← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 198

Sashe 28

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin wannan tunani ne taga kiran Mamy na shigo mata, jikinta ya kuma yin sanyi, a hankali ta d’aga wayar saidai kafin ta iya furta koda kalma kuka ya kufce mata, lallashi da shawarwari na gari Mamy ta dinga bata har saida Zulfan taji tausayin kanta dana mahaifiyarta sanin cewa mahaifiyarta batasan da mutuwar Aurenta ba har rana mai kaman ta yau, yinin ranar haka Zulfa’u tayishi jiki a mace...

A can gidan biki kaw Hafiz da kansa yazo ya d’auki matarsa suka tafi gidansu bai bari ko wata mata ta kai mishi ita ba.. Suna isa Sawwama ta yaye lullub’in dake kanta don dama tuntuni ya isheta da nauyi k’awayen Magajiya ne suka hanata cire lullub’in tuntuni...

Mik’ewa tai ta shiga bin gidan kallo ta fito da sauri tana hangen ta yanda zata hango uwar gidanta, wayam bataga kowa ba.... Dawowa parlor tai ta samesa yana kwance k’ullin kaza da ya shigo dashi kana tace “Ina matarka...?”

Ba tareda ya dubeta ba yace “Tayi tafiya....”

Sawwama ta kuma dubansa kana tace “Tafiya.... Tafiya fah kace.... Kasa jure amsar amaryar tata tai shi ya sanyata yin tafiya koko dai salon nata kishin kenan....?”

Bai tankata ba yaci gaba da abinda yake....

Sawwama ta gyara tsayuwa tace “Magana fah nake maka...”

“Toh ai maganar taki ne batada amsa...” Ya fad’i nan ma ba tareda ya dubeta ba...

K’wafa tai tana watsa masa mugun kallo kana ta nemi waje ta zauna tana sakin hamma....

Ya ida warware ledar kan yayi wani aune Sawwama takai hannu ta cafko tsoka guda ta wuga a baki sai sautin taunarta ne kawai ke tashi....

Hafiz ya d’ago idanu yana dubanta tsaban takaici saida yaji dama bai warware ledar ba...

Tsame hannunsa yayi kana yace “Kije ki d’auko plate a kitchen a haka ai bazai maki dad’in ci ba....”

Ba tareda ta kallesa ba sai aikin tauna take tana gwaguyan k’ashi tace “Wayace maka kazar amarci a plate akeci, idan baka sani ba na k’ara maka ilimi a ledarta akeci...” Ta k’arashe tana kuma karyo cinyar kazar ta shiga dannawa a bakinta...

Tamkar wanda ruwa ya shanye haka yayi zaune dirshan a wajen yana kallon ikon Allah, ya tuna aurensu da Zulfah k’in siya mata kazar yayi har saida abokansa suka sai mata kuma ko da ya kawo batamaci ba hasalima da safe ya tadda ta d’uma masa kazar ta saka masa a flask idan bai mance ba da kazar marcin Zulfah yayi breakfast maiji da lafiya...

Guntun tsaki yayi kana ya mik’e ya nufi kitchen d’auko plate, babban abinda ya bashi mamaki shine daga fitarsa zuwa kitchen veranda kawai ake tsallakewa amma koda ya dawo ya tadda Sawwama ta gama da kazar nan tas sai curin k’asusuwa da ya hango....

Tamkar maraya haka ya shigo da plate a hannu yana dubanta...

“Ina kazar....?” Ya tambaya sanda yai mata tsaye aka...

Wani kallo tai masa a dak’ile kana tace “Ban gane ina kaza ba, dama kazar na waye...? Ince tawace toh na cinye kayana...” Ta k’arashe tana sakin gyatsa mai k’arfin gaske....

Tsabagen takaici bai kumabi takanta ba ya shiga d’aki yayi shirin baccinsa...

Haka nan ta shigo ta taddasa kwance da alama bacci ya soma yin gaba dashi...

Dariyar rainin hankali ta saki kana tace “Eh lallai dole kazo ka bajemin a gado kana bacci, idan kasan wata bakasan wata ba....”

Hannu tasa ta shiga bubbugashi tana fad’in “Hafiz... Tashi fah zakayi don yau ba ranar bacci bane....” Ta k’arashe tana juyi gabanshi had’ida zuge zip d’in rigarta....

Dirshan ya tashi ya zauna ga d’an banzan yunwar dake azalzalarsa, ko d’an sallahn nuna godiya ga mahalaccinsu da ni’imar da ya azirtasu dashi Sawwama ba bari sunyi ba ko dashike shima gogan aurenshi na fari Zulfa’u ta tarsasa masu yin sallah, dashike shima ba gwanin son sallar bane tuni ya shiga biyewa amaryarsa suka lula duniyar ma’aurata...

Tun ango na zak’ewa had’ida nuna k’warewarsa har dai ya fahimci shi jariri gaban amaryar tasa, tun yana fahimtar mai ake ciki har dai ya rasa gane da wacce yake tare amarya tasa budurwa ce ko kuwa akasin haka, a dole Hafiz ya sakarwa amarya ragamar komai ya koma sai direction d’in da tabi dashi...

Daren aurensa da Zulfah ya tuna dukda cewa a shaye ya dawo mata dare ne da bazai tab’a shafewa ba a tarihin rayuwarsa, sam babu had’i tsakanin Zulfah da Sawwama, jikin dake tsole masa idanu a waje ashe duk hotone ta gama sakwarkwacewa ko Zulfah data haihu ta shayar da d’iya jikinta yafi na amaryasa zama zamzam....

Gaba d’aya zuciyar Hafiz a cushe yake gashi bawai enjoying kasancewarsu yake ba ga uwar yunwa da gajjiya da suka kuma sauk’ar masa lokaci guda ga amarya batasan gajjiya....

Da k’yar Hafiz ya samu ya k’waci kansa kiran sallan farko ya tsarkake jikinsa ya d’auro alwala ya nufi masallaci abinda bai saba ba fita sallar asuba sai gashi a sahun farko yana jiran liman ya k’araso...

Wasu daga cikin mutanen unguwar saida abin ya d’aure masu kai, idan yaga suna dubansa saidai kawai ya kawda kai gefe don bazasu gane bala’in da ya baro a gida.....

Koda aka idar da sallar asuba kasa komawa gida yayi ala dole ya tsaya sauraren karatun bayan sallan asuba, bashi ya dawo gida ba saida gari ta soma haske, gaba d’aya jikinsa ciwo yake masa yawa an masa duka....

Cikin sand’a yake takowa tamkar mai tsoron kada wani ya jishi, a haka ya tura k’ofar parlorn ya shige sad’af-sad’af ya d’an yaye labulen k’ofar d’akin yana hangenta yanda ya hangota sai sakin minshari take ta barbaje tana bacci ko shakka babu bata gabatar da sallan asuba ba...

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yayi kafin ya dawo parlor da k’yar yake d’aga k’afafunsa da kwankwasonsa da suka masa mugun tsami ya zube saman doguwar kujera tuni bacci yayi awon gaba dashi...

Sawwama kaw tana tashi rana tsege-tsege ta shige band’aki ta jajjab’a wankanta ta fito tayi sallah a gaggauce kaman yanda ta saba, zuciyarta fari tas ta tsala wankanta ta cancad’a kwalliya ta fito parlor ta tadda Hafiz tamkar gawa sabida yanda ya sake jiki saman kujera yana baccin huce gajjiya, murmushi tai a zuciyarta tace duk yanda akai matar taka raguwace...

Batabi takanshi ba ta kunna radio sautin wak’ar marigayiya Barmani mai coge ya shiga tashi, sai tik’a rawa take tana bin wak’ar dake tashi duk iya sallaman da ake bataji ba Sahariyya ta kalli Najah kana tace “Ke bazasujimu ba mu shige kawai...”

Kai tsaye suka kutsa kai cikin parlorn sallama saman bakunansu....

Kallon arziki basu ishi Sawwama ba don ci gaba ma tai da tik’ar rawarta ta barsu nan tsaye da flask d’in abinci suna kallon ikon Allah....

Hango Yayansu kwance magashiyan saman kujera ya sanyasu kuma duban juna...

Sahariyya tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta isa gareta tana gaidata had’ida sanar da ita karin kumallo suka kawo....

Sai sannan Sawwama ta rage sautin kafin ta juyo ta dubesu a dak’ile

“Toh da kuka kawo karin sai akace sai kun sanar dani, nan ba fili bane da bazaku ajiye ba, koko dai salon ku katsewa mutun jin dad’insa inyi...,?”

Sahariyya ta kasa daina mata kallon mamaki, Najah tai k’arfin halin sakin murmushi kana tace “Wai dama Hajiya ce tace mu gaidaku mu dubo mata yaya kuka tashi....”

Batakai aya ba Sawwama tace “Toh kun gani ai garau muka tashi, yanda kukazo kuka tadda matar gidan ya tabbatar maku da hakan idan kuma ba salon gulma ce irin taku ba...”

Sahariyya ta had’iyi k’atutun bak’in ciki, a dak’ile tace da ita “K’warai munga kin tashi garau Yayan namu kuma fah munaso muji yaya ya tashi don muje mu sanar da Hajiya, sannan kud’in zuwa kawai ta bamu ba dawowa tace mu amsa wajen Yaya...” Ta k’arashe tana juya mata idanu itama....

Murmushi mai shewa Sawwama ta saki kana tace “Ke banson rashin kunya babu ubanda ya isa ya tayar min da miji lokacin tashinsa baiyi ba don haka ku wuce ku fice min a gida tunda sauran raha a fuskata, wacce ta aikoku d’in idan bata baku kud’in adaidaita ba kwa koma da k’afafunku...”

Sahariyya zatai magana Najah ta janyo hannunta tana mai girgiza mata kai alamun tai shiru kana tace “Kinga Addah mu tafi kawai...”

Sahariyya tai k’wafa kana ta janyo hannun k’anwarta suka sa kai zasu fice a dai dai lokacinda Sawwama ta janyo foodflask d’in da k’afafunta ta bud’e tai tozali da soyayyiyar k’osai nasha-nasha amaimakon wainar k’wai da kaji ko kifi kaman yanda tai tsammani hakan ya tabbatar mata flask d’in ruwan zafin da tai tsammanin ruwan shayi ne kenan ruwan kunu ne, tabd’i aiko bazata sab’u ba har sun isa veranda ta k’walla masu kira

“Kai Kai ku dawo nan....!”

A tare suka juyo suna dubanta...

Sawwama ta gyara d’aurin kallabi kana tace “Meye wannan...? Waye kuke zaton zaici maku wannan abin, ku tattara ku maida ku kawo abincin da ake baiwa amare...” Ta k’arashe tana shura masu foodflask d’in da k’afarta....

Sahariyya da tuni hak’urinta ya gaza banda huci bata komai a zuciye tayo kanta sai kuma Najah tai saurin rik’ota....

Sawwama tai tsaye tana murmushi mai kamada ki kwatanta, Najah tace “Addah Sahariyya d’auka don Allah mu tafi aka gane muna fad’a da ita dariya za’ai mana tinda ansan yanda mukeda Zulfah....”

Banda harara babu abinda Sahariyya keyi, itako Sawwama tuni ta tura k’ofar parlornta ta shige ta barsu nan tsaye da abincinsu suna iya juyo yanda ta k’ara sautin wak’arta tana ci gaba da tik’ar rawarta...

Haka suka tattari kulolin suna mamakin wane irin bacci Yaya Hafiz yake duk wannan bidiri da ake baiko motsa ba balle ya tashi...

Haka suka komo gidawa Hajiya nik’i-nik’i da sanyin gwiwa...

Hajiya tana hangosu ta fito tana washe baki tana tambyarsu yaya ankai, yaya suka sami surkarta da d’anta....

Najah ta kalli Sahariyya da tuni ta saki tsuka ta dangwal kwanon hannunta tai shigewarta d’aki...

Hajiya ta bitada kallo cikeda mamaki kana ta maido da dubantaga Najah tace “Wai juye abincin sukai suka baku kwanukan ku dawo dashi... Allah sarki kaji d’iyar albarka har wanke kwanon tai...”
Chapter 28 · 0% Book details