Sashe 154
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washe gari kaman yanda ya umarceta ta shirya hakan ce ta kasance, daga nan cikin d’aki yanda take tana iya sauraro muryarsa yana gaida Mamy had’ida sanar da ita cewa yanzu zai biya ya d’auko su Mummy suyi sallama dasu....Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, addu’an samun strength kawai take cikin zuciyarta tana mai neman agaji da taimakon ubangijinta da ya bata ikon jurewa... Ga tinanin Mamani ya kasa barin zuciyarta, haka zata tafi basuyi sallama ba, sosai wanna abu ya tsaya mata a zuciya, fatanta Allah sa tana cikin k’oshin lafiya a dik yanda take....
Tana ji Mamy tana cewa bara ta shiga ta dubo Raihanar, bugun zuciyarta ya k’aru... Wato dai da gaske shid’in mijinta ne... Ta lumshe idanunta a hankali siriryar hawaye ta gangaro mata, saurin saita kanta tai sakamakon jiyo shigowar Mamy da tai, bazataso Mamy ta danganta cikin yanayin damuwa da tashin hankali ba dan jiyan kusa raba dare tai a d’akin tana bata baki da kuma nasiha... Sai take ga kaman bata kyautawa Mamy ba kar ta d’ago bata son auren D’anta ne.... Mamy ta sakar mata murmushi kana tace “Daughter kin shirya...?”
Ta jinjina mata kai a hankali kana tace “Eh Mamy...”
Jinjina kai Mamy tai kana tace “Toh maza gashi nan yana jiranki a parlor zaku wani wajen before kuzo ku wuce koh...”
Nan ma jinjina kai tai kana tace “Toh Mamy...”
Mamy tace “Allah miki albarka kinji....Idan kun dawo sai ku shiga wajen Abban naku tare kuyi masa sallama ko...” Nan ma jinjina Mata kai tai had’ida amsawa kana ta nufi parlor k’irjinta na matuk’ar bugu idanunta a k’asa...
A tinaninsa bazata saka kayan da ya kawo mata jiya ba sai gani yai ta saka sun kaw mata kyau... Kyakkyawan murmushi ya saki ba tareda ya sani ba, sosai yaji dad’in saka kayan da tai.... Idanunta a k’asa ta k’araso gareshi had’ida risinawa ta gaidashi.. Ya amsa yana mai shagala da duban yanda tai masa kyau sosai.... Shiru ne ya d’an biyo baya har tana dak’ida kana ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Muje koh...”
Babu musu ta risina had’ida bin bayansa... Yanda suka jera dole su birgeka... Yana sanye cikin jampa fara k’al da tai matuk’ar amsar fatarsa saiko bak’ar dara wanda ta k’ara fito da hasken fatarsa, kai da ganshi kaga sabon ango sai watsa k’amshin nan nasa yake... A haka suka nufi motarsa,yau d’in da kansa ya bud’e mata front seat ta shige kana ya zagaya ya zauna a mazaunin driver....
Gidansu Shamsu suka soma zuwa yanda ya kaitawa Maman Shamsu suka gaisa ya kuma sanar da ita yau suke tafiya Kaduna daga nan Abuja zasu shige dan duba jiki Daddyn Siyama... Mama tai masu fatan sauk’a lafiya had’ida saka masu albarka... Daga nan gidan Ammah suka wuce sukai mata sallama itama, har Zulfa’u ma ta fito suka gaisa, gaba d’aya fatan alkhairi sukai masu da sauk’a lafiya had’ida sak’on gaisuwa ga jikin Daddy....
Daga gidan Ammah basu zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Haule, gidan Mahaifin Raihanah.... Bugun zuciyar Raihana ya k’aru, tsoro da firgici suka wanzu sosai saman fuskarta, harga Allah batasan ya yanda zata soma jerawa dashi su shiga cikin gidan da sunan mata da miji ba.... Shi kanshi ya kula da yanda gaba d’aya ta daburce, ya fahimci tsananin tsoron da ya wanzu saman fuskarta... Sai faman rakub’e rakub’e take bayansa ta kasa cimmasa, gashi tin daga waje suke jiyo hayaniyar ‘yan daudu sai faman shewa suke cikin gidan.... Sameer ya d’an dakata kad’an har ta cimmasa, a hankali suke takowa har suka shigo cikin gidan sallama saman bakunansu dikda cewa muryar Sameer ne kawai mai iya fita, itakam Raihanah saima k’ok’arin mak’alewa bayansa da take.... Haba nan fah kallo ya koma kansu, gaba d’aya illahirin jama’an dake tsakar gidan suka bar abinda suke suka zuba masu ta mujiya... Haule dake kokawan k’watan tukunya hannun ‘yan daudu dan idan ta dafa abinci ta bari a nan kitchen saidai tazo ta samu an lashe mata tukunya gardawa sun cinye shisa sam da zaran ta d’aura abinci saidai tai zamanta ta jira ya dafu ta d’auke ta gudu dashi d’aki suci da ‘ya’yanta dan idan ba haka ba to kaw tabbas ma gardawa ta girka, ga Sahariyya ta k’aro wualk’anci tinda aka fasa aurenta da Sameer sai Naja’atu ne ma ke k’ok’arin taimakawa mabaifiyar tata, ga Baba Alhaji tinda yayi Amarya yanaji Haule na drama da ‘yan daudu a waje amma ko lek’owa baiyi, saidaima Magajiya ta fito tana mik’a ta mik’awa ‘yandaudunta sauran takardan tsiren da suka cinye ita da angonta a d’aki... Haule saidai taji hawayen da basu shirya zuba ba suna gangaro mata... A ‘yan kwanaki ukun dik Haule ta fice hayyacinta, kaman ba ita ba....
Tanaji ‘yandaudun nan suna fad’in “Wai Wai Wai bakin ‘yan gayu yau akai a gidan namu... Lale lale barkanku da zuwa... Namu ne ku ko nasu...?” Suka k’arashe cikin salo.... Ita dai Raihanah saima dad’a b’oyewa da tai bayan Sameer abin na kuma basu tsoro had’ida al’ajabi ganin irin wad’annan mutane cikin gidan Baba Alhaji....
Wani mugun kallon da Sameer ya aikama ‘yandaudun suka shiga ja da baya suna kame baki had’ida furta “Wai bari mu matsa kar maza suyi faccakali damu...”
Haule baki sake take dubansu yanda sukai mata bala’in kyau tamkar wasu taurarin cikin film, har malmalar tuwon dake cikin tukunyar hannun Haule ya fad’o Haule bata ankara ba.. Wai Raihanah ce take gani haka kaman wata sarauniya.... Sahariyya dake daga d’aki tana fad’in “Ya kuka daina fad’an kuci gaba man....” Birki tai ma kalaman nata sakamakon hangosu da tai hasken hantsi ya haske masu fuska har wani kashe idanu suke.... Ai take taji wani irin jiwa na d’ibanta... Raihanah da k’irjinta ke bugu ganin irin duban da Addah Sahariyya Ke masu tuni jikinta ya d’auki rawa zata kuma mak’alewa bayan Sameer amma sai jiyo sauk’an hannunsa tai saman nata ya rik’eta gam.... Idanun Sahariya suka sauk’a kan hannayensu yanda suke mak’ale cikin na juna... Zuciyarta yai wani irin tsinkewa k’afafunta taji sun gaza d’aukanta... Kasa tab’uka komai tai itama sai dubansu da take baki sake daga ita har mahaifiyarta Haule...
SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_
*98*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
NOT EDITED!