← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 198

Sashe 138

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mamani ta dubi Abbah tace “Alk’ali kada ka saurari matar nan... Na rok’i arzikinka kaji d’ahna....!” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo hannayensa....
Girgiza kai Abbah yake cikeda d’imauta lokaci guda yake furta “A’a Mamani.... Inaso naji abinda matar nan zatace....”
Juyowa yai yana duban Ya Abidah lokaci guda yake furta muna saurarenki....”
Ya Abidah ta jinjina kai kana taci gaba da fad’in “Banso kukaji wannan daga bakina ba, amma ku sani dole ce tasa zan amoda wannan Sirri da ya jima a rufe...”
K’irajai sukaci gaba da bugu.... A yayinda Ya Abidah taci gaba da fad’in “Kaman yanda kuka sani nida ‘yar uwata Mariya bama ga maciji, na mata iyaka da kaina, na kumayi iyaka ma kaina da ita da yanda take rayuwa dama duk wani wanda ya jib’inceta.... Saidai hakan baisa na kasa cika alk’awarinda na d’aukawa mahaifiyarmu ba cewa nid’in zan kula da ahalinmu bayan babu ita a raye.... A lokacinda Mariya tai aure taci kuka sosai na rashin ‘yaruwarta wacce take magajiyar mahaifiyarta a tareda ita... Kun sani Babbar Ya itace tamkar mahaifiya a lokacinda babu mahaifiya.. Ban halarci aurenta ba, haka ban taka yanda take ba... Kuma ita batada ikon takowa yanda nake.... Harta Bara’atu da Dumba duk saida nai masu iyaka da Mariya matuk’a sun zab’i zama dani... Basu d’auki hud’uba ta ba dikda cewa Sun nuna min sunyi na’am da hukuncin da na gindaya masu.... Hakan sosai yake ci masu tuwo a k’warya musamman Dumba wacce suka taso tareda Mariya tamkar k’awaye, a b’oye sukan fita su tafi gidan Mariya bada sani na ba, hakan yasa basu yanke alak’a kwata kwata da ita ba kaman yanda na umarcesu...

D’an fasalai taja kad’an kana taci gaba da fad’in “Wata rana kwanta bacci nai mafarki da mahaifiyarmu tana kuka tana cewa na kasa rik’e mata amanan zuri’arta... A mafarkin nima Ina kuka Ina sanar da ita cewa Mariya itace taci amanata ta salwantar da Zuri’armu... Mama Hajja bata daina kuka tana fad’in bazata tab’a yafe min ba.... Wannan mafarki ya d’aga min hankali sosai, yasa k’iyayyar ‘yaruwata ya kuma tasiri cikin zuciyata, Mama Hajjah ta rasu batasan cewa Mariya ta tsiratar da kanta ta k’yale Fatima da Ma’aruf ta kasa kula dasu kaman yanda ta d’auka min alk’awari.... Koda na sake bacci mafarki na sakeyi Mama Hajja na cemin kece Babba ki kula dasu.... Ranan nayi zurfi cikin tinani na kuma d’au alwashin kula da sauran ahalinmu da suka rage koda ace bazan iya duban idanun Mariya nace na yafeta ba... Koda ace bazan iya kasancewa da ita inuwa guda ba, domin kaw ganin fuskar Mariya ba komai yake haifar min ba face tina iftila’in dana fuskanta had’ida mutanen da na rasa dik ta dalilinta....
Wani rana na tsinci tataunawar Bara’atu da Dumba suna cewa zasu tafi su duba Mariya dan a kwanakin bata gane jikinta... Hankalina ya tashi sosai hakan yasa nabi bayansu a sace har naji dalilin rashin lafiyarta juna biyu gareta, a lokacin tana d’auke da jaririn cikin d’anta na fari.... Koda naji wannan batu gida na koma ba tareda sunsan cewa na fita naji tattaunawar su da Mariya ba... Koda na dawo gida bayan kwana biyu sai naji inason na san halinda ‘yaruwata Ke ciki.... Na d’auki mayafi nayi nad’i irinta buzaye ta yanda babu mai gane kamanni na, na fice na nufi gidan Mariya.... Nan ma lab’ewa nai ina hangota daga tsakar gida tana gudanar da aikace aikacenta.... Shigarta d’aki da wuya kishiyarta Lami ta fito tana ‘yan waige waige tamkar maras gaskiya, ni kuma koda naga haka jikina sai ya bani akwai abinda wannan matar take k’ullawa, bansan mijin Mariya ya k’ara aure ba dik a tinanina Mariya ita kad’aice ashe mahaifiyarka ta tilasta maka auren Lami bayan Mariya ta shafe shekara guda tak a gidanka babu koda b’atan wata...”
Abbah ya jinjina kai cikeda al’ajabi domin kaw anyi haka, Mamani ita ta tilasta masa yima Mariya kishiya dan kawai ta shekara gidan miji babu juna......
Ya Abida taci gaba da fad’in “Hakan yasa mafarkin da nai da Mama Hajjah ya shiga dawowa kwanyata cewa na kula da ahalinmu.... Ana a haka naga Haule matar Alhaji d’an uwanka ta fito daga d’akin Lami suna k’usk’us suna cewa ta shige d’aki mu cika aiki.. Shegiya mai shegen munafunci da iyayi ita a dole ga matar so.... Malam yace wannan biso idan muka bisne a k’ofar d’akinta hardai yana cikin k’asa bai fito ba toh kuwa tabbas bazata haife abinda Ke cikinta ba saidai ya mutu a cikin cikinta amma bazai tab’a fitowa duniya ba kaman yanda wannan laya yake bisne a k’ofar d’akinta... Suka kuma sakin shewa had’ida tafe hannaye a hankali.... Lami taceda Haule maza ta fito tai mata rakiya kafin wani ya gansu... Jin haka yasa na kuma b’oyewa har suka fice... Naga wajen da sukai bison jikin d’akin Mariya, daga nan fitowa nai ina k’ok’arin ficewa a sad’ad’e na b’ata hanya... Toh fah a nan ne na kuma karo da wani tashin hankalin wanda ya tabbatar min cewa tabbas Rayuwar Mariya na cikin had’ari babba bama ita kad’ai ba harda kai Usman da jairinku dake cikin Mariya... Alhaji d’an uwanka da matarda ka girma ka santa a matsayin mahaifiyarka su na hango suna tattaunawa wata muhimmiyar magana da alama basuso kowa yaji kuma shakka babu naji sun ambaci Mariya da mijinta...Jikin yai sanyi sosai da ganin irin rayuwar da ‘yaruwata Ke ciki... A haka na koma gida Ina tinanin al’amarin... Washe gari na kuma b’adda kama ba tareda sanin kowa naje na toni wannan laya na canza da wata layar....”

Jikin Aunty Lami yaci gaba da tsuma maganar Malam ya fito cewa ABU A DUHU, dama ya sanar dasu muddin aka samu tangard’a wajen bisne wannan layar toh fah za’a haifo cikin kuma itama Mariya bazata mutu ba, sannan dik wani shirin da zasuyi bayan wannan haske bazai tab’a bayyana masu ba, sunyita cin karo da Abu a duhu, Wato ashe dai wannan mata ita ta toni wancan layar tasu... Muryar Ya Abidah ta sinkayo yanda taci gaba da fad’in “Koda nazo fitowa a sace na kuma cin karo da Mamani da kuma Baba Alhaji suna tattaunawa wannan karon tamkar shi yake tsoratar da ita, da alama D’an nata yasan wani Sirri nata da bataso kowa ya sani... Lab’ab’awa nai na saurari abinda suke fad’i wanda yai matuk’ar bani al’ajabi

Mamani rok’on Alhaji take tana fad’in “Alhaji ka bar zancen nan a nan Usman bazai tab’a sanin ba nice na haifesa ba domin kaw mahaifiyarsa ta jima da rasuwa kuma shid’in d’ah na ne....”
Alhaji ya kuma b’allawa Mamani harara kana yace “Kin jima kina ci mun fuska akan Usman, ni ne d’anki na asali amma kin d’auki soyayyar duniya kin basa, gabaki d’aya dukanmu ‘ya’yanki babu wanda kike masa soyayyar da kikewa Usman... Yanzu tinda matarsa ta sami juna biyu hankalinki ya kuma karkata kan Usman da iyalinsa...”
A hasale Mamani tace dashi “Toh naga kai dik matar daka aura sai wannan jarabebbiyar matar taka ta koreta... Ni ba matar Usman nake so ba jikana dake cikinta nake so zan kuma bata dik wani kulawa da take buk’ata muddin jikana na cikin jikinta...”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Ni kuma na miki alk’awarin koda an haife wannan ciki sai na salwantar dashi, kuma baki isa kiceda Usman komai ba, dan wllhi kinji na rantse idan har kikai yanda yasan inada alhakin b’acewar d’ansa toh sai na tona miki asiri sai na sanar dashi cewa mahaifiyarsa ta jima da mutuwa kuma kece silan mutuwar ta... Bazai yuwu Usman yafini nasara a rayuwa ba....”
Ya Abidah ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Ga tsananin mamakina kuka naga Mamani tanayi tana rok’on d’an nata kada ya tab’a sanar da Usman cewa ba ita ta haifesa ba domin kaw mutuwa zatayi tabbas idan ta rasa soyayyan d’anta Usman.... Tabbas basuyi zaman dad’i da mahaifiyarsa ba amma tana jin k’aunar d’an data rasu ta bari tamkar ita ta haifesa.... Sannan k’annensu gaba d’aya sunfi k’aunan Usman samada Babban Yayansu Alhaji, Usman ya zamto tamkar uba a gidan tamkar shine magajin Alhaji Mahmood Mailafiya, girma soyayya da komai mashi ake badawa....”

Goggo Mairo ta Kazaure dake tsananin kuka ita ta katse Ya Abida da fad’in “Mamani dama D’an Yaya Hurera ya rayu bai mutu ba kaman yanda aka sanar damu dashi da ita duk sun mace... Shin dama naki d’an shine ya mutu... Innalillahi wa innalillahi raji’un...!!!”

Sabbin kuka ya ya kaure yayinda Mamani ta kasa d’ago fuskarta sai hawaye masu tsananin d’umi dake gangaro mata....
Chapter 138 · 0% Book details