ka canza min Sameer, saikace ba abokina aminina da na sani ba... Koda shike kaje Kano kayi sabbin Family sabbin friends da kuma sabon wajen aiki dole ma ka mance ni...”

Gajeren murmushi Sameer ya kumayi, suna tafe yake ci gaba da fad’in “Kaima kasan ba haka bane Abokina... So stop being ridiculous...”
Sultan ya d’an murmusa had’ida sakale hannaye cikin aljihun wandonsa lokaci guda yake ci gaba da jefo tambayoyi na siyayasa ga abokin nasa wanda ya d’auki dukkan yardarsa ya basa... Cikin amsoshin Sameer d’in ya fahimci tabbas Siyama bata da wannan labari na k’arin auren Sameer, don koda yace masa Amarya ce tasa ya mance dashi sai ce masa yai batama tareba tukunna gaban Mummy take yanaso ya soma sanar da Siyama kafin su tare... Hakan yasa Sultan ayyanawa cewa Dama ta sameshi... Shi kad’ai sai sakin murmushin cin nasara yake...

***

Ita kaw Raihana gaba d’aya haka kurum taji ta tsani wannan abokin Ya Ma’aruf d’in dan taga sanda Mummy ya aikota kawo masu ruwa yanda ya kafeta da idanu, gaba d’aya sai taji ta tsanesa bai mata ba.... Suna kitchen ita da Mummy tana taya Mummy aikace aikace da shike Mummy dama chef ce mai zaman kanta dan a wajenta Sameer ya koyi mu’amala sosai da kitchen... Dan tinda suka taho Kaduna Mummy tai mata register a makarantar ta kama daga aikace aikacen kula da tsaftan gida da jiki gayu da girki dik Mummy koya matasu take tamkar wata d’iyarta gashi sosai Allah ya had’a jinin Raihanar da Mummy... Mummy ta k’udura a ranta cewa in sha Allahu sai ta gyarama Sameer d’inta matarsa tsaf ta yanda dik wasu abubuwa da ya rasa a aurensa na baya zai samesu yanzu... Hakan yasa taja Raihanar sosai jikinta dan ta sake da ita....

***

A can Abuja fah....?

Wani Sabon tashin hankali yanda Ammi ta dake ta rufe idanu saidai su tafi gidan Aunty Daula su zauna gaba d’aya, Aunty Hanne naci gaba da zigata cewa gwara suje can duk su tare waje d’aya ta gane ma idanunta yanda kud’ad’en mijinta Ke tafiya... Ammi kaw ta hau kan shawarin Aunty Hanne tace ata fau saidai su d’unguma gaba d’aya su tafi gidan Daula tinda mijinta dai shi ya sayi Gida dan haka babu Uban da ya isa ya hanata zama cikin gidan... Siyama tace tayi daidai hakan za’ai, Yesmin kaw ba k’aramin dad’i hakan yai mata ba dan ko babu komai Yesmin zata samu Ta saka idanu kan Nabilah da Khalid....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*102*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Da tsananin mamaki Khalid Ke duban mahaifiyar tasa, da gaske take gidan Aunty Daula zata tafi... Shin wannan wane irin musiba ne da yak’i ci yak’i cinyewa... A hankali ya soma girgiza kai hannayesa dafe da kunkuminsa yake duban Ammi da Siyama yanda sukai masa k’ebebe aka.... Lokaci guda Khalid ke furta “No Ammi... I won’t allow you to go there, idan san zama cikin mutane kuke ga gidan Aunty Hanne why not bazakuje....” Katsa tai da fad’in “Naga gidan Hanne na zab’i gidan nawa mijin ai.... Kai Khalid bari kaji na fad’a maka... Idan mutuwa kake kana tashi baka isa ka hani zuwa wannan gidan ba... Siyama shige muje....!”
Saurin tare gabanta yai yana fad’in “Ammi please don’t do this... Na rok’i arzikinki kar kije Ki d’aga masu hankali... Idan kinaso ni zan biku dik yanda zakuje but please Ki k’yalesu haka nan....”
Siyama dake faman danna masa mugun kallo tace “Wai Khalid wa Ammi kake dika wad’annan abubuwan... I can’t believe you are doing this to your very own mother... Khalid Wai anya kanaso kai albarka kuwa....?”

Da tsananin mamaki yake kaikaitowa yana mai duban Siyama... Ya karkato sosai yana dubanta kana yace “Really Siyama... What do you even know about albarka... Tell me Siyama, kin baiwa aurenki daraja..? Kin baiwa mijinki daraja...? Kin baiwa mahaifinki dake kwance daraja by disrespecting his own wife... Siyama is that what you call albarka.... Answer me wannan shine neman albarka a wajenki..!!!” Ya k’arashe cikin tsananin b’acin rai jijiyoyinsa na mimmik’ewa....
A zuciye Ammi tace “Khaliiiddd!!!!”
Bai daina kallon Siyama ba yana mai ci gaba da huci yake furta “No Ammi Ki k’yaleni na fad’a mata gaskiya for once in her life idan har ta rasa mai fad’i mata gaskiya ne....!” Bai kai aya ba sai sauk’an mari yaji a k’uncinsa.... Ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban Ammi datai marin tana sakin huci... Lokaci guda taci gaba da furta “Bani address d’in gidan kafin nai maka abinda yafi mari....!”
Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyar tasa yanda tana ganin gaskiya tana rufe idanunta... Tsawa ta kuma daka masa “Zaka bani ko sai na maka baki kabi daji....!!!”

Jiki a mace ya zaro wayarsa cikin aljihu ya rubuta mata address d’in had’ida mik’a mata... Ammi tace da Siyama “Maza amsa ki gani...”
Siyama na watsa masa harara ta finciki wayar had’ida forwarding address d’in zuwa nata wayar.... Ko tsayawa basa wayar hannu da hannu batai ba saima danna masa da tai cikin aljihunsa tana mai aika masa muguwar kallo... Ammi ta buga tsaki kana taceda Siyama “Shige muje Hanne suna jiranmu....”
Babu musu Siyama tabi bayan mahaifiyarta tana mai watsawa d’anuwanta Khalid mugun kallo...

Haka yanaji yana gani har suka b’ace masa bai saki k’uncinsa yana mamakin hali irin na Ammi ba, gaskiya sai yanzu ya kuma tabbatar da k’ok’arin Daddy tsawon shekarun nan da yai da ita a matsayin matarsa... Cikin wane irin yanayi ya nufi Intensive care unit... Ya shiga d’akin da Daddy ke kwance... K’uri ya masa daga nesa yana hangosa idanunsa a lumshe.. A hankali ya isa jikin gadon kana ya kai hannunsa saman na Daddy ya dafa... Saida ya cire nose mask d’in dake mak’ale fuskarsa kana ya soma fad’in “Daddy I’m sorry... But I don’t know if I can take this anymore.... I thought I was strong enough to face all this...But then na fahimci bazan iya ba... You need to get better Daddy... You need to get out of this place please Daddy... I can’t.... I’m sorry...!” Ya k’arashe yana mai kifa kansa saman hannun Daddy guda hawaye suna bin k’uncinsa... Sosai Khalid yake kuka mai ban tausai, saida yai mai isarsa kafin ya kumayi ma mahaifin nasa addu’a ya fice...

****

A can gidan Aunty Daula kaw, kasancewar basu jima da dawowa Daga asibitin ba yasa dik suna parlor bama su haura sama ba tukuna.... Jin k’aran doorbell yasa Nabilah saurin mik’ewa tana fad’in “I’ll get that...!” Dik a zatonta Khalid ne ya dawo.... Da tsananin mamakinta tsaye ta gansu carko carko sai faman cika suke suna yatsina fuska...
Yesmin ta bud’e murya tace “A bamu hanya mu wuce, masu gida sun k’araso....!” Tai maganar tana mai bangaje Nabilah da har lokacin kallon mamaki take binsu dashi...
Suka kuwa kutsa kai suka shigo cikin gidan daidai sanda AuntyB taji shirun Nabilah yai yawa ta k’araso k’ofan itama... Da mamaki take dubansu...
Aunty Hanne tace “What..! Ko korarmu za’ai.....?”

Ga tsananin mamakinsu murmushi sukaga AuntyB ta sakar masu kana ta soma fad’in “Aa Haba dai, ai nan gidanku ne... Nan ya kamata ku sauk’a dama... Ku shigo, ku shigo bismillah....” Ta k’arashe tana kuma basu hanya....
Tuni Aunty Bara’atu ta umarci Karimatu mai aikin Aunty Daula ta taya Kubura haurawa da suitcases d’insu Upstairs... Nabilah ma dai bata kuma zaman parlorn ba ta haye parlorn sama abinta...
Chapter 166 · 0% Book details