← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 198

Sashe 169

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yesmin dake lab’e saman staircase harda tsallen murna take... Saidai kaman daga sama taji ta tinstiro tamkar za’a wurgota k’asa.. Ta saki wane irin ihu mai cikeda razani... Sai kuma taji an rik’e k’afafunta tana reto a tsakani.... AuntyB ta gani rik’eda k’afarta guda Ta daddage k’arfinta lokaci guda Yesmin Ke furta “Aunty Kimin rai dan Allah kada ki jefoni k’Asa... Wayyo... Wayyo na shiga uku... Aunty kimin rai mutuwa zanyi idan kika jefoni... Wayyo Allah na...!”
AuntyB da babu alamun raha tattareda ita tace “Daga yau kin daina munafunci na miki alk’awari...!” Ta kuma yunk’ura kaman zata saki k’afar Yesmin...
Yesmin ta kuma sakin ihu tana doka kirawa jama’an gidan suzo su ceceta...

A d’ari Ammi ta fito tana hangen kan Yesmin dake reto daga can saman staircase... Shiko Khalid tsaki ya danna kana ya zari wayarsa yai ficewarsa ko takan Yesmin dake ihun taimako baiyi ba. Ammi ma tana doka masa kira yazo ya ceci ‘yaruwarsa hannun dangin mayu amma inaa ko saurarenta baiba ya fice abinsa...
Yesmin na ihu Ammi na ihu, Kubura kaw mai zatai banda dariya... Fad’i take Aunty wurgota zan capke....”

Su Aunty Daula da Siyama suke ta faman baiwa AuntyB baki kan tai hak’uri kada ta jefa Yesmin.....
Aunty B kaman zigata suke sai tayi kaman zata saki Yesmin sai kaji Ammi da Yesmin na sakin sabon ihu...
AuntyB tace “Zaki sake..? Zaki sake shiga sharo babu shanu... Zaki sake shiga tsakankanin ma’aurata..!”

Yesmin na ihu kaman ranta zai fita take fad’in “Wllhi na tuba... Bazan sake ba... Wayyo dan Allah kada ki jefani kimin rai...!”

Da k’yar da sid’in goshi AuntyB ta janyo Yesmin ta fasa jefota daga saman bene...
Yesmin ta zube a wajen tana maida numfashin azaba... Aunty Bara’atu tace “Dan Allah gobe ma Ki sake kinji... Kada ki fasa...!” Daga haka ta shige d’aki abinta Ammi kaw sai Sanna tayo sama a guje tai kan Yesmin dake numfashi da k’yar tana dubata, Siyama kaw gajeren tsuka kawai taja abinta had’ida komawa d’aki... Kubura kaw bata daina dariya ba dan har video saida tai recording a wayarta yanda Yesmin ke reto daga sama tana ihu gashi dama fuskarta mulke yake da mayukan bleaching inji Kubura... Ko banza ta sami na kallo tana darawa... Haka takai masu d’aki itada Karimatu mai aikin Aunty Daula suna kallo suna k’ek’yata dariya...

****
KANO

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*103*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Ga dukkan alamu dai ta tabbata akwai saka hannun Hafiz a b’acewar Akram tinda gashi shima Hafiz ya b’ace b’at babu shi babu dalilinsa, Jami’an tsaro basu fasa binciken yanda zasu sami Akram ko Hafiz ba...
Magajiya ta gyara zama sosai tana duban Sawwama kana tace “Hafiz bazai tab’a fitowa a raye ba kema kinsan waye Duna... Dan haka abu mai sauk’i amsar kud’in sassan jikin Hafiz zamuyi kinga riba ya zama namu....”
Sawwama ta nusa kad’an kana tace “Amma Magajiya baki tinanin abin nan ya dawo kanmu, kinga fah Akram yanada matsayi sosai wajen mijin Zulfa’u, kuma Engr Mutallab ba k’aramin mutum bane a gari... Anya kinaga baza’a zak’ulo mu ba.... Hafiz da Akram ba kaman sauran ‘Yandaudun da muka saba kassarawa bane.... Anya kuwa kinaga zamusha...?”
Tsuka Magajiya ta buga kana tace “Ta yaya za’a zak’ulo mu... Ke tin kafin a haifi uwarki Duna ke satan mutane yana garkuwa dasu yana amsar kud’in fansa... Kuma kaman yanda ya sanar dake babu wani maras kunya mai k’aryar uniform da ya isa ya kawo k’arshen ta’addancinsa a fad’in k’asar nan... Dan haka bazamuyi biyu babu ba, dole ya bamu diyan Hafiz dana Akram....!”

Daidai nan Baba Alhaji ya d’ago labule yana bin Magajiya da wani irin duba.... Jikinsa har k’yarma take... Sawwama da tsoro ya d’an nuna a fuskarta duban mahaifiyarta tai taga babu ko alamun gizau a tattareda ita sannan ta dubi Baba Alhaji taga naci gaba da huci....
Sawwama ta duk’a ta d’au mayafinta tana fad’in “Ni zan wuce Magajiya sai munyi waya....”
Ta d’ago tana duban Baba Alhaji da yai k’ebebe a hanya yana binta da muguwar kallo... Lokaci guda yake furta “Kije ina bak’ar munafuka azzaluma... Ashe saida min d’an nawa kukai... Kuka bisa da sharrin shi ya sace Akram... Toh dubunku ya cika asirinku ya tonu... Yanzu ba sai anjima ba zan kirawo ‘yansanda suyi gaba daku... Kuma Wllhi billahi sai kun fito min da d’ah na...!”
Sawwama data d’an razana saurin rik’o babban rigar Baba Alhaji tai tana fad’in “Haba Baba kaima kasan bazamu tab’a yin haka ma Hafiz ba... Ba sai ka kaiga kiran ‘yansanda ba....!” Ta k’arashe tana mai kashewa Magajiya idanu alamun ta tayata shawo kan Baba Alhaji....
Baba Alhaji kaw bige hannun Sawwama yai daga jikin rigarsa yana fad’in “Kyaci uwaki bak’ar munafuka azzaluma... Sakar min riga...!”
Sawwama bata cikasa ba saima dad’a marairaice masa da take tana kuma duban Magajiya dake ci gaba da taunar chewing gum d’inta alamun koma a k’asar gyalenta, lokaci guda take ci gaba a kashe ma Magajiya idanu alamun ta shawo kan Baba Alhaji kar ya fice kiran Jami’an tsaro... Ga tsananin mamakinsu muryar Magajiya suka sinkayo tana fad’in “Barsa yaje... Dan Allah kaje Kaga waye zamu jefa rana....!” Tai maganar tana mai takowa zuwa gaban Baba Alhaji kana taci gaba da fad’in “Kanada shaida....?”
Baba Alhaji yai shiru sai muzurai, sai kuma yace “Allah shine shaidata....!”
Dariya Magajiya Ta kece dashi kana tace “Allah baya zama gatan azzalumai bara kaji na fad’a maka... Ai shi ba azzalumin kowa bane kuma ya sanya zalunci ta zamto haramun tsakanin Al’umma... Ko ka mance kalan zaluncin da kai kaiwa d’an uwanka... Ka mance cewa kaso kassara rayuwar d’an uwanka da gudan jininsa... Toh mai zaisa kai mamaki dan wasu sun tasamma kassara rayuwar Naka d’an... Ai bari kaji na fad’a maka dik abinda mutum keyi a duniyar nan ko ba dad’e ko ba jima kansa yake komawa... Abinda kai shi za’a maka... Ashe k’aryar zalunci kake... Dan Allah ga fili ga doki... K’ofa a bud’e take ka tafi wajen jami’an tsaro Kaga yanda zan jefa maka laifin alhakin mutuwar d’anka a wuyanka kuma duniya kaf su yarda kaman yanda muka jefa ma d’anka Hafiz alhakin b’acewar Akram... Kadai san wannan shine a dakeka kuma a hanaka kuka koh...? Toh bismillah shege ka fasa... Jeka ga hanya...!” Ta k’arashe tana jijjiga gabansa had’ida kuma turo d’aurin kwali gaban goshi...

Ga mamakin Sawwama hawaye ta gani na kwaranyowa daga idanun Baba Alhaji... Lokaci guda yasa gwiwoyinsa duka biyu yana rok’on Magajiya yana fad’in “Kiyi min rai dan Allah kada ki bari a kashe Hafiz... Wllhi Ina son d’ah nah... Dan Allah ki ceceni ki dawo min da Hafiz gareni, na tuba wllhi....” Ya k’arashe yana had’e hannayensa biyu waje guda...
Magajiya na jijjiga take murmusawa cikeda k’asaita ganin Baba Alhaji duk’e gabanta yana rok’onta... Saida Ta kuma takowa har gabansa kana ta d’an shafi kansa tace “Dalin Dalin... Wllhi har ka bani tausayi... Zanso Hafiz ya dawo gareka amma saidai kashhhh..!!! Qaddara ya riga fata... Duna baya ganin abu yayi masa ya k’yale sannan dik abinda Duna yayi amfani dashi toh fah wani bil’adama baya kuma amfana da wannan abin... Duna salwantar da wannan abin yake.... Shawari d’aya tak ya rage gareka idan har kanaso ka amfana da d’anka Toh fah saidai kabi sahu mu amshi kud’in diyan shi... Kaga shike nan baka haifosa ya koma a hotiho ba, ko banza ka amfana da kud’in sassan jikinsa....!” Ta k’arashe tana mai zaro idanunta da suka sha Farin tozali a fuskar Baba Alhaji da har yanzu k’yarma yake....

Girgiza kai yake yana duban Magajiya shaye da mamaki kana yace “So kike kice na saida d’an nawa...?”

Murmusawa ta kumayi kana tace “Ni taimakonka nake kar ka tashi a tutan babu don ina mai tabbatar maka cewa kaida Hafiz saidai ku had’u a lahira kuna la’antar juna dan bakuyi aiki mai kyau ba a duniya balle nace had’uwarku zai maku dad’i... So shawari ya rage maka....!” Ta k’arashe tana wani taku tsakiyar d’akin...
Gumi ta ko ina ke tsartsafowa Baba Alhaji... Yana duk’e a wajen sai kece gumi yake... Wannan wace irin bak’ar ranace a rayuwarsa... Da kansa ya amince ya amshi kud’in sassan jikin d’ansa Hafiz.... D’an da yaci buri akansa har yaso salwantar da d’an d’anuwansa dik a sabida dashi... Yau gashi da kanshi zai bari yanaji yana gani ‘yan ta’adda su salwantar dashi bashida kuma halin hanawa.... Tuni ya kwabe hularsa da babban rigarsa ya zauna dirshan a tsakar d’akin yana kuka sosai... Sawwama ko duban mahaifiyarta tai had’ida jinjina mata kana tai ficewarta abinta...

***

Da k’yar ta iya mik’ewa tana duban Shamzy dake gefenta tana shiryawa, Shamzy ta bud’e murya tace “Wai ni Muhibbah har yanzu k’wak’walwarki bata iya d’aukan strong drugs... Jibi fah tin jiya kike yashe a nan sai yanzu...”
Tsuka Muhibbah tai had’ida kame b’angaren kanta dake tsananin mata ciwo kana tace “Ina Bash... Bai iso bane....?”
Shamzy ta tab’e baki tace “Bash fah tin asuba yake jiranki a gidan nan, yana parlor... Kece kin kasa tashi a bacci daga testing new products d’inmu....”
Tsuka Muhibbah ta kumayi kana ta mik’e da k’yar ta k’ara saman k’aramar table dake d’akin ta d’au maganin ciwon kai ta afa had’ida korawa da ruwa kana ta nufo downstairs yanda Bash ke zaune yana jiranta... Daga k’ofa ta hango bodyguards d’insa sun k’akk’ame....
Bash na hangota ya k’araso gareta yana fad’in “Finally the Queen is awake.... Kema kinsan na tsani jira Muhibbah.. Sabgogin gaba na sunada yawa... Badon nasan business zamu tattauna ba da bazan tsaya jiranki kina b’ata min lokaci ba... So did you get my message last night...?”

Gajeren tsuka tai kana tace “Bash ba wannan ba, wata alfarma nake so kamin....”
Bash ya gyara tsayuwarsa kana yace “Kaman mai kenan...?”
Chapter 169 · 0% Book details