← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 198

Sashe 124

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffah da Baba Ali sun zaga ko ina sun kuma gaisa da dangi, hartada Mamani saida suka shiga suka gaisheta, Baba Ali ya sami Mamani sukaita zabga zance har sai yaji kaman kar su tafi, dan ko babu komai Mamani ta skashi nishad’i hali yazo d’aya... Hartadasu sashen Baffah Wada da sauransu duk sun shiga sunyi gaisuwa...Daidai da gidan Baba Alhaji saida sukaje... Saidai Sameer bai masu rakiya ba don tinda ya masu jagora zuwa cikin gidansu yai ficewarsa shima, Aamiru d’an gidan Baffah Ado shi ya zazzaga dasu sauran wajajen... Kasancewar Nabilah na makaranta shiyasa ma basu had’uda ita ba, gidan Aunty Bara’atu sukaje daga k’arshe yanda suka sanar da ita mak’asudin zuwan nasu gashi basu sami Nabilah ba kuma ance yini zatai a makaranta...
Aunty Bara’atu tasan yanda Nabilah ta d’auki zancen auren nan, kuma Daula ta sanar da ita duk shirin mahaifin Khalid, bata tantama turo abokan Khalid d’in da Daddy yai nada nasaba da shirye shiryensa... Dan haka bata b’oyema Baffa komai ba sanin cewa ta riga tasan shirin Daddy, kuma yanzu idan sukace zasuga Nabilah wani rikicin zasu kuma b’allowa domin kaw sosai Nabilar Ke fushi da Khalid... Duk wasu shirye shirye daga bakin Aunty Bara’atu suka samu suka kuma dank’a mata sak’on Daddy, da fari k’in amsa tai a cewarta basai Daddy yayi haka ba... Baffah yace wannan ai na amaryace kuma dama ko wacce amarya anai mata hakan... Zaiso su gana da Nabilah amma saidai goben fitar sassafe zasuyi, Aunty B tace kar ya damu zata tura masa layin k’awar Nabilar Yusra idan duk da abinda zasu tattauna sai ya dinga communicating da Yusran... Sosai hakan yaiwa Baffah, Har ransa yake jin karamci irin na Aunty Bara’atu, kuma ya yarda Khalid gidan Dattako yazo..
***

A b’angaren Akram kaw tinda suka komo daga campaign hankalinsa ya gaza kwanciya, ya k’agu ya had’uda Yusuf yaji yanda ya kaya masa da bak’in gidan Engr... Ga mahaifiyarsa data tsaresa da wasu tambayoyi had’ida tuhuma...
“Akram ni tinda ka k’irgo kawunanka a masu zuwa nema maka aure babu Gwamna mai jiran gado ciki zuciyata Ke fad’amin wani abin... Akram anya kuwa...? Wane irin aure ne wannan zakace ko gayya da yawa bakaso ayi, shifa aure d’an shela ne ba b’oye b’oye... Ka fad’a min mai kake b’oyewa Akram ni mahaifiyarka ce....”
Shafa sumarsa yai a hankali kana yace “Umma ni babu abinda nake b’oyewa, kuma abinda yasa ban saka his Excellency a masu zuwa tambayamin aure ba sabida shine zaije ya amsa min auren, kinga bai kamata na d’aura masa d’awainiya da yawa ba, kuma Umma wane gayya za’ai tinda ita Zulfa’un ita tace batason babban buki...Babu yanda banyi da ita ba amma sai ce min tai wannan ba aurenta na fari ba kenan dan haka ita batason a kambaba Bikin, ni babu wani abinda nake b’oye miki Umma ki yarda dani....”

Numfasawa tai kana tace “Shikenan tinda kace haka, biki naka ne kaida ita sai yanda kuka tsara abinku... Amma ka tabbata Gwamna shine Wakilinka...Dan sanin kanka ne shid’in tamkar uba ne a wajenka... Tin bayan rasa mahaifinka babu wanda yai d’awainiya dakai da danginka sama dashi, toh kada kayi wasa da amana... Har kullum wasiyyata a gareka kenan...”
Jinjina kai yai dikda k’irjinsa dake tsananin bugu kana yace “In sha Allahu Umma, na miki alk’awari Excellency shi zai karb’a min aure...”
“Shikenan tashi kaje, Allah shi maka albarka ya kuma dafa maka...”
Ameen Umma ya amsa dashi kana ya mik’e ya fice yana neman layin Yusuf...

Koda suka had’uda Yusuf yasha mamakin jin cewa masu neman auren k’anwar Zulfa’u ne wad’ancan d’in... Toh ko mai ya had’asu da Engr..??? Wannan tambayarce shi kansa Yusuf d’in bai sani ba shima...

***

A can Abuja kuwa Khalid da ‘yan uwansa lullub’e suke cikeda Farin ciki, sosai sukai murnan zuwansa, baga Aunty Daula ba baga yaranta ba... Shi kanshi Khalid d’in bazai k’arya ta cewa dik sanda yake taredasu yakan tsinci kanshi cikin Farin ciki, yana samun farin ciki a tattaredasu wanda ya rasa daga nashi ‘yanuwan da sukafi kusanci dashi... Wani rayuwa yake experiencing wanda baiyi ba a baya, rayuwace da ‘yanuwa Ke k’aunar juna suka kuma damu da damuwar juna, where everybody’s opinion matters... Ba irin rayuwar gidansu ba da ba’ayin abu sai idan abinda wanda sukeda k’arfin iko ne suka fad’i, ba kuma a d’aukan shawarin kowa da mahimmanci sai nasu...
Ya kuma sakin murmushi yana duban yanda yaran keta tsalle kowacce tana fad’in saidai yaci abinda suka tarbesa dashi, dangin chocolates ne da kayan mak’ulashe, abinka da yaro...
Aunty Daula ta shige tsakiyan yaran tana fad’in “Toh a k’yale Yaya ya huta, kunga bai jima da isowa ba...”
Khalid na murmushi yace “No it’s ok Aunty... Nayi kewarsu nima ...” Ya kamo hannayensu yana amsar kyautukansu d’aya bayan d’aya yana nuna Farin cikinsa... Lokaci guda shima yake dank’a masu nasa tsaraban da yayo masu... Haba nan fah suka kuma shagala da murna da farin ciki, wata irin k’aunace tsakanin Khalid da yaran... Aunty Daula dai k’yalesu tai ta tafi kitchen dan ci gaba da shirya masu dinner d’in tareda taimakon mai aikinta Karima....

Da dare bayan sun ida cin abinci take tanbayarsa mutan gidan su Ammi da Siyama, Khalid yace duk lafiya suke...
Yanda yai maganar tamkar mai d’aukeda damuwa, dan ta kula tinda yaran suka bar parlorn suka nufi b’angaren karatu dan yin homework d’insu yanayin Khalid d’in ya canza sosai tamkar wanda yai nisa cikin tunani...
D’an gyara zamanta tai tana mai karantarsa kana tace “Problem..?”
Murmusawa yai a hankali ba tareda yace komai ba...
Muskutawa ta kumayi kana tace “Kaman kayi nisa cikin tunani tunda yaran suka tashi... Akwai matsala ne..? Ko akwai abinda kake so ne...?”
Murmusawa ya kumayi had’ida d’an fuzar da siririyar iska kana yace “It’s about my Dad, he’s been acting strange lately.... Inaji kaman akwai abinda yake b’oyemin... Like he’s up to something.. Na kasa gane mai yake shiryawa... Da fari yamin introducing d’inku abinda ya kasa yi tsawon shekarun nan, kwatsam yanzu yaji ya had’ani daku... Na biyu wani sabo da kirki na musamman na shiga tsakaninsa da abokaina, and now kwatsam ya sakani kular masa da gyaran gidansa na nan Gwarimpa har yana tambayar ra’ayina.... Wad’Annan abubuwan sun d’aure min kai.... Like, what is he planning..? Could it be aurena da Yesmin suke shiryawa ba tareda sanina ba shida Ammi... I know my Dad nasan yanda yakejin maganar Ammi, kuma na sani yanda Ammi tai niyyan had’a aurena da d’iyar sister d’inta toh fah sai tayi... And shi kuma Daddy abinda tace shi zaiyi.... Idan hakan ta kasance da gaske I don’t know... Ban sani ba ko inada k’arfin hak’urin da zan iya jurewa nai masu biyayya...” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa...

Numfasawa Aunty Daula tai cikeda tausayinsa kana tace “Toh kai baka son zab’insu ne...?”
D’agowa yai ya d’an dubeta kad’an kana yace “I’ll be honest with you Aunty... Yesmin ‘yar uwatace, toh zaifi kyau idan ta tsaya a matsayinta na ‘yar uwata... Amma any other relationship aside from wannan bazai tab’a yuwa ba tsakaninmu....”

Numfasawa kad’an Aunty Daula ta kumayi kana ya ambato sunansa...
Wannan karon ma d’an duban nata yai

“Ka yarda da mahaifinka....?”
Ya jinjina mata kai a hankali...
“Ka yarda bazai maka abinda zai cutar dakai ba....?”
Shiru yai wannan karon tamkar mai nazari kana yace “Na yarda...” Yai maganar cikin murya mai rauni....

Jinjina kai Aunty Daula tai kana tace “Wasu lokutan iyaye sukan hanga mana abinda yafi kyau da dacewa a garemu... Ko yaya ne believe me babu iyayenda zasuso suga ‘ya’yansu ba cikin Farin ciki ba, shiyasa wasu lokutan idan sun mana zab’i sai muga kaman sunyi katsalandan ma rayuwarmu ne ko suna nuna k’arfin ikonsu akanmu ne, Toh ba haka bane tsaban soyayyace da suke mana wanda su a nasu Ganin akwai abinda suka hango wanda mu ba lallai mu hango ba... Khalid Iyayenka suna sonka suna kuma k’aunarka, saidai su irin nasu hanyar da zasu nuna maka nasu k’aunar kenan... Never kada ka tab’a doubting wannan... Sannan a koda yaushe dik yanda kakai da son abu toh ka nemi zab’in Allah ciki sai Kaga nasara, farin ciki da kwanciyar hankali wanda bakai tsammanin samu ciki ba...”
Khalid da zuciyarsa tai matuk’ar masa sanyi da jawaban Aunty Daula, samun kansa yai yana mai jinjina mata kai kana yace “Hak’ik’a naji dad’in shawarwarinki gareni Aunty... Kuma kaman yanda kikace zab’in Allah is always the best... Na gode k’warai for listening to me, and also for your kind advice...”
Aunty Daula ta murmusa kana tace “Babu komai, this is what family are for after all... Yanzu yaushe zakaje duba gidan...?”
D’an numfasawa ya d’anyi kad’an kana yace “Gobe nake son lek’awa in sha Allah, dan already tin ina kaduna nayi magana da wani company.. So idan naje naga yanayin aikin sai a soma right away...”
Jinjina masa kai ta d’anyi kana tace “Shikenan idan ka dawo goben sai ka kaimu shopping together with the kids, I’m sure that will be fun....”
Khalid ya murmusa yace “An gama Aunty na...”
Itama murmushin tai daidai sanda yaran suka shigo parlorn rik’eda littafansu da suka ida homework ciki...

Washe gari sosai sukaji dad’in fita shopping gaba d’ayansu, malls da dama suka dinga zagyawa Aunty Daula na jidan kaya abin har ya soma baiwa Khalid mamaki tamkar wata mai had’a lefe irin kayan da take jida, sannan akasarin kayan sai ta tambayi ra’ayinsa take d’auka ko kuma idan ta kula ya k’urama wasu kayan idanu Toh su take zab’a.... Shi dai bai kawo komai ba, dik cikin kirkinta ne da girmama opinion d’in duk wanda take taredasu ya d’auki Hakan....
Basu dawo gida ba saida ta tabbata rabin kayan da zasu zuba a lefe choice d’in Khalid ne....
Wani Sabo na musamman na kuma shiga tsakaninsu gaba d’aya, sosai yak’e ganin girman Matar Baban nashi dikda a zahiri baifi ta k’ere masa da wasu shekaru k’alilan ba... K’annensa kaw jinsu yake tamkar ciki d’aya suka fito, basuda maraba da Siyama a wajensa...

A b’angaren Ammi kaw bata damu dan Khalid d’in na Kaduna ba don ita dik tinaninta hakan na cikin shirin Daddy ne na aurawa Khalid Yesmin...

***
Chapter 124 · 0% Book details