← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 198

Sashe 62

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta saki kana tace “Oh d’azu Ammi tai waya Dad yana hanya gobe, kasan ya jima baya k’asa so ya kamata naje mu tarbeshi, we are leaving to Kaduna first thing tomorrow morning nida Yesmin....”

“With whose permission...?” Yai maganar fuska babu alamun wasa yana mai zura mata idanu...

Kallo ta bisa dashi kana tace “Sameer ce maka nayi fah Ammi ce ta kirani so kake nace mata bazanzo ba, kar ka mance she’s my mother....”

K’uri kurum ya mata kana yasa kai ya shige yana mai rage agogon hannunsa yake fad’in “You’re not going anywhere....” Bai jira cewarta ba yasa kai ya shige bathroom...

Tirk’ashi! Kallo tabisa dashi har ya shige tana mai tsananin mamakin yanda gaba d’aya Sameer ya canza mata, da a bayane basai ta tambaya ba duk abinda tayi daidai ne amma yanzu wai har order da doka yake kafa mata, toh ko dai ya daina sonta ne...? Ta tambayi kanta, babu amsa, cikin sauri ta lalumi wayarta ta fice kiran Laila domin neman shawari....

***

Aunty Lami sai faman safa da Marwa take, takai mari takai gawro ita kad’ai, yau d’in ita zata kwana wajen Abbah, Mamy nacan zata duba Raihanah kafin ta wuce gida sabida masu zuwa mata gaisuwa, ita kaw Raiha Mamani ce a wajenta ita zatake kwana da ita dukda cewa ba wani abin zata iyayiwa mai jinya ba da naka a kusa yafi, ma’aikatan lafiyar suke komai a asibitin...

Zufa ya kuma ketowa Aunty Lami gani take tamkar Ma’aruf ya ganeta ya gane fuskarta tsaf itace matar data d’aukesa a kasuwa ta b’anb’are hannunsa daga na mahaifiyarsa a lokacin da Mahaifiyar tasa ta fice hayyacinta tana mai neman d’auki na jama’a sabida haihuwa data zo mata bagatatan... Ta kuma share gumin tana mai sakin numfashi da k’yar...
Abbah ya bita da kallo cikeda mamaki don batasan idanunsa biyu ba, kaman daga sama taji muryarsa ya ambato sunanta “Lami...”
Ta juyo a firgice alamun tsoro da firgici a tattareda ita....
Bata iya amsa Abbah ba sai zuba masa ta mujiya da tayi....
Abbah ya d’an gyara daga kwance zuwa kishingid’e kana yace “Lafiya kike tsaye wajen, mai ya hanaki bacci...?”

Tambayar da Abbah ya mata sai taji tamkar Abbah ya riga yasan komai, ta rasa mai zatace sabida lokaci guda taji tamkar harshenta ta zarge, da k’yar ta iya furta “La... lafiya kawai banjin baccin ne akwai wani abinda kake so ne....?”

Murmushi d’auke fuskar Abbah domin gaba d’aya yinin ranar annuri ta gaza d’aukewa a fuskarsa sabida d’imbin farin cikin da ya tsinta kansa ciki yace “A’a bani buk’atar komai, hasalima ni ji nake na warke banida wata buk’ata da ya wuce su sallameni a wajen nan haka na koma gida cikin ahalina mu kasance gaba d’aya tare....”
Zuciyar Lami ta kuma tsinkewa don ita kanta ta jima bataga Abbah cikin irin wannan yanayi na farin ciki ba....
Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana ta k’araso gefen gadonsa ta zauna... Tana mai sakin murmushi take fad’in “Alhaji ga dukkan alamu kana cikin farin ciki...?”

Abbah ya jinjina mata kai cikeda aminta kana yace “K’warai Lami ina cikin farin ciki wanda na rasashi a baya, Ibangijina ya dawo min da wannan farin cikin...”

K’irjinta ya kuma bada Dam! Kardai sunsan cewa wannan likitan d’ansu ne Ma’aruf.... Idan kaw haka ne dole tasha cikin Abbah taji komai...
Ta kuma gyara zama murmushin bai bar saman fuskarta ba tana mai k’ok’arin gyarawa Abbah pillow da yake bisa tace “Alhaji halan wani abin ne ya faru...?”

Abbah ya kuma dubanta da fuskarsa mai k’unshe da tsantsan annuri kana yace “Babban al’amari ya faru Lami da sannu zaku fahimci hakan gaba d’aya...”

Tinda taji hakan tasan Abbah baiyi niyyan ya sanar da ita komai yanzu ba, tasan halin mijin nata domin kaw wani irin baud’edd’en mutum ne haka nan kalamansa wasu lokutan a baud’e suke zaiyi magana amma sai ka rasa gane inda ya dosa,idan kaw bazai fad’i mata ba ita zata sanar dashi mutuwar jikarsa idan yaso hankalinsa yayi gida komai ya fanjama fanjan kawai, ta gaji ta gaji da zullumi gwara ta sani idan Ma’aruf ya bayyawa iyayensa ne.... Ita a halin yanzu batama k’i Abbah ya mutu ba akan asirinta ya tonu....

Bata kuma cewa komai ba ganin Abban ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci, bayan giftawan wasu dak’ik’ai data tabbatar yayi baccin ta fice kiran Haule domin susan madafa....

***

A b’angaren Siyama kuwa tas ta d’auki shawarin Laila cewa kada ta bari wani k’ato ya mata mulkin fir’aunanci a gidanta da sunan yana aurenta, idan ta riga ta sabar masa da sai abinda yaga dama za’ai shikenan ta zama wofi a cikin gidanta don shi namiji tankar yaro ne duk abinda ka d’aurashi bisa shi yakeyi don haka koda wasa kar ta bari wannan raini ya shiga tsakaninsu, tuni taci gaba da shirinta washe gari sassafe ko sallama Sameer baici arziki a masa ba don shi tuni yayi asubanci ya nufi asibiti duba yaya patient d’insa ta kwana, fitarsa da kad’an suma suka d’aga zuwa Kaduna....

***

A gidan Hafiz kuwa tinda garin Allah ya waye yake jinsa wani iri haka nan, wani ikon Allah safiyar ranar da tunani da begen d’iyarsa Kausar ya tashi domin kawa daren jiyan yayi mafarki da ita, yarinyar ta k’ara masa girma tayi kyau daga can nesa taketa k’ek’eta masa dariya saidai da ya nufota zai d’auketa sai ta b’ace ma ganinsa... Tinda ya farka daga wannan baccin kewar d’iyarsa ya damesa, baikobi takan Sawwama ba ya fice cikin sauri da niyyan ya soma zuwa Kasuwa ya duba shago daga nan ya d’an sai mata tsaraba yakai mata...

Yana isa Kasuwa dashike yanzu a kantin mahaifinsa yake zama don shi yanzu baida kantin baida jari baida komai a d’an zaman da yake a kantin Alhaji mahaifinsa yake d’an samun na kashewa.... A bakin kantin ya tarar da Tasi’u yaron shagon yanzu yakeda niyyan bud’ewa, suka gaisa da Tasi’u, nan Hafiz ke tambayarsa Alhaji bai iso ba....?

Tasi’u yace “A’a ai kaman rashi naji ana cewa anyi, nima dai banje ba domin jiya ma ni na kulle kantin a hannuna mabud’an suka kwana, daga nan nima dama can zan wuce....”

Hafiz ya dubesa da mamaki kana yace “Rashi...? Toh waye ya rasu....?” Badai Abban su Zulfa’u ba don yasan shine a asibiti...

Tasi’u yace “Wllhi nima dai ban sani ba amma ina tsamman ba babban mutum bane...”

Hafiz ya jinjina kai kana yace “Shikenan Tasi’u bari na wuce can gidan...”
Tasi’u yace “Toh Maigida a sauk’a lafiya, Allah jik’an musulmi....”
Hafiz ya amsa da Ameen kana ya shige yana tunanin toh kodai a mak’ota akayi rashin tinda da ace a gida ne da ko ba’a kira wayar salulansa ba za’a kira na matarsa... Da wannan tunanin ya hangi teburin mai kayan wasan yara, ya saki murmushi a hankali kana ya k’arasa ya sai doll baby da kuma dangin kacau kacau....

Sai buga sauri Hafiz yake ya isa gida yaji abindake faruwa ya kuma dank’awa Kausar tsarabarta, tuni ya tari babur ya d’ale yana mai sanar da mai babur d’in yanda zaya kaisa...

Babban tashin hankalin da riski Hafiz shine ganin taron mutanen a k’ofar gidan mahaifinsa suke....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*51*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Da k’yar k’afafunsa suke iya d’aukansa, ji yake gaba d’aya k’afafun nasa suna masa nauyi, waye ya mutu a gidansu, makokin waye ake...? Meke faruwa ne...? Cikin sakanni zuciyarsa ta dinga jefo masa tambayoyi, daga can ya hangi Baba Alhaji mahaifinsa na masabaha da mutane suna kuma masa ta’aziya, zuciyar Hafiz ta kuma tsinkewa.... Yaci gaba da d’aga k’afafunsa da k’yar sanda ya nufo kusan mutanen sosai yaji ana cewa Allah shisa mai ceto ce....

K’afafun Hafiz suka d’auki rawa ba tareda yasan dalili ba... A daidai lokacin da sukai idanu hud’u da mahaifinsa sanda wani mutumi ke furta “Ga mahaifin yarinyar ma, sannu sannu kaji koh Hafizu Ubangiji ya baka masu zama yasa ita kuma mai ceto ce...”

Sam Hafiz bai iya amsa shi ba, hasalima bai fahimci mai yake nufi ba gaba d’aya ya zama lost and confused.... Duru duru yake ganin mutane yanda sukai chaa sunai masa gaisuwa, yana jiyo muryoyinsu tamkar daga nesa....
Yana ganin sanda mahaifinsa ya mik’e ya nufi cikin gida bayan ya rakasa da muguwar kallo....

A gigice Hafiz ya tsallake mutanen ya nufi cikin gida yana mai kiran mahaifin nasa.... Cak yaja yayi birki sanda yaga mata sun cike farandar mahaifiyarsa... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka ya nufi dandatson matan yanaji kaman zai kifa da k’asa...
Naja’atu ce ta nufosa a guje ta rungume tana kuka sosai....

“Najah lafiya , meke faruwa... What is happening... Talk to me Najah... Ina Kausar.... Where’s my daughter...? Look I bought her a lot of toys, nasan zatai murna... Kin gani....” Ya shiga k’ok’arin bud’e ledar yana ciro kayan wasan.....
Ba Naja’atu dake rungume dashi tana kuka ba harta mutanen dake zaune farandar saida sukaji k’walla na zubo masu...
Cikin tsananin kuka Najah ke girgiza masa kai sanda yake kuma tambayarta d’iyarsa.... Cikin muryar kuka take furta “Ya Hafiz Kausar babu....”

Cak ya tsaya yana binta da wani irin duba cikin rashin yarda da kalaman da suke fitowa daga bakin k’anwar tasa yake furta “What do you mean Kausar babu... Mai kike nufi Naja’atu.....?”

Cikin Kuka Najah ke fad’in “Yaya Kausar ta rasu, mun rasa Kausar , Allah ya karb’i abinsa....”

Fuzgewa yayi daga rik’on data masa yana mai binta da wani irin duba yake girgiza kai kana ya shiga furta “No no no, my daughter is alive.... D’iyata tana raye..... I know she’s alive... Ni na sani... Ina Hajiya... Ina Hajiya nasan tana wajen Hajiya... Yanzu zan bata toys d’inta.....” Tamkar zararre haka shiga surutai, lokaci guda ya nufi d’akin Hajiya gadan gadan bai damu da matan da yake haye kansu ba shidai kawai yaga Kausar d’insa...
Chapter 62 · 0% Book details