← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 198

Sashe 36

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Nabilah kuwa tinda tai wayan nan suka kula da canzawanta, gaba d’aya walwalarta ta d’auke k’arshema ce masu tai tafiya zatai..
Aunty B ta tab’e baki tace “K’ila dai sirkin namu ne ya tab’oki...,”
Nabilah ta kuma turo baki gaba tace “Sirki, Sirki fah kikace Aunty... Nidai bani kula kowa kuma banida lokacinsu...”
Aunty B tace “Aiko bazamu zuba miki idanu haka nan ba dole ki kawo mana Sirki...”
Nabilah ta mik’e ta rataya handbag d’inta tana masu sallama, Zulfah ta mik’e da niyyan yimata rakiya koda bakin gate ne don ta lura akwai abindake damun ‘yar uwar tata tana son tambayarta....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_

*30*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Agogo Siyama ta kuma dubawa ya nuna k’arfe 10:00pm daidai, ba d’abi’arsa bace kaiwa irin wannan lokaci a waje, ko a baya idan yanada surgery da dare yakan sanar da ita ko ya sanar da sakatariyarsa ta kirata ta fad’a mata...
Ko a mafarkinta bata tab’a zaton akwai abinda zatai Sameer yayi irin wannan fushin ba, tinda take dashi duk sab’anin da zasu samu bai tab’a k’in d’aga wayarta ba amma sai gashi yau ta kirashi yafi sau abinda yafi bai d’agawa k’arshema kashe wayar yayi gaba d’aya...
Tana nan zaune wajen har gyangyad’i ya soma d’aukarta taji k’aran tab’a k’ofa...
Ta mik’e zunbur tana mitsike idanu....
Kallon kirki bata isheshi ba yasa kai ya nufi upstairs....
Siyama tabi bayanshi a guje kana tasha gabanshi sanda yake shirin shiga d’aki...
“Partner let’s talk please...” Tai maganar cikin raunanniyar murya...
Baice mata komai ba saima k’ura mata idanu da yayi...
Gaban Siyama ya fad’i sakamakon hango wani sabon tashin hankali da tai cikin k’wayan idnunsa, muryarsa ta jiyo yana fad’in “Ammi ta sanar dake wani abu gameda rayuwata ne...?”
Tambayar ta kuma haifar mata da fad’uwar gaba, kasa furta komai tai sabida tsananin tausayinsa da ya sauk’o mata, tabbas ta lura akwai abinda ake b’oye masa ba’aso ya sani...
“Tell me Siyama, Wannan shine dalilin..? Shine dalilin da yasa kika k’yamaci had’a zuri’a dani.... Was that the reason....?”
K’walla suka ciko idanun Siyama, cikin rawar murya take furta “Partner believe me wllhi bansan komai ba nima.... Ban sani ba...”
Jinjina kai yayi yana murmushi wacce tafi kuka ciwo kana yace “Don’t lie to me again, an jima ana min k’arya ana fooling d’ina... Amma ki sani wannan shine karon k’arshe, Sameer d’in da kike gani tsaye a gabanki ba d’aya yake da wancan Sameer d’in ba who fell in love with you and your lies.... No one, no one would ever fool me again... Sannan ko mai ake rufewa akaina I’d find out...” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige d’akinsa ya bar Siyama tsaye a wajen tana hawaye, ita kanta gaba d’aya ta rasa wasu irin abubuwa ne ke faruwa, duk abinda Sameer ya fad’i gaskiya ne akwai sirrin da ake b’oye masa amma ita kanta bata sani ba gashi yak’i bata chance ta masa bayanin cewa ita kanta batasan mai iyayensu ke rufewa ba....
Jiki a sanyaye ta shige nata d’akin tana tunanin kwana gida guda da Partner ba tareda tayi matashi da k’irjinshi ba....

***

Washe gari sassafe ya fice harta Siyama batasan lokacin da ya fice ba sai tashi tai taga babu motarsa, ta sauk’o k’asa ta hangi dining table d’insu babu komai bisa wanda da a baya ne da yanzu ta tadda breakfast maiji da lafiya, shiryawa tai ta nufi gida don ko office bazata iya zuwa ba...
Tana isa gidan ta tadda Kubura da Yesmin na fad’a don Yesmin taga cookies d’in dataiwa Khalid a hannun Kubura tanaci tana lumshe idanu sannan koda ta tambayeta sai cewa tayi Khalid ne ya bata musamman...
Ta yanda Yesmin ke shiga bata nan take fita ba Kubura ma tak’i yin shiru sai yafa mata maganganu take...
Siyama ta dafe kanta tana fad’in “Waiku dan Allah bazaku tab’a jituwa ba, baku da wani abinyi ne....?”
Yesmin tace “Cousin wllhi sai Ammi ta kori yarinyar nan I can’t stand her anymore...”
Kubura tai shewa kana tace “Wllhi nida Ammi mutu ka raba, haka kikazo kika taddani a gidan nan kuma haka zaki tafi ki barmu ehe...”
A kufule Yesmin tai kanta zata kai mata duka Siyama ta shiga tsakani daidai lokacin da Khalid d’in ya shigo cikin shiri wanda ko ba’ace maka ba fita zaiyi....
Gaba d’aya daga Yesmin d’in har Kuburan suka natsu, sai mugun kallo da suke aikawa junansu...
Ko wacce daga cikinsu hangen d’an paper bag d’in dake hannunsa suke...
Siyama ta dubesu duka biyu tai dariya kana ta maido da hankalinta ga Khalid dake tambayarta Ammi...
Murmusawa tai tana duban ‘yan matan nasa kana tace “Kaga nima zuwana gidan kenan, why not ka tambayi ‘yan gidan...?” Ta k’arashe tana nuna masa su Yesmin da Kubura wacce tuni ta shiga goge table tana satan kallon kyawawan yatsun k’afafunsa dake jere cikin takalmi...
Baice komai ba yasa kai ya nufi cikin parlorn Yesmin na gaisheshi kai a sanne...
Idan jakan hannunshi ya amsa shima zai amsa, batasan yazo wuya da ita ba, baison shishigi sam a rayuwarsa....
Kubura ta kauda kai gefe tana dariyar mugunta, yayinda Yesmin ta had’iyi bak’in cikinta...
Bai k’arasa staircase ba Ammi ta sauk’o tana fad’an tun daga bathroom take jiyo hayaniyan Yesmin da Kubura...
Turus tai ganin Khalid yasha ado jampa da hula wanda ba kasafai yake hakan ba...
Gaisar da ita yayi, ta amsa kana ta k’arada “Babana sai ina kuma...?”
“Kano, inada pending activities acan...” Ya fad’i yana zira wayarsa cikin aljihu...
Mamaki ya kama Ammi, wannan yawan zuwa Kano da Khalid keyi anya na lafiya...
Shiru ta d’anyi kana tace “Khalid ka fad’amin gaskiya mai kake zuwa yi Kano...?”
D’an dubanta yayi kana yace “Ammi yanzu da girmana za’amin wannan tambayar, Ammi aiki ke kaini...”
Siyama kuwa tunda taji yace Kano ta soma tunani koma dai Sameer ya koma ne, idan kuwa haka ne tabbas gwara tabi Khalid taje ta samu mijinta don bazata tab’a bari ko wane irin al’amari ne ya rusa masu rayuwar farin ciki da suka taso cikinta ba....
Jinjina kai Ammi tai kana tace “Toh shikenan Allah taimaka, da fatan dai kayi breakfast...?”
Yace “Nasha tea dai banson cin solid abu idan zan hau hanya...”
Nan ma jinjina kai tai had’ida masa Allah ya kiyaye ya tsare hanya.. Siyama tai saurin cewa zata bishi...
Daga Khalid d’in har Ammi kallon mamaki suka bita dashi...
Khalid yace “Lafiya dai ko...?”
Wani kallo ta aika mashi kana tace “Lafiyar kenan wajen mijina zanje ko laifi ne...”
Ammi ta bita da kallo ba tareda tace komai ba don tasan kwanan zancen...
Siyama taci gaba da fad’in “Kaga zamu tsaya gida na d’anyi parking...”
A d’an kaikaice ya dubeta kana yace “Zaki b’atamin lokaci dai, wllhi 5 minutes zan baki ki shirya duk abinda zaki shirya....”
Sosai take son tafiyar shiyasa bata tsaya tanka Khalid ba...
Yesmin kaw tanata jira taga ma waye Khalid zai mik’a jakar nan sai gani tai ya fice dashi a hannunsa take zuciyarta ta soma zargin Khalid ba aiki yake zuwa Kano ba tabbas watace ke neman k’wace mata shi a can, idan kuwa hakane wllhi bazata tab’a bari hakan ta kasance ba Khalid nata ne ita kad’ai....

***

Momy zaune saman darduma ta ida sallan walha kenan sai ganin Sameer tai tsaye kanta idanunsa sunyi jazir....
Gabanta ya yanke ya fad’i, aje cazbahan dake hannunta tai kana tace “Sameer lafia...?”
Baice komai ba sai dubanta da yake zuciyarsa naci gaba da mashi zafi.... A hankali yake furta “Momy can you please tell me the truth once and for all....”
Girgiza kai Momy tai tana dubansa kana tace “Sameer why are you doubting your own mother... Why Sameer...?”

Cikin zuban hawaye ya d’ago mata takardan dake hannunsa kana yace “I’ve a DNA result that clearly shows Daddy is not my biological father.....”

Wani irin bugu k’irjinta yayi bata tsammanin Sameer zai tsananta binkice irin haka ba, hawaye ne taji suna kwararo mata bata tab’a tsammanin zuwan irin wannan ranar ba ranar da za’ace Sameer d’inta zai fahimci ba ita ta haifeshi ba... Muryarsa ya kuma katseta cikin tsananin rawa sanda yaci gaba da fad’in “Momy why...? Why Momy... Why did you decide to keep it from me..”

Cikin kuka take furta “Because the truth will hurt you Son, Sameer bamu tab’a muzguna maka ba ko wani abu makamancin haka, a ko yaushe burinmu shine ka kasance cikin farin ciki, ka shigo rayuwarmu ka haskaka mana a lokacin da duniya ta mana k’unci....”

Cikin rawar murya ya furta “But don’t you think I deserve to know who my real parents are... Suna raye ko suna mace, idan suna raye ina suke... Idan sun mutu inaso nasan matsayinku a wajensu...?”

Momy ta share hawayen da suka kwararo mata jiki a snyaye ta k’arasa bakin gado ta zauna, tabbas batasan ta yanda zata soma ba, batasan ta yanda zata soma sanar da Sameer ga yanda akayi ya k’are a hannunsu ba, ta tabbata idan ta sanar dashi cewa suma basu san iyayenshi ba hakan sai yafi komai masa ciwo wanda k’uncinshi shine abinda batason gani a rayuwarta...
A hankali idanunta naga wani b’angaren ta furta “Sameer ka fita don Allah and kar ka sake zuwa min da zancen nan....”

Duban tsananin mamaki yake mata kana ya jinjina kai yace “Alright Momy, zan fita kaman yanda kika ce sabida har abada zaki tabbata uwa a gareni koda ace akwai sirrin da kike b’oyemin, but Momy zanci gaba da bincike har sai na gano su waye sukai sanadiyan zuwata wannan duniyar... I’m sorry idan kalamaina sun maki tsanani... I’m sorry Momy...” Daga haka sa kai yayi ya fice zuciyarsa na kuma raunana..
Gida ya koma kana ya soma shirin komawa Kano, abubuwa da dama su suka cunkushe a zuciyar Sameer, yana buk’atar a masa bayani a warware masa komai dalla dalla, da k’yar ya iya driving da taimakon Allah har ya isa garin Kano, daga Mama har Shamsu sam babu wanda ya gane kansa tinda ya dawo, k’arashe ma kulle kansa yayi a d’aki ya kwanta ko baccin dole wanda baiyiba tun daren shekaran jiya zai d’auke sa...

***
Chapter 36 · 0% Book details