Sashe 177
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa magana tai, ta kasa amsasa sai hawaye dake ziraro mata, batasan ta ya zata soma fad’in abindake damunta ba, shin ta ya ma zata soma ce masa ga dalilin kukanta...? Batasan soyayya ba dan bata tab’a yi ba amma ko shakka babu ta kasa cire damuwar abinda ya faru jiya tsakanin ya Ma’aruf da Aunty Siyama... Ta rasa mai take ji cikin zuciyarta, shin tausayin Ya Ma’aruf take ko kaw tausayin Aunty Siyama take..? Shin Kodai tausayin kanta take..? Ko tsoron fuskantar k’alubalen dake gabanta take...? Tambayoyi ne da dama cikin zuciyarta da batasan ta ya zata iya amsama kanta su ba, yanayi ne cikin zuciyarta da batasan ta ya zata fasalta yanda takeji ba... Hannayensa taji saman fuskarta ya tallafo fuskar nata... Bai kuma tambayarta ba wannan karon sai saka hannunsa guda da yai ya soma share mata hawayen... Jin hannunsa saman fuskarta ya kuma sanyata sakin kuka a hankali...
Janyota cikin jikinsa yai wannan karon yana mai furta “Come here...! It’s ok.....!” Yaci gaba da lallashinta a hankali yana shafa bayanta har kukan nata ya tsagaita.... Yana iya jiyo sautin bugawan zuciyarta cikin k’irjinsa.... Yanayi mai hawahalan fasaltuwa ya tsinci kansa ciki... Yanayi ne da zai tabbatar yakan tsinci kansa ciki muddin yana tareda matarsa Siyama... Toh Maiyasa yake jin haka tareda Raihanah..? Shin son yarinyar ya fara ko kuwa dai tausayinta yake har yanzu...? Shi kansa baida wannan amsa... Yanajin sanda take mutsu mutsun cire jikinta Daga nasa, a hankali ya d’an d’agota sassanyar murmushi saman fuskarsa...
“Feeling better..?” Ya tambaya yana dubanta...
Ba tareda ta dubesa ba sabida tsananin kunyarsa da takeji, ta jinjina masa kai a hankali... mik’ar dasu tsaye yai a tare kana yace bari yaje yaga Daddy....
Ta jinjina masa kai a hankali har lokacin fuskarta a k’asa tana mai share ragowar hawayen idanunta...
Har ya soma tafiya ya sinkayo Muryarta tana fad’in “Yaya...!”
Juyowa yai yana dubanta... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Dan Allah ka yafewa Aunty Siyama kaji....!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya....
Jim yai yana dubanta, lokaci guda annurin fuskarsa ya d’auke... A hankali ya tako zuwa gabanta kana ya kuma kamo hannunta suka zauna saman kujera...
“Wannan dalilin da yasaki kuka...?”
Shiru bata amsasa ba...
Ya d’an kauda kai gefe kad’an had’ida fuzar da huci a hankali.... Karkatowa ya kumayi yana dubanta kana yace “Raihaan bana son ki sake min zancen Siyama kinji koh....!”
Yanda Yai maganar ya sanyata d’agowa tana dubansa... Sadda idanunta tai kana tace cikin sanyin murya “Kai d’in zuciyarka mai yawan afuwa ne... Kuma idan har zaka yafewa Baba Alhaji da Hajiya dik abubuwan da sukai maka, mai yasa bazaka yafewa Aunty Siyama ba....? Aunty Siyama tana k’aunarka kuma ta gane kuskurenta dan Allah ka yafe mata... Dik d’an adam ajizi ne Yaya... Please ka yafe mata kaji... And... and everybody deserves a second chance..!”
Yai k’uri yana dubanta kana ya kuma fuzar da fuci a hankali.... Hannunta guda ya kamo cikin nasa kana yace “I’ll think about it....!”
Daga haka mik’ewa yai yana duba agogon hannunsa kana yace bara yaga Daddy.... Ta jinjina masa kai har ya fice.... A hankali ta mik’e had’ida sauk’e ajiyan zuciya kana ta shiga tattare masa d’akin...
A can parlor Sameer ya iske Daddy da Mummy da alama isowarsa suke jira... Daga can saman carpet ya zauna had’ida gaida Iyayen nasa... Suka amsa cikeda sakin fuska dikda tausayin d’an nasu da ya cika zukatansu... Daddy ya d’an bud’e murya yace “Doc an fito...?”
Sameer ya jinjina kai yana k’ok’arin k’ak’aro murmushi “Eh Daddy... Allah sa dai bamu makara ba...?”
Daddy ya girgiza kai kad’an “No aima inaga tafiyar nan mu barta har zuwa gobe idan Allah ya nufa zamu kai... D’azu mukai magana da Uncle d’in naka, jikin nashi da sauk’i Alhamdulillah, so yace mu barshi ma fito gobe kawai idan Allah ya nufa...”
Sameer ya jinjina kai yana hamdala da jin cewa jikin Daddyn Siyaam da sauk’i sosai... Daddy ya kuma katsesa da fad’in “Sameer dama akwai maganar da nakeso mu tattauna...”
Jin haka yasa Mummy mik’ewa ta basu waje...
Sameer ya gyara zamansa gaban Daddy yana mai furta “Alright Daddy..”
Lokaci guda yaci gaba da fad’in “About your wife Siyama... Mummynka ta sanar dani komai, abu baiyi dad’i ba amma babu yanda muka iya da hukuncin ubangiji.... Nima dai hak’urin zan baka Sameer... Kai hak’uri, ka yafewa matarka ka kuma had’e kan iyalanka... Siyama tana cikin wane yanayi na tashin hankali duba da halinda mahaifinta ya tsinci kansa cikin, kai hak’uri ka tausasi zuciyarka kaji ko...Wannan shine girman..... Yanzu yau mun bar maganan tafiyar, kaje ka sami iyalinka ba sai kowa ya shiga maganar ba, ku sasanta kanku idan yaso in Allah ya kaimu goben sai mu tafi Abujan gaba d’aya...”
Idanunsa a k’asa yake jinjina kai kana yace “In sha Allah Daddy... Zanyi yanda kace..”
Daddy ya murmusa kana yace “Allah shi maka Albarka....Tashi kaje..”
Ya kuma risnawa had’ida amsa Daddy, lokaci Dad d’in Ke cewa “Kace da Mummyn naka ta kawo min maganin...”
Sameer ya amsa da toh Daddy kana ya shige...
***
Tana duk’unk’une waje guda a parlorn sabida tsananin ciwo da kanta ke mata ta kuma sinkayan ringing d’in wayarta, wannan karon d’an uwanta Khalid ne mai kira... Take taji sabbin hawaye na zuwa mata... Ta d’aga da k’yar Murya a matuk’ar sanyaye....Jin yanayinta ya sanyaya masa jiki dikda albishir mai dad’i da yake shirin sanar mata....
Mik’ewa tsaye yai cikeda kulawa... Lokaci guda yake furta “Siyama what’s wrong...? Where are you...Siyama meke faruwa...?”
Lokaci guda ta fashe mashi da kuka tana mai furta “Khalid... Partner... Khalid Sameer yayi aure... Partner yayi aure Khalid.... Sameer bai k’aunata... Yayi fushi dani Khalid, ya samu madadina....!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka...
Shafe goshinsa kad’an Khalid yai cikeda tashin hankali dan dama yasan hakan ka iya faruwa muddin labarin auren Sameer ya isaga ‘iyar uwar tasa....
Cikin kwantarda hankali yake furta “Siyama listen to me, just calm down kinji....!”
Cikin kuka take ceda Khalid “How could you expect me to calm down Khalid, ko bakaji mai nake ce maka bane.... Sameer yai aure... Aure fah yai Khalid... He doesn’t care about me anymore....!”
Khalid yace “Siyama Sameer na sonki dan yayi aure doesn’t mean ya daina sonki, Ki kwantar da hankalinki kinji...”
Girgiza kai kurum take tamkar Khalid d’in na ganinta tana mai ci gaba da goge hawayenta take fad’in “Khalid please tell me.... Am I really a bad person... Why is all this happening...? First it was Daddy and now Sameer... Khalid this isn’t fair... It is not fair..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka wanda ya kuma raunana zuciyar Khalid... Cikeda tausayin ‘iyar uwar tasa yake furta “Siyama... Sis, please listen to me... Ki daina kuka kinji....!”
Shiru ya d’an biyo baya sai sautin ajiyan zuciyar Siyama... Khalid yaci gaba da fad’i cikin kwantar da hankali “Siyama... Some times in life, we just have to accept things the way they’re... Ba komai muke samu yanda muke so ba, bazai yuwu mu samu komai yanda muke so ba Siyama... Some times dole muyi hak’uri mu karb’i k’addara a yanda tazo mana...So we just learn to let go and move on.... Please stop stressing yourself out Siyama...!” Ya k’arashe cikeda kulawa yana mai furta “So tell me, where are you now...?”
Ta kuma share hawayenta kana tace “Kaduna... But I’m leaving now...Its pointless staying here, after all....!” Ta d’an fuzar da iska kad’an tana gathering strength d’inta kana tace “How’s Daddy doing... Ya jikin nasa...?”
Khalid yace “Daddy is doing better, in fact he’s out coma...”
Hamdala taji bakinta na furta murmushi saman fuskarta dikda hawaye dake ci gaba da gangaro mata...Ta k’arada... “And Ammi... How’s she.. How are things there...?”
D’an numfasawa yai kana yace. “Things turned out the way we least expected... But komai lafia...!”
Jinjina kai take tana mai ci gaba da shiri take fad’in “Zan d’auki hanya yanzu in sha Allah...”
Cikin sauri Khalid ya katseta “Wait... Wane hanya kike magana...?”
Tana mai ci gaba da abinda take tace “Abuja of course...!”
Girgiza kai Khalid yai kana yace “A’a Siyama, a halinda kike ciki you cannot drive.... Kiyi hak’uri har zuwa gobe sai ki biyo train... A halinda kike ciki you can’t even travel Siyama...!”
Dafe kanta dake tsananin sarawa tai kana tace “Kar ka damu bro zan iya... Just pray for me kaji... I love you...!!” Daga haka bata kuma jiran cewarsa ba ta katse kiran Khalid na fad’in “Siyama.. Siyama please...!” D’if yaji ta katse kiran....
Nabilah ce ta k’araso nan garden d’in da yake tsaye cikin asibitin.... Ganin yanayinsa ya d’an tada mata hankali.... Tambayarsa tai meke faruwa...?
Ya d’an fuzar da iska kad’an kana yace “Siyama ce.... Bazai yuwu na barta ta d’auki hanya a halinda take ciki yanzu ba.... I need to call Sameer, he’s the only person that can stop her right now...!”Ya k’arashe yana dialing layin Sameer, gaba d’aya kallo guda zaka masa ka fahimci a tsananin birkice yake... Allah sarki d’an uwa ya wuce wasa....
Nabilah tai zaune tana duban yanda ya manne waya a kunnensa sai safa da marwa yake yana jiran Sameer ya d’aga wayarsa....
“Come on Sameer, pick up your phone...!” Sai faman nanata hakan yake... Kira na biyu a na uku Sameer ya d’aga.... Ko gaisuwa Khalid bai tsaya ba ya shiga sanar dashi halinda ake ciki...
Shima Sameer d’in bai wata wata ba ya katse kiran yace gidan ya nufa, zai dakatar da ita....
Hakan yasa Khalid samun relief sosai...
Sameer kaw gudu ya dingayi bisa kwalta, yana isa gidan ya fad’a ciki yana doka mata kira “Siyama..! Siyama..! Partner..!! Where are you... Siyama...!!” Haka ya dingabi k’ofofin gidan yana dubata... Saida ya shiga d’akin baccinsu ya hangi hotonsu kife saman gado alamun tareda hoton tai bacci... Girgiza kai Sameer yai a hankali kana ya fice babu shiri dan ga dikkan alamu Ta riga ta fice daga gidan....
Wayarta ya soma k’ok’arin kira saidai sam bata d’agawa, k’arashe ma katse kiran take....