← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 198

Sashe 25

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ‘yan kwanaki biyun da Sameer baya nan saida abin ya dami Abbah, ya lura baya ganinsa a masallaci haka nan ko k’yallin motarsa bai ganin goftawanta a unguwar, ranan dai bayan an ida sallan lisha ya tare Shamsu yana tambayarsa Sameer, abin har saida ya baiwa Shamsu labari, mutumin da a baya babu ruwansa da kowa a unguwar tamkar shi kad’ai yake rayuwarsa dukda Shamsun ma dangin hakan ne amma yana hankalta da dattawan unguwar yanda suke sabo da juna amma banda Alhaji Usman Mailafiya sai gashi lokaci guda sun shak’u matuk’a da Sameer har yana tambayarsa lallai Sameer akwai shi da saurin shiga ran jama’a... Shamsu ya d’an murmusa ya sanar dashi Sameer yaje dubo gida ne...

Jikin Abbah yayi sanyi da ya fahimci ganin iyayensa Sameer ya tafi, da gaske dai wannan saurayi babu abinda ya alank’anta shi da Ma’aruf d’insa...

Ranan jiki a sanyaye Abbah ya koma gida, harta su Mamy saida suka fahimci d’an canzawan nasa na kwana biyu, lokacin da Sameer ya dawo kuwa saida farin ciki ya nuna a tattareda Abbah, lallai bahaushe yayi gaskiya da yace sabo turken wawa....

A satin Hafiz ya d’aga masu hankali da maganan k’arin aurensa, abu kaman wasa wuta wuta aka tambaya sadaki da lefe gidansu Sawwama, wai zo kaga farin ciki wajen Sawwama da Magajiya, duk wani b’uli da suka san cewa ka iya jawo masu matsala musamman mutanen unguwarsu saida suka tosheta don Magajiya ta d’au alwashin wannan shekaran sai d’iyarta Sawwama ta tare d’akin miji ba d’akin saurayi ba kaman yanda tasha yin hakan a baya...

Gidansu Sawwama basu yanke lokaci mai tsawo ba wata guda jal suka yanke dashike dama alla alla suke su mik’ata su huta, shi kanshi Hafiz ba wai d’aukin auren yake ba saidai baisan dalilin da yake matuk’ar so ayi auren wuta wuta ba, baisan ko rashin matarsa Zulfa’u bane yasa yake so ayi bikinshi da Sawwama nan kusa ko zai rage kewar matarsa da yake...

Duk wannan bidiri da ake sam Zulfah bata sani ba, hasalima farin cikin kammala bautan k’asanta take, gashi Aunty B tace da zaran ta gama Iddarta zata samar mata gurbin aiki ya rage mata kewa, yanzu babban burinta bai wuce ta sanya mahaifiyarta da d’iyarta a k’wayan idanunta ba....

***

Kaduna....

“Mummy ya fah wuce duk yanda kike tunani, kawai Mummy kisa a fara maganar auren mu inaga ta haka ne kawai zan samu attention d’insa.... Please Mum talk to your sister...” Ta k’arashe kaman zata runtuma ihu ta cikin wayar...

Daga d’aya b’angaren mahaifiyarta tace “Yesmin are you sure kinyi duk abinda nace kiyi...?”

Cikeda shagwab’a Yesmin tace “Mummy I did everything you asked me to do, amma wllhi Mummy kallo fah ban isheshi ba, I’ve exhausted all my efforts already....”

Cikin kwantar da hankali mahaifiyar tata ke fad’i mata “Ki kwantar da hankalinki ni zanyi maganawa Faridar kinji koh, kedai kawai just focus don’t lose hope kinji koh...”

Yesmin ta jinjina kai a hankali kaman mahaifiyar tata na kallonta kana tace “Alright Mum, take care... Say hello to Daddy for me...”

Daga haka katse wayar tai tana tunanin yanda zata karkato hankalin Khalid gareta...

Kubura dake lab’e bakin k’ofa rungumeda bedsheets zata kai d’akin Mamy nan ta lab’e tana sauraren wayan Yesmin...

Kusan cin karo sukai da Yesmin d’in da batasan Kubura na lab’e jikin k’ofarta ba...

Wani mugun kallo Yesmin ta watsa mata kana tace “Ke wai meye kike bibiyata, lafiya...?”

Kubura ta tab’e baki tace “Yo naga dai hanya ta biyo dani nan, d’akin Mamy zan shige Sirkar kirki...” Ta k’arashe tana d’aga gira samawa Yesmin...

Yesmin ta bitada kallo tana maimaita kalmar sirkar kirki cikin zuciyarta... Gajeren tsaki kurum tai kana ta nufo downstairs...

Hango Khalid da tai zaune tareda Ammi suna fira ya sanyata saurin komawa sama a d’ari ta d’auro makeup saman fuskarta...

Daga yanda take k’arasowa tana iya jiyo muryar Ammi tana tambayarsa..

“Mai kuma zakajeyi Kano....?”

A tak’aice yace da ita “Ammi I’ve unfinished business there...”

Ammi ta kuma dubansa da kyau kana tace “Unfinished business...?”

Jinjina mata kai yayi yana mai ci gaba da canza tasha had’ida furta “Yes Ammi but ba jimawa zanyi ba kwana biyu zuwa uku kawai zanyi...”

Ammi ta jinjina kai kana tace “Ina maganar mu ta kwana...?”

Ya d’an d’ago ya dubeta kana yace “Wanne kenan...?”

“Ka sani sarai maganar k’anwarka Yesmin nake maka, naga alama yi kake kaman ma bakasan tana gidan nan ba... What’s wrong with you Son...?”

Girgiza kai Khalid yayi had’ida kishingida cikin kujera kana yace “But Ammi I thought we’ve already talked about that... Ammi I’m not interested, I don’t love her for heaven’s sake..”

“Kai kai rufe min baki meye haka...? Wani you don’t love her ka samu banson sakarcin banza, a ina zaka samu mace kaman ita donma ka samu anason baka ita ai dai kasan Yesmin ba class d’inka bace, Khalid ka natsu kaji abinda nake fad’a maka tun wuri ka aje wannan masifar girman kan naka ku daidaita da ‘yar uwarka nasan ba sonta bane bakayi kawai tsaban jidakan tsiyarka ne kake cewa haka, Yesmin tana nan a gidan nan har tsawon sati biyu don haka kafin ta tafi naji batu mai dad’i....”

Kallon Ammi kurum yake ba tareda ya iya furta komai ba, rai b’ace ya mik’e yana fad’in “Da safe zan wuce Kano In sha Allah zan sami Daddy a office na mishi sallama....”

Yana tafe Ammi na fad’in “Ka tabbata kayiwa Yesmin ma sallama...”

Bai tsaya amsa Ammin nasa ba ya fice takaicin Yesmin na d’awainiya dashi...

Jiki a sanyaye Yesmin ta koma sama ba tareda ta iya sauk’owa ba..

Washe gari Khalid ya sauk’a a birnin Kano....

Niko nace Nabilah kinada bak’o...LoL

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_

*24*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Suna barbaje a parlorn Hajiya suna tattauna batun auren Yayansu Hafiz Sahariyya ta kuma kwashewa da dariya had’ida rangad’a gud’a tace “Hajiya wllhi zanso ace Zulfah na gidan Ya Hafiz za’ai auren nan nasan bak’in ciki sai kusan aikata lahira...”

Hajiya ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yanzu ne Hafiz ya nuna min cewa ni na haifsa, kuma banda abinki Sahariyya ai yanzu ma labarin ya risketa sai taji kaman tai hauka don kishi tinda sakinta akai aka auro wata, kuma a d’akin Zulfa’u za’ai jeren Sawwama, duk wata tsiyar Zulfa’u tattare mata zaiyi idan yaga dama ya zuba a shara tinda yak’i aminta a sanar da iyayenta babu aurensa akanta...”

Suka kuma washe baki suna k’ek’eta dariya cikeda farin ciki...

Naja takai dubanta ga Kausar dake wasanta hankali kwance kana tace “Yarinya kin kusa komawa gidan ubanki kiyi tashin hannun kishiyar uwa....”

Sahariyya ta b’allawa yarinyar harara kana tace “Aikuwa kaman kin sani ana gama cin amarci zan kwashi wannan tsiyar na kaita gidan ubanta, badai gani yake muna musgunama gudan jininsa ba, tau kaw yanaji yana gani matarsa zata lallasa mata bugu bai isa cewa komai ba, aini naji dad’i ko banza jinin Zulfah zatai girman hannun kishiya...”

Suka kuma b’allewa da dariya idan ka d’auke Hajiya dake zullumin abubuwan da suke fad’i, ko tak’i ko taso Kausar jininta ne, wannan abu idan ta tuna sai taji kaman idan ana musguna mata na d’anta Hafiz ake musugunawa, a d’an hasale tace dasu “Toh toh ya isa haka... Najah d’auko Kausar ki mata wanka...”

Wani kallo Naja ta aikawa Hajiya kana tace “Tab wllhi ban iya rainon d’anda ban haifa ba Hajiya, Uwarta na biyu Raihana ta mata...” Ta k’arashe tana k’ishingid’a cikin kujera had’ida danna earpiece a kunnuwanta...

K’wafa Hajiya tai kana ta mik’e ta d’auko Kausar da kanta ta shiga kwab’e mata kaya don Raihana na kitchen na aikin abincin rana da babu wanda yayi har saida ta dawo daga makaranta....

***

Fitowarsu kenan daga class suna tattauna lecture d’in da suka fito, sai dariya suke suna jinjina rashin mutuncin malamin nasu da yanda Nabilah bata tsoronsa har saida ya zamto idan bata aji sai ya gane, da yawan malamai sabida tsaurin idanunta da rashin tsoronta suka santa, gashi ba halin ka kayar da ita don babu laifi tana karatun ta daidai gwargwado..

Habib d’aya daga cikin course mates d’in nasu yace “Dr Manzo yau ya had’uda gamonsa... Ni tun last semester da akace zai d’aukemu kuma he’s very strict nace toh akwai aiki randa sukai arangama da Nabila....”

Yusrah k’awarta k’waya d’aya tak saiko Habib da Safwan da suke taimaka masu da tutorials tace “Wllhi ni damuwata ma kardai taje ta janyo mutumin nan ya tsanemu mu shiga uku ga course d’in nasa ita kanta ba wai fahimta ake ba...”

Safwan yace “Kuma kuna magana tayi k’us kaman bata wajen....”

Harara ta watso masu gaba d’aya kana tace “Iyakaci yace na daina shigar masa aji ba shikenan ba tinda kuna nan zaku koyan.... Ke Yussy dan Allah kizo mu tafi wllhi na gaji sallah ma a gida zanyi...” Ta k’arashe tana rataye side bag d’inta....

Gaba d’aya suka shiga darawa suna fad’in tai a hankali Dr Manzo ba kaman sauran lecturers d’in bane yanda course d’insa take a baud’e haka shima yake a baud’e....

Zata kuma magana wayarta dake cikin jaka ta d’auki ruri....

Lalumar wayar ta shigayi tana fad’in “Sai kuyi ai daga ku har shi Dr Manzon banida lokacinku....” Aya ta sakawa kalaman nata ganin bak’uwar lambar da ake kiranta dashi, kaman bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga a dak’ile don ba kasafai take d’aga lambar da bata sani ba don idan an fad’i mata abinda bai mata ba ko wanene mai kiran zaiji maras dad’i ne shiyasama wani sa’in bata d’agawa...

Gabanta ne yayi mummunar fad’uwa jin muryar dake mata magana cikin wayar, ta kasa furta koda kalma sai lugude da k’irjinta ke ci gaba dayi, dukda cewa bai wuce a k’irga ba ta tab’a jin muryar tasa amma ko kusa bazata iya mance sautin muryar ba wanda shi kad’aine mai irinta a iyaka saninta....

Murmushi yayi a hankali kana yace “Are you surprise... Kin d’auka na mance koh...?”

K’ok’arin saita kanta tai kana tace “Malam inaga wrong number ka kira please do not call this line again.....”

Bai bari takai aya ba yace “Don’t think of hanging up on me.... Ina kallonki daga yanda nake, ki sallami samarukan naki kizo mu k’arashe deal d’inmu...”
Chapter 25 · 0% Book details