Sashe 119
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hafiz dake huci ya jinjina kai yace “Na maki alk’awari muddin kika cika mun burina ni Hafiz bazan kuma k’yaleki ba...”
Nan ma dai murmushin tai tana mai shafa fuskarsa da duka tafukan hannayenta, lokaci guda ta mik’e had’ida basa baya...
Cikin dakekkiyar murya take fad’in “Zan taimaka maka kuma Zulfa’u zata dawo gareka...”
Mik’ewa tsaye Hafiz yai ya tako kad’an har zuwa gabanta.... Lokaci guda yake sakar mata murmushi, itama d’in murmushin take sakar masa... Hannu yasa ya kamo k’ugunta ya matsota kusansa.... Fuskarsu dab da juna yake furta “Ni d’in naki ne sai yanda kikai dani.....”
Tamkar zakin da ya kwana babu abinci haka ta janyo Hafiz ta shiga sarrafasa....
SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_
*83*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A haka sati guda ta shud’e, ta ko wanne b’angare shirye shiryen bikin suke... Tabbas dik abinda aka masa lokaci INDA RAI zaizosa, zaune Aunty Daula tai bayan ta ida waya da Nabilah da kuma Aunty B... Ita kad’ai sai sakin murmushi take tana jinjina hankali irin na Nabilah, babu yanda batai ba ta sanar da ita abubuwan da take so a zuba mata a kayan lefe amma fir Nabilah tak’i sanar da ita... Tabbas Khalid yayi dace, gaba d’aya lokaci guda k’aunar Nabilah da danginta ya ratsa zuciyarta, ta k’agu ranan biki yazo su had’u suga juna... Tana nan a haka wayar Daddy ya shigo mata, tambayarta shiryen shiryen yai shima kana suka d’an tattauna batun dan lokaci bai jira... Abu kaman wasa gashi yanzu satittika ake k’irgawa....
Yana ida wayar Baffah yai sallama a k’ofa, Daddy ya amsa had’ida masa izinin shigowa... Cikeda risinawa Baffah ya k’arasa saman tampatsetsen carpet d’in turkey dake malale a wargajejen parlorn ya zauna daga can gefen Daddyn, Daddy ya mik’a masa hannu sukai masabaha kana Baffah ya gaida Daddyn cikeda girmamawa....
Daidaita zamansa Daddy yai saman d’aya daga cikin kujerun alfarma da sukaiwa parlorn nasa k’awanya....
“Baffah..” Daddy yace had’ida yin gyaran murya..
Baffah ya amsa cikeda fargaban wannan kira na gaggawa da Daddyn yai masa....
“Nasan zakaji mamakin nemanka cikin sauri da nai lokaci guda....”
Jinjina kai Baffah yai a hankali kana yace “Haka ne Daddy...”
Daddy ma ya jinjina nasa kan “Abinda yasa na nemeka cikin gaggawa ba komai bane illa sanin cewa da nayi Khalid baida aminin da ya wuceka....”
Baffah ya kuma jinjina kai yana tinanin mai kuma Khalid d’in yai wannan karon...
Daddy ya d’an murmusa ganin gaba d’aya kaman Baffan a tsure yake kana yace “Ka kwantar da hankalinka abokinka baiyi komai ba, hasalima ma baisan abindake gudana ba....” Fasali ya d’anja kafin ya zaro checkbook dake aje saman k’aramar table d’in dake gefen kujeransa.... B’allan guda yai kana yayi rubutu jiki ya mik’awa Baffah....
Baffah yabi check d’in da duban mamaki “Daddy na menene...?” Ya tambaya yana kuma juya takardan...
Gyara zama Daddy yai kana yace “Inaso kaje Kano ka sami Nabila a madadin Khalid, nasan ango yakan baiwa amaryarsa wasu ‘yan kud’ad’e kodai na events ko wasu hidiman gabanta dan ba’a raba mata da hidima....” Gaba d’aya Daddy sai ya kuma d’aure kan Baffah... Shi gaba d’aya ma sai ya rasa wacece ma Nabilah... Daddy ya d’an murmusa kad’an kana yace “Na sakaka a duhu koh... Toh karka damu bari na fayyace maka komai da kuma dik wani shirina... Ina kuma fatan na sami goyon bayanka d’ari bisa d’ari a matsayinka na aminin d’ah na....”
Dikda Baffah baisan shirin Daddyn ba amma sai ya sami kansa da jinjina mar kai yana mai furta “Zaka sameni mai yi maka biyayya da bin umarninka in sha Allah Daddy....”
Daddy yaji dad’i sosai ya jinjina kai yana furta “Shiyasa ban tab’a danasanin kasancewarka abokin d’ah na ba dan nasan kaid’in yaron arziki ne..”
Mugun sanyi jikin Baffah yai ko da Daddy ya karanto masa shirinsa na auren Khalid d’in taryan taryan, ya tina kwanakin baya yanda ya baiwa Ammi da Siyama full support d’insa wajen ganin an raba tsakanin Khalid da Nabilah, ya tina dik fad’i tashin da akai wajen datse tsakaninsu ya bada nasa gudummawar, tabbas sai yaji bai kyauta wa amininsa ba, bai kyautawa abokantakarsu ba, sanin kansa ne tin tasowarsu Khalid bai tab’a soyayya da wata mace ba sai Nabilah, instead ya basa goyon baya yai supporting d’insa like a brother sai ya biyewasu Ammi da son zuciyarsu ganin sun datse k’aunar dake tsakankanin zukata biyu da Allah ya had’a, tabbas maganan da jiya Khalid yai masa yayi gaskiya cewa shid’in bai tara sani da Allah ba, Allah ka iya canza al’amaransa a duk lokacin da yaso, domin kaw shid’in Buwayi ne gagara misali... Ko a mafarki bai tab’a zaton auren Khalid da Nabilah mai yuwu bane sai gashi lokaci guda Allah ya sauya zuciyar mahaifinsa, tabbas ya yarda shi aure nufi ne na Allah kuma wani bai auren matar wani... Yayi alk’awarin baiwa Daddy his unconditional support har burinsa ya cika na ganin auren ya tabbata cikin yardar Allah, ta hakan ne kawai zai sakawa abokinsa butulcin da yai masa a baya....
Bayan sun ida tattaunarwasu da Daddy ya mik’e yanaiwa Daddyn sallama daidai sanda Khalid yai sallama ya shigo parlorn...
Mamaki ya cika Khalid d’in ganin Baffah tareda Daddy har suna sallama da juna, since when suka zama close haka..? Ga wata ‘yar takarda hannun Baffan da sam baiso Khalid d’in ya gani... Kallon kallo sukabi juna dashi sanda Baffan zai fice, Baffah sai sakar masa murmushi yake... Sosai Khalid ya karkata yana duban Baffah dake k’ok’arin ficewa yana mamakin wannan al’amari... Take masa baya yai niyyan yi sai kuma ya sinkayo muryar Daddy na kiransa, dole ya fasa bin bayan Baffah ya komaga kiran mahaifinsa... Daga can gefen k’afar Daddyn ya d’an zauna yanai masa sannu da gida....
Daddy ya amsa masa da yalwar fari’a kana yace “Dama ina nemanka....?”
Gaban Khalid ya fad’i ganin amininsa bai jima da ficewa daga parlorn ba... Badai wani abin yayi ba, tinda shine sarkin laifi a gidan Siyama ce ‘yar lele...
Murya har na sark’ewa yace “Daddy nayi wani abin ne...?”
Girgiza masa kai Daddy yai alamun a’a kana ya d’orada “Bakayi komai ba Son... Wani aiki nake so kamin a can Abuja, toh bansan ko kanada lokaci ba....”
Cikin sauri Khalid ya shiga girgiza kansa yana fad’in “Haba Daddy, ka wuce tambayan lokaci a wajena, umarni kawai kai d’in zaka bani....”
Daddy ya jinjina kai cikeda jin dad’i “Allah shi maka albarka... Akwai gidana na can estate d’in dake Gwarimpa, za’ai renovating... So inaso kai supervision aikin... Idan akwai wasu fittings da kake sona canzasu to your taste sai a canza.... Ka fahimta....”
Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace “Daddy su Aunty Daula zaka maida can.. Ko zaka maida Ammi Abuja ne....?”
D’an murmusawa Daddy yai kana yace “Kawai inaso a gyara gidan ne Son Incase of tomorrow... Kasan ance gida biyu maganin gobara....”
Ya jinjina kansa a hankali “Haka ne Daddy... Yaushe kakeso a fara....?”
“Kar ya wuce cikin week d’in nan if possible....”
“Alright Daddy... In sha Allah za’ai yanda kace....”
Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kana yace “Allah shi maka Albarka Son...”
Khalid ya amsada Ameen Daddy kana ya mik’e... A hanyarsa ta ficewa ya had’uda Ammi ta cika tayi fam sai faman danna masa muguwar kallo take... Kafin yai aune ta janyo hannunsa tana fad’in “Shige muje dama shigowarka nake jira...”
Khalid na tambayar “Mi nayi kuma Ammi....? D’an sakar min hannun...”
Bata saki hannun nasa ba bata fasa janyosa zuwa cikin parlorn Daddyn ba take fad’in “Bazan sakeka ba, na gaji da wannan wasan yaran da ake dani a gidan nan ehe....” Ta k’arashe sanda suka iso cikin parlorn gaban Daddy...
Daddy ya d’ago yanai mata duban mamaki...
Har lokacin huci take, ta shiga nuna Khalid da yatsa tana duban mijin nata “Toh gashi nan... Inaga idan yaji daga bakinka zai fi aminta cewa baida mata sai Yesmin.... Na gaji na gaji da yin k’anan muryawa Mahaifiyar Yesmin... Kullum cikin bata baki nake ina sanar da ita za’a tsaida magana k’wakk’wara... Daddyn Siyaam wannan harda naka laifin, gaba d’aya ka zubawa Khalid idanu yana nema ya maida mutane tamkar wasu mutanen banza... Toh wllhi bazan zuba maku idanu ba, maganar aurene dole a tsaida magana d’aya yanzu kam... Na gaji da wannan come gaba come baya da ake....” Ta k’arashe tana bud’e hannayenta alamun fad’a...
Tagumi Daddy ya rapka yana duban yanda Ammi ke falfala masa ruwan fad’a tsaye akansa saikace wata uwarsa...
“Kin gama...?”
Ya tambaya yana dubanta...
Wani kallon wulak’anci ta watsa masa daga nan yanda take tsaye kana tace “So kake na maimaita maka...?”
Girgiza kansa yai a hankali kana ya dubi Khalid yace “Jeka abinka kaji....”
“Toh Daddy...” Khalid yace sanda yake k’ok’arin ficewa...
Ammi ta bisa da kallo baki sake tana furta “Aww yanzu cewa zakai yaje, a maimakon ka tirsasa ya sakama ransa ya auri Yesmin an gama... Haba Daddyn Siyaam Wllhi kai kake d’aurewa yaron nan gindi yake raina mutane... Khalid! Khalid!!..” Tabi bayansa tana kira saidai bata cimmasa ba dan ya jima da ficewa...