← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 198

Sashe 132

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mamaki ya cika Daddy ganin Engr na kutso kai cikin parlorn, mutane kaw sai faman bud’a masa suke, Jalo na biye dashi har suka isa mazaunin su Abbah suka zauna suna masu yi masu masabaha.... Mutane kaw sai k’asa k’asa da murya suke suna ambato sunan Engr suna fad’in shid’in ne dai da gaske, abinka da sanannen d’an siyasa....Marok’a kaw tuni suka soma wasa shi suna fad’in Alkhairansa.... Mamaki ya cika Abbah dikda cewa shi d’in ba ma’aboci siyasa bane yasan Engr Ma’aruf Mutallab matsayinsa na d’an takaran gwamanan jiha da yai fice, kuma ko shakka baiyi sanda Mahaifin Khalid yazo nemawa Khalid d’in auren Nabilah tare sukazo da shi Engr d’in... Toh amma abinda bai gane ba... Shin dama Engr Mutallab yanada alak’a da mai neman auren Zulfa’u ne...? Wannan tambaya shi yaketa yawo a kwanyar Abbah, gaba d’ai ya gaza fahimtar meke faruwa har saida ya sinkayo muryar Baffah Wada yana tambayar Engr
“Rankashi dad’e shin kune masu amsar auren Zulfa’u....?”
Murya a dake Engr yace “K’warai mune....”
Baffah Ado yace “Toh ai sai aci gaba da gudanar da d’aurin aure....”
Hafiz da jikinsa Ke tsananin karkarwa had’ida tsuma cikin sauri ya katsesu da fad’in “Ta ya za’a aura mata mutumin da ya b’oye kanshi ya kasa bayyana kanshi... Baffah kar azo ai auren da za’azo ana danasani a baya....”
A zuciye Baffah Ado ya mik’e yana nuna Hafiz da d’an yatsa yake fad’in “Kai Hafizu wllhi billahilAzim idan baka shiga taitayinka a wajen nan ba zan maka rungumar buhun dawa na fiddaka da k’arfin gaske, ka shiga hankalinka tin wuri ka daina maida mutane k’anan mutanen... Cikinmu babu sa’anka....”
Hafiz yaci gaba da huci yana rarraba idanu ga gumi dake keto masa.....

Baffah Wada ya dubi Engr yace “Kuyi hak’uri d’an yau ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, Malam Imam muci gaba da abinda ya taramu.... Imam ya jinjina kai, yana mai kuma tambayar Baffah Wada wanda shine Alwalin Zulfa’u... Yana k’ok’arin tambayar Engr kenan sukaji wata murya tana fad’in “Ku dakata...!”

Gabaki d’aya juyowa sukai suna dubanta, mahaifiyar Akram ce sai Yusuf da Kawunan Akram guda biyu da sukazo suka tambaya masa auren Zulfah....
Mamaki ya kuma cika mutanen parlorn, wannan wane irin al’amari ne.... Aka bada hanya ma Umma da tawagarta suka shige....
Baffah Wada yace kece wace...?”
Umma tace “Ni ce Mahaifiyar Akram... Wad’annan da kake gani k’annena ne kuma su sukazo suka tambayawa Akram auren Zulfa’u...”
Kawu Jafaru yace “Tabbas mu mukazo muka tambaya mashi auren Zulfa’u... Amma kwana biyu da suka shige yazo ya sameni ya sanardani yana so ranar aurensa sadakin da ya bayar da sunan aurensa da Zulfa’u ya juya ya zama sadakin Ubangidansa yana so auren ya tashi daga kanshi ya koma kan Ubangidansa Engr Ma’aruf Mutallab... Koda na tmbayeshi dalili sai cemin yai na mishi wannan alfarmar mai yuwa zai iya tafiya wani waje mai nisa a wannan ranar dan bazai iya fuskantar Ubangidan nashi ba....”
Umma ta k’arada “A kwanakin nan d’ah na Akram ya sauya k’warai, babu yanda banyi ba ya sanar dani abinda ke faruwa musamman tsakaninsa da Gwamnan gobe.... Sai bayan da muka nemeshi muka rasa Yusuf abokinsa ya sanar damu komai, ya sanar damu cewa Gwamnan mai jiran gado shine asalin manemin wannan yarinya Zulfa’u, kuma tabbas ya wakilta d’ah na Akram yai masa jagoranci ne... Ina mai rok’onku da ku baiwa wannan bawan Allah auren d’iyarku shid’in mutumin kirki ne....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye suna gangro mata....
Girgiza kai Engr yai kana yace “Ummah ki barni na karb’awa Akram aurenta ni mai iya sadaukar masa da komai ne....”
Girgiza kai Ummah take ta kuma had’e hannayenta waje guda tana fad’in “Kai d’in kai kafi kowa cancanta ka zama mijinta... Gwamana dan Allah kabi wasiyyar Akram ka amsawa kanka auren Zulfa’u a yanzu... Na rok’eka....” Ta k’arashe tana hawaye...
Daddy yai saurin dafa hannayen Engr yana mai sakar masa murmushi yake fad’in “Kai d’in mutumin kirki ne, mutumin arziki ne da kowa yai maka shaida ta k’warai...Wanda kowa zaiso had’a zuri’a dakai....”Daddy ya kuma kai hannunsa kan na Abbah da ya koma tamkar gunki yana kallon wannan ikon Allah lokaci guda Daddy yaci gaba da fad’in “Alhaji Usman ka bani dama na tambaya kuma na karb’awa K’anina Ma’aruf auren d’iyarka.... Shi d’in mutumin kirki ne... Kar ka mance fad’in ma’aiki ne... Idan na gari yazo neman auren d’iyarku toh ku bada, rashin bayarwan ka iya haifar da fitina... Alhj Usman ni Engr. Ahmad Madi Mailafiya Ina tambayawa K’anina Engr. Ma’aruf Mutallab Maidala auren d’iyarka Zulfa’u... Shin ka bashi a d’aura auren yanzu...?”
D’agowa Abbah yai yana dubansa yayinda Hafiz Ke faman girgiza kai yana adu’an yaji kalmar a’a daga bakin Abbah... Su Baffah Wada Baffah Ado da sauran jama’an wajen dake fatan amasar Abbah ta zamto eh gaba d’aya tsit parlorn tai ana jiran amsar Abbah.... Maida dubansaga Engr Abbah yai, dikda cewa Engr ya kasance sanannen d’ansiyasa amma baisan dalili ba sosai mutumin ya kwanta masa a rai tintini dukda cewa shi d’in bai kasance mai hidima da ‘yan siyasa ba.... Fuska a murtuk’e Abbah ke duban Engr kana ya soma fad’in “You take care of my daughter... Ka kular min da d’iyata... Itad’in ta kasance d’iya mai biyayya, kuma taga iftila’i da yawa na rayuwa... Ta cancanci Farin ciki....”

Jin abin yake tamkar a mafarki... Allah ya isa buwayi kuma gagari misali... Tabbas shid’in shine mai sauya al’amara a lokacinda yaso ya kuma ga dama... Yazo nan wajen da niyyan amsawa Akram auren Zulfa’u ne sai gashi aure ya tashi daga kan Akram ya koma kansa... Shin waye ya isa ya juya wannan idan ba mai mulkin sama da k’asa ba... Lokaci guda Engr yake fad’iwa Abbah “Nayi maka alk’awarin d’iyarka bazatai kuka ba in sha Allah... Zan knaunaceta da duka zuciyata dan dama tuntuni zuciyar mai k’aunarta ne, mai k’aunar sauraren muryarta ne.... Ni Engr Ma’aruf Mutallab Maidala nayi maka alk’awarin kular maka da d’iyarka har k’arshen numfashi na....”
Haba nan fah parlor ya kacame da farin ciki, wane ikon Allah harta mutanen da basu San kan labarin ba irinsu Khalid sai abin yai matuk’ar burgesu... Farin ciki da annuri ya cika fuskokin mutanen... Take Engr ya wakilta Daddy ya amsa masa auren Zulfa’u... Ikon Allah kenan, Daddy ya taho Kano da niyyar amsawa d’ansa Khalid aure sai gashi ya amshi aure biyu, wannan abin farin ciki da yawa yake... Nan fah Hafiz yaji duniyar tana juya masa... Babbar rigarma baisan sanda ya cire yayi wurgi da ita ba, ji yake tamkar ya k’arasa ya shak’o wuyan Engr saidai bodyguards d’insa guda biyu kawai sun isa suyi watandan Hafiz...Al’ajabi ya cika illahirin jama’an dake wajen, nan fah hargowa da kacaniya ya kacame tsakanin Al’umma tuni labari ya famtsama cikin gida, ga kuma wani k’ishin k’ishin da sukeji cewa auren Sameer bada Sahariyya aka d’aura ba, da k’anwarta aka d’aura dan haka kowa sai cewa yake da Naja’atu aka d’aura auren Yaya Ma’aruf....
Tinda Hafiz yasa kai ya fice babu wanda yaga koda wulk’awarsa, Magaji sai sauri yake ya samu ya cimmasa kafin yai wani abinda zai janyo masa kwanan police station tinda yasan idan yayi haukarsawa Akram yasha bazai wa Babban mutum kaman Engr yasha ba...

Shiko Khalid tinda suka fito daga taron d’aurin auren ya tsare Baffah da tambayoyi...
Baffah na k’ek’yata dariya yake fad’in “Haba ango dika wad’annan tambayoyin ta ina zan soma amsa su... Kaga muje chines restaurant ka shirya mana gajeriyar liyafa, Ko ya kukace guys....?” Ya k’arashe yana duban su Misbahu.....
Baba Ali yace “Nidai dik ba wannan ba, tinda yak’in neman auren nan dani akai, ya kamata a kaini naga amaryar nan kafin na bar garin nan...”

Baffah ya dangwari k’eyar Baba Ali yana fad’in “Toh Sarkin ‘yan magana, fad’a masa dakai akai yak’in neman aurensa...”
Baba Ali yace “Yo ba gaskiya nake fad’i ba... Kaga da Allah muje nasan shi kanshi angon ya matsu baiga amaryar sa ba... Dole na bata labarin gwagwarmayar neman aurenta da aka sha taredamu....”
Murmusawa kurum Khalid yake dan shi kanshi sosai yake son ya sakata a idanunsa... Yusrah Baffah ya kirawo ta sanar dashi suna can gwammaja gidan Aunty Bara’atu, dashike Baffah yasan gidan sabida lokacinda sukazo sunje har gidan wajen Aunty Bara’atu babu wani b’ata lokaci yai jagoranciwa abokan nasu... Khalid gaba d’aya ganin abubuwan da suke kan faruwa yake tamkar a mafarki....
Tuni Aunty B tasa an kuma gyare masu parlorn waje, ga tarban abinci na musamman da aka jere masu, saida suka biya masallacin gefen gidan suka gabatar da sallar azahar kana suka k’araso gidan...
Ita kaw Nabilah tinda aka sanar da ita an d’aura aurenta take kuka tamkar ranta zai fice, gaba d’aya haka ta duk’unk’une cikin farar laffayan da aka d’aura mata tana zabga kuka wanda ita kanta batasan na menene bane. Shin na farin ciki ne ko kuwa akasin Farin ciki.... Shin anya mijin da aka aura mata mai k’aunarta ne... Idan yana k’aunarta maiyasa har rana ta yau ranar d’aurin aurensu bata saka shi a idanunta ba bataji daga gareshi ba... Shin menene makomar aurenta....?”
Chapter 132 · 0% Book details