← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 198

Sashe 50

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai Nabilah tai tamkar Aunty B d’in na ganinta kana tace “A’a Aunty banjin itace domin kaw ita da Hajiya takan kirata nafi kyautata zaton watace daban sannan duk yanda akai su ukun sunyi tarayya wajen ganin bayan Yayana Ma’aruf.... Amma whoever she is sai na bincikota....”

Aunty ta fuzar da iska tana mai ci gaba da fad’in “Don’t forget you’ve my support, You can always count on my support... Zan taimaka maki wajen binciko Aminiyar Sirri...”

Nabilah tai mata godiya kana sukai sallama Aunty B tana mai gargad’inta kada tayi mahaifiyarta taji wannan batu domin ko shakka babu d’aga mata hankali zaiyi ya d’ago mata tsohon mik’in dake cikin zuciyarta...

*SameenaAleeyou(Mrs💖)📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

*40*

Abbah da Sameer zaune a parlorn suna cin abinci saman darduma, sosai Abbah yake kula da d’abi’unsa wanda suke matuk’ar kama da nashi musamman a lokacin da yake matashi kaman Sameer d’in, yana son tambayar Sameer wasu abubuwan amma saidai baisan ta yanda zai soma ba, baisan ta yaya zai soma jefo masa tambayoyinsa masu wuyan fasaltuwa ba, a b’angaren Sameer ma sosai yake jin abubuwa da dama gameda mutumin saidai shima baisan ta ina zai soma ba, Mummy ita kad’ai zata warware masa sark’ak’iyar da ya tsinci kansa ciki... Idan suka had’a idanu da Abbah saidai kaga ya sakar masa murmushi mai sanyin gaske a yayinda shi Sameer d’in sai ya sami kansa yana mai sadda idanu k’asa...

Sallaman da akai ne ya sanyasu maida hankulansu zuwaga k’ofar bakunansu na mai amsa sallaman ba kowa bane illa Baba Alhaji Yayan Abbah...
Abbah ya fad’ad’a murmushinsa yana mai fad’in “A’ah Yaya kaine tafe, shigo k’araso mana, bisimillah...”
Ya k’arashe yana mai nuna masa wajen zama....

Yanayin fuskar Yayan nasa ya tabbatar masa akwai wani abin a k’asa don gaba d’aya babu walwala tattareda Baba Alhaji...

Sameer ya risina ya gaidashi ya amsa sama sama, Abbah na mik’a masa hannu alamun suyi masabaha Baba Alhaji yace “Usman ina Raihanah....?”

Shiru Abbah yayi yana tunanin wacece ma Raihanah tinda ba wai Hajiya na barinta ta fita bane...
Shiko Sameer sunan sounds familiar to him, yanata tunanin ina yasan sunan...

“Tambayarka nake ina d’iyata Raihanah..? Na dawo gida Haule ta sanar dani Mamani ta d’aukota ta taho da ita nan... Ce maka akai na gaza rik’onta ne ko mai..? Mahaifiyar tamu ma da kakeji kaike rik’eda ita sabida dai tafi nuna maka soyayya ne shiyasa take zaune gidanka, ka yankawa k’annenmu filaye cikin gidanka ka kashe masu zukata duk don ace kaiga gwani a dangi koh... Toh bada d’iyata ba ni zan iya rik’on kayana sam bazan yarda kaga gazawata ba...”

Tinda ya soma magana kan Abbah ke k’asa shiko Sameer jiki a sanyaye ya mik’e yana neman had’o kalmomin da zai masu sallama dasu tinda ya lura sauraren conversations d’insu sam ba huruminsa bane....
Kaman wani munafuki haka ya fice yana k’ok’arin saita takalmansa, saidai fitowarsa kenan sukai caraf Mamani rik’eda hannu Raiha sai balbala masifa take sun nufo sashen Abbah...
Gaban Raihanah ya yanke ya fad’i ganin fuskar mutumin da bazata tab’a mance taimakonsa a gareta ba nan gabanta, shima d’in cak ya tsaya yana dubanta domin kuwa tsaf ya ganeta, dama tanada relation da Abbah, toh kodai wancan mutumin shine mahaifinta, idan bai mance ba har k’ok’arin neman mahaifinta yayi don ya sanar dashi kalan wahala da d’iyarsa ke sha hannun matarsa, idan kaw Raihanah ta dawo nan gidan k’anin mahaifinta ne hakan sai yafi masa dad’i... Ya saki murmushi shi kad’ai kafin ta sami zarafin gaishesa fit ya b’ace a wajen... Tai wani sororo da ita don Mamani kam ma ko kulada mutum batai ba, abinka da idanun girma ga uwar masifa da take faman juyewa...

“Ke shige muje nace ayita a rubuce cewa bazaki koma gaban Haule ba...” Ta k’arashe tana zungurin Raihanah da sandar hannunta, Rihanah data dawo daga duniyar tunani tai wuf ta shiga bin bayan Mamani...

Sameer na fitowa suka had’uda Mamy wacce ta fito kitchen, a karo na biyu da ya kuma had’uwa da matar wacce yakejin wani babban al’amari gameda ita, kasa d’auke idanunta daga barin dubansa tai murmushi bai gushe saman fuskarta ba, Sameer ne yai k’ok’arin saita kansa ya soma gaidata...
Mamy tai saurin katseshi da fad’in “A’a daga waje kuma k’araso ciki mana....”
Ba abin yace mata a’a ba don sosai yake tsintar kansa da jin nauyin matar...
Yana d’an sosa k’eya yake fad’in “Toh Hajiya na gode....”
Dad’i kaman yakar Mamy ta shiga doka kirawa Nabilah da Marliya...
Duk wannan abu a idanun Aunty Lami dake lab’e akayisu, cikinta ya bada wani irin k’ara kaman mai shirin sakin zawo...
Ta dafe hannaye biyu a k’irji tana fad’in “Oh na shige na shiga uku ni Lami kullum k’ara kusanci suke.....” Jiki har na rawa ta koma sashenta ta rarumi mayafi ta fice fuuu...
Nabilah dake lab’e tana duban Aunty Lami yanda take lek’en Mamy da wannan mutumi sosai abin ya bata mamaki, toh wannan d’in wayene sannan meyasa Aunty Lami ke lek’ensa.... Kiranda Mamy ke mata ya sanya batabi Aunty Lami d’in ba don ganin k’anda ta nufa daga ganin wannan mutumi da kwanaki ta ganshi parlorn Abbah, tanason sanin alak’arsa da gidansu....

***
Baba Alhaji na hango Raiha ya mik’e yana sab’a babbar riga yake fad’in “Ke shige mu tafi gida....”
Bai kai aya ba Mamani da ta k’arashe dogorowa da sandarta tace “Bazata tafi ba, nace bazata bika ba.... Ai bansan ka zama shanyayye har haka ba, bansan Haule har haka ta shanyeka ba, auho ta bika ku tafi ku sabautar da ita kaman yanda kuka sabautar da Zulfa’u koh....?”

Gaban Abbah ya yanke ya fad’i jin an ambato d’iyarsa Zulfa’u...
Saurin d’ago kai yai yana duban Mamani da Baba Alhaji kana yace “Mamani mai kike nufi... Ina Zulfa’u... Shin ba auren Hafiz take ba....?”

Lokaci guda Mamani ta saki kuka tana tattaro bakin zani take fad’in “Manu ka yafeni, ka yafeni tsanar Zulfa’u da nai a baya... Haule da d’anta sun sabautar da Zulfa’u ta shiga duniya babu wanda yasan k’anda take, Hafizu ya saki Zulfa’u ya auro Ahalil kitabi... Wayyo ni Halimatu kaicona...

Tinda ta soma magana k’afafun Abbah suka gaza d’aukarsa, tabbas idan akwai babban mai laifi toh fah shine, shine ya tilastawa Zulfa’u auren Hafiz dukda cewa ba sonshi take ba sannan ya mata baki cewa idan ta kashe aurenta saidai ta nemi wani uban bashi ba kuma kadata kuskura ta dawo masa gida daidai da rana guda bai tab’a tuntub’ar yaji wani irin zaman aure d’iyarsa keyi ba, bai tab’a bata dama ta kawo kokenta wajen mahaifinta ba, a koda yaushe Hafiz ne yayi daidai a idanunsa... Shin wane irin mahaifi ne shi, anya hakkin Zulfa’u zai barsa a rayuwa, abu mai kaman wuya kaga hawaye idanun Abbah sai gashi k’walla sun ciko idanun nasa....
Gijif ya zame cikin kujera yana mai furta “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un....” Kalma bayan kalma a hankali can k’asar mak’oshinsa....

“ Kanajina Sarki wllhi Raihanah bazata koma gidanka ba kuma d’anka sai ya nemomin jikata yanda ta shiga ta fita idan kuma ba haka ba kotu ta rabamu....”
Marliya da shigowarta parlorn kenan taji ana zancen Addarta Zulfah ta b’ace don tunda taji Raiha na gidan ta nufi sashen Mamani ta tarar basu a sashen shine ta nufo parlorn Abbah don taji muryar Mamani a nan....
Take idanun Marliya suka kawo ruwa, gabanta yaci gaba da bugawa cikin wane irin kuka ta fice a parlorn ta nufi sashen Mamy tana kuka tana k’wala mata kira...

Daga Mamy har Nabilah da Sameer gaba d’aya mik’ewa sukai suna tambayar Marliya lafiya...
Cikin tsananin kuka Marliya ta fad’a jikin Mamy tana shessheka take fad’in “Mamy Addah Zulfah....!”

Mamy da gabanta ya yanke ya fad’i saurin d’ago Marliya tai tana tambayarta “Addah Zulfah...? Mai ya sami Zulfa’un... Marliya ki sanar dani mai ya sami d’iyata....

Ai Marliya bata kai ga bata amsa ba Raihanah ta shigo a guje tana kuka sosai take fad’in “Abbah ne... Abbah ya fad’i bai numfashi...”

Mamy tama rasa wanne zatai, ai a d’ari Sameer ya fice ya koma sashen Abbah suka d’unguma gaba d’aya kowa bai cikin hayyacinsa sai koke koke da salati kakeji..
Kankace mai Sameer ya shiga k’ok’arin ceto rayuwar Abbah da yai wata irin sumewa dafe da k’irjinsa...
Mamani hannu aka take kuka tana fad’in Baba Alhaji ya fice mata bata koh k’aunar ganinsa, tuni ya cikawa babbar rigarsa iska ya fice yana mai kuma jaddada masu sai ya dawo ya d’auki d’iyarsa....
Dole Sameer ya saka Abbah a mota Mamy na rik’edashi suka fice, suma su Nabilah tuni suka tari adaidaita sukabi bayansu cikin kuka shab’e shab’e....

SameenAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*41*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Nan da nan babu b’ata lokaci aka soma duba Abbah, daidai da dak’ik’a Sameer bai bar kan Abbah ba taredashi ake komai sanin cewa shima likitan ne....
Su Mamani dasu Nabilah an rasa mai dannan wani cikinsu sai kuka suke shab’e shab’e, dama dama ma Mamy itace mai d’an k’arfin halin juriya da karanto addu’o’i dukda cewa abubuwa da dama ne sukai mata caa cikin zuciyarta, ga Abbah kwance rai a hannun Allah ga kuma maganar b’acewar d’iyarta Zulfa’u, duk juriya da jarumtaka irinta Mamy saida k’walla suka shiga gangaro mata cikin zuciyarta take furta “Ya Allah ka dubemu ya Allah kar ka d’auki mijina yanzu, Allah ka d’aga kafad’unshi ya Allah... Allah kar ka bari bak’in tarihin da ya auku shekaru talatin baya ya maimaita kansa, duk yanda Zulfa’u take ka bayyana mana ita.... Bazan iya jure rashin wata d’iya ba....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka wanda yasa Marliya da Nabilah k’arasowa suka rungume mahaifiyarsu suna kukan tare...

Kan kace mai asibiti ya cika da dangi idan ka d’auke zuri’an Baba Alhaji wanda su kad’aine basu a wajen, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai Sameer ya fito daga d’akin da Abbah yake, gaba d’aya suka mik’e suna tambayarsa “Dr wane hali yake ciki...?”
Chapter 50 · 0% Book details