← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 198

Sashe 77

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai tai kana tace “Yes you heard me loud and clear.... Don’t ever think of me again...!” Ta kuma sa kai ta shige cikin sauri hawayen da take dannewa na zubo mata... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Khalid yai tsaye a wajen... Ba Ammi kawai ba harta su Siyama tsaye sukai suna duban Khalid wanda ya koma tamkar ruwa ya shanye....
Ammi ta janyo hannayen yaranta su Siyama da Yesmin tana mai masu alamu da bakinta cewa suyi shiru su shige cikin gida kurum su k’yale Khalid da alama burinsu ya cika Khalid da Nabilah sun rabu rabuwa ta har abada....

Cikin sauri ya shiga bin bayanta yana furta “Hey hey!!...” lokaci guda ya finciko hannunta ta dawo da baya tana mai furta “Don’t touch me...!”
Tsaye kurum Khalid yai yana kallon yanda hawaye ke zuba daga idanunta.... Gaba d’aya sai yaji babu dad’i ya tuna a halinda ya risketa da mahaifiyarsa da kuma ‘yanuwansa, kalan wulak’anci da cin zarafin da ya tadda suna mata.... A hankali yake furta “Did they hurt you... Let me see are you hurt...?”

Cikin kuka take furta “Kar ka matso yanda nake, kaje kaji da iyayenka they’re all that matters....”
Hango hannayenta yayi yanda suka kukkuje... A hankali ya dafe kansa yana mai fuzar da iska lokaci guda yake furta “See, kin gani koh... Shiyasa bansan mai ya kawoki nan ba... Gashi nan sunji maki ciwo, do you think I can bear seeing you hurt...You know you’re so naughty....” Da zafi zafi yayi maganar...

Daddy dake tsaye balcony d’insa yana hangosu daga yanda yake, k’arasowa kusa sosai yayi yana mai sauraronsu...

Nabilah taci gaba da fad’in “Among the two of us who’s been naughty... huh? So kake Ina gani ka d’auko hanyar halak’a na k’yaleka... Do you even think zan barka ka zab’i hanya maras d’aurewa, hanyar da zai kaikaga halak’a... Well, no.... Ko mai zasumin I don’t care as far as hakan zaisa ka sami amincewa da yardar mahaifanka domin yardarsu na tareda yardar Allah ne...” Ta d’an sassauta murya kad’an kana tace “Please enough of this already.... Let’s go our separate ways...”

Murmushin k’arfin hali Khalid keyi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake fad’in “And who told you sabida ke na tafi na bar gida..? Oh c’mon give me break princess.... Kawai bazan tsaya amin auren dole bane, don har abada bazan tab’a son yarinyar da suke so na aura ba, I’ll rather die than na auri wannan yarinyar kin fahimta....?"

Nabilah tai shiru tana dubansa yanda yake huci, tabbas har cikin ranta taji babu dad’i da yace ba sabida ita ya bar gida ba.... Lokaci guda tai kicin kicin da fuska kana tace “Well, yayi kyau... Thank goodness cos I don’t want to be in the image.... Rayuwarkace kayi yanda Kaso da ita Allah ya gani na fad’i gaskiya na fita... And ka sanar da wannan abokin naka kada ya sake kirana....” Cikin tsiwa tai maganar wanda yasa Khalid murmusawa don ta juye masa Nabilar da ya soma sani had’uwarsu ta farko...
Ya bud’e murya yace “Fine naji... Zan amshi zab’insu...”

Cak Nabilah ta tsaya tana saurarensa lokaci guda yaci gaba da furta “And zan fice daga rayuwarki na har abada, badon komai ba sai don banaso wani cikinsu ya kuma hurting d’inki....”

Ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka zubo mata...
Khalid yayi k’arfin halin furta “Alright Miss Grumpy nayi binda kikeso ki tsaya muyi proper goodbye please....”
Bata tsaya ba saima sauri data k’ara tamkar zata kifeda k’asa.... Khalid yayi saurin bin bayanta amma ko kad’an bata bari ya cimmata ba....
A hankali ya furta “I love you... And I’ll always does....” Ya lumshe idanunsa siririyar hawaye ta sauk’o masa...

Daddy da komai ya faru akan idanunsa a hankali ya koma da baya ya zauna yana mai nazarin abinda ya faru tsakanin Khalid da yarinyar nan, idan ya fahimci wani abu shine yaran suna tsananin son junansu kuma dukansu sun sadaukar da farin cikinsu ne domin kare junansu, amma idan har abinda Farida take fad’i kan yarinyar gaskiya ne mai yasa baiji ajikinsa yarinyar tanada wani aibu ba....? Toh amma bijire masa da Khalid yayi fah...? Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ya dauk’i ruwa dake saman k’aramar table ya kurb’a...

Nabilah tana isa mota ta rungume Aunty B tana kuka sosai....
Aunty B jiki a sanyaye ta maida mata martananin rungumar kana tace “Let it out daughter... Yi kukanki....”

Saida tayi mai isarta kafin ta iya furta “Aunty na rabuda Khalid rabuwa ta har abada....”
Aunty B ta kuma rungumeta tana share mata hawayenta take furta “This is for the best Nabilah, hakan yafi tinda danginsu sam basa k’aunarki.... Kuma tabbas kinyi k’ok’ari da har kika taso kika nunawa Khalid rashin dacewan abinda yayi, k’arshen soyayya da zaki masa kenan ki nusar dashi kuskure babba da yayi a baya domin al’amarin iyaye nada girman gaske, Allah ya zab’ar maku abinda yafi zama alkhairi a gareku baki d’aya kedashi....”
Jinjina kai kurum tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba kana suka d’auki hanyar gidan wata k’awar Aunty B domin su d’an yada gajjiya su kuma yi sallah kafin su d’auko hanya don basuso dare ya masu....

***

Tamkar maras numfashi haka Hafiz ke zube a wajen, koda motsa ‘yar yatsansa ne ya kasa, ya kwashe kusan sa’a guda zube a wajen gashi babu abinda aka fasa a cikin gidan saima wasu sabbin ‘yandaudu dake shigowa cikin gidan.... Ashe Wai hakance take faruwa idan d’aya daga cikinsu yayi aure toh fah sai sunzo sun had’a masa kalan tasu bukin shine sallamarsu tsakaninsu dakai, toh ita Sawwama ba’ai mata nata ba sai yanzu....
D’andaudu guda ne ya kusa tuntub’e da Hafiz ya doka salati yana dafe k’irji ganin mutum zube a wajen... Lokaci guda yake furta “Na shiga uku ni Lanti waye haka nan zai kadani k’asa ya tonan asiri ya ragen farashi.....” Ya shiga haske fuskar Hafiz sosai da d’an tocilan jikin wayarsa, lokaci guda ya saki shewa yana fad’in “Kai kai kai kuzo Yo ai ni na taki sa’a nai babban kamu, wannan zankad’ed’en saurayi haka...” Ya shiga shafa fuskar Hafiz yana kareraya... Maganganunsa ya janyo hankulan sauran ‘yan uwansa ‘yandaudun suka d’ungumo sukayo kan Hafiz kowa na masa nasa salon karya jikin....
D’ayan yana fad’in ku bari a bisa a sannu inaaa gaba d’aya sunyi chaa akan Hafiz har saida hankalin Sawwama yazo garesu, tayo kansu tana fad’in “Toh Lanti wa kuka samu haka, kwayi hak’uri ku barma guda d’aya ai.....” Batakai aya ba sukai idanu hud’u da Hafiz dake zube wajen yana numfashi da k’yar....
Sawwama ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku mijin nawa....”
Lanti yace “Aaaaah kice abin du namu ne... Ayyiriri gaskiya kin iya zab’e k’awata Yo dole kike b’oye mana shi ashe... Yau dai sai a barmu mu d’anah....” Ya k’arashe yana tafe hannaye....
Sawwama ta shiga turesu tana fad’in “Banson iskanci kunajina koh, kowa ya fice min a d’aki ku jira daga waje.....” Ta k’arashe tana k’ok’arin d’aga Hafiz....

Da k’arfin gaske ya fincike daga rik’on da ta masa yana mai tsananin huci dukda zogi da k’irjinsa ke masa.... Lokaci guda ya capko wuyanta ya shak’e da duka k’arfinsa, wasu irin ruwa suna fitowa daga idanunsa da suka koma tamkar jan gauta har saida ya danganata da jikin garu... Cikin wata irin dashesshiyar murya mai cikeda firgici yake furta “Wllhi yau sai na kasheki.... Matsiyaciya muguwa azzaluma.... Kin rabani da matata Kamilan mace natsestiya wacce batada kusanci da irin halayyanki, kin kashe Kausar, kin halak’amin rayuwa... Kaman yanda kika kashe mun aurena da d’iyata Wllhi sai na kasheki nima....” Ya kuma danne wuyanta sai zaro ido take tana yunk’urin yin nishi har saida’yan daduronta sukayo kan Hafiz suna yunk’urin janyesa... Wasu kuwa suka fice a guje don kar ayi kisa suna wajen, mai kalangu da garayama ya cika ma rigarsa iska a guje....

Da k’yar suka iya janye Hafiz daga shak’anda yayima Sawwama.... Yaci gaba da huci hawaye masu tsananin zafi suna ci gaba da zubo masa.... Fincika yake daga rik’on da suka masa yana fad’in duk wanda ya kuma zuwa kusansa sai ya kasheshi...
Sawwama ta mik’e da k’yar tana mai watsa masa harara take fad’in “Koda wasa kada ka saka ka kuma cewa ni na kashe maka aurenka da d’iyarka, ka fara zargin kanka kafin ka tuhumi wani don duk abinda yake faruwa yanzu are consequences of your actions, kuma da kake cewa na kashe d’iyarka da aurenka uwarka da ‘yanuwanka zaka soma tuhuma baniba don ni tayasu kawai nayi.... Sannan da kake cewa nida tsohuwar matarka mun banbanta naga nidakai duk kanwar jace, nasan baka fasa komai ba a halayyanka don haka koda wasa kada na kumaji ka zageni... Sannan bari kaji na fad’a maka babban kuskuren da zaka tapka shine kayi tunanin rubutamin saki don wllhi sai ka fice min cikin gida, Don idan baka sani ba ka sani a lokacin da baka a hayyacinka lokacin da asiri ke tasiri akanka tsaf na sakaka ka sauya takardun gidan nan zuwa sunana, kuma babur d’inka da aka sace ba sacewa akai ba nice nan na sa aka d’aukemin, harta kantinka da ya kama da wuta ba Wai tsautsayi bane, a’a nice nan na saka aka kwashemin kayan ciki na kuma bada umarnin a bankama kangon gini wuta sabida gudun rana irinta yau ranan da zakace zaka rabu dani... Domin ni nan daka ganni duk abinda kaga nayi toh fa sai idan zan sami riba a cikinta... Don haka ka tattara k’afafunka ka fice min a gida tun kafin nasa su lallasa maka bugu ko ka sakeni ko baka sakeni ba na saku don bakada sauran amfani wajena.... Kai kira saminu gurmi ya sake mana sabon kid’a.....” Ta k’arashe tana juyi yayinda sauran ‘yantashan nata suka tayata da ele da gud’a....

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un........ Abinda zuciyar Hafiz ke iya nanatawa kenan.... Wani hadiri hadiri da taurari yake hangowa cikin idanunshi, mai ya jefa kanshi ciki....? Shin anya Sawwama ‘yar adam ce...? Kenan gaba d’aya rayuwarsa ita ta kassara masa... Mai ya mata da tsananin haka....? Ya rintse idanunsa yana mai ci gaba da jefa k’afafunsa ba tareda yasan yanda ya dosa ba....
Chapter 77 · 0% Book details