← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 198

Sashe 23

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita Sawwama da Mamanta suka dubi juna suka shek’e da dariya, Magajiya tace “Kinmin daidai yanzu ne zaki fahimci matsayinki a wajensa idan har da gaske sonki yake....”

Sawwama ta murmusa tana mai jijjiga ita kad’ai kana tace “Allah Magajiya ki tsaya ki gani tas saina mallakesa ni kad’ai a tafin hannu na.....”

Shewa suka kuma sakawa Magajiya tana mai rangad’a gud’a....

****

*Kaduna*

Tsaye take tana hangensa sai faman shirya masu dining table yake bayan ya gama dafa masu abinci mai sauk’i dai dai ci da dare, a hankali Siyama ta lumshe idanunta domin kuwa ko shakka babu tayi missing komai nasa...

Juyowa yayi ya ganta tsaye a wajen tana dubansa, kashe mata idanu guda yayi kana ya k’araso ya sureta cak suka nufi teburin cin abincin sai faman cakulkuli yake mata tana zillewa...

Zaunar da ita yayi saman kujera kana ya d’an rank’wafo yace “I’m the waiter here... Mai Queen d’in take son ci...”

D’agowa tai tana dubansa kafin ta saki murmushi tace “Kai Partner... I missed your delicious dishes..”

“I know that’s why I cooked for you honey....”

Murmushi ta kumayi kana ta mik’e tace “I’ll serve....”

Ba musu ya koma ya zauna yana dubanta yanda take serving abincin a hankali, nazarinta yake yana tunanin something is wrong with her, don gaba d’aya ya lura da canzawa da tayi ita kanta ta tsargu da irin duban da yake mata gaba d’aya gani take kaman ya hango abinda tai, mummunar fad’uwan gaba ne ya dirar mata sanda ta jiyo muryarsa na fad’in

“Partner... You know you look like a pregnant woman....Are you sure babu ajiyana a tattaredake....?”

Zaro idanu waje tai tana dubansa ba tareda ta iya ci gaba da serving abincin ba....

Murmushi saman fuskarsa ya mik’e ya k’araso gareta had’ida rungumeta ta baya hannayensa duka biyu d’aure saman shafeffen tummy d’inta...

Kansa saman kafad’anta idanunsa a lumshe yake ci gaba da fad’in “Partner don’t you think is about time mu fara tunanin building namu family d’in....?”

Saurin rintse idanu tai k’irjinta naci gaba da bugu, k’ok’arin saita kanta tayi kana tace “Let’s eat Partner, the food is getting cold already....” Ta k’arashe tana mai cire jikinta daga nashi jin ya soma sumbatar wuyanta....

Zata zauna kujeran gefe ya kuma janyota ta fad’o saman cinyarsa, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Honey I missed you... I missed you so much....”

Gaba d’aya sunyi nisa a wata uwa duniya har saida suka jiyo k’aurin k’onewan abincin kafin Siyama tai azamar k’wace kanta ta nufi kitchen d’in ta kashe gasscooker d’in da Sameer ya mance a kunne...

Tsayuwa tai kitchen d’in tana mai maida numfashi, bata isa ta mik’awa Sameer kanta a daren yau ba domin kaw ta mance pills d’inta da a kullum take shan k’waya d’aya a gida....

Bata koma parlorn ba sabida tunanin mai zatai ya kub’utar da ita hannun Sameer yau, ruwan zafi ta hanga cikin electric kettle take ta janyoshi ta d’an bige kad’an ya zube mata a k’afa...

K’ara ta k’walla wanda ya sanya Sameer nufo kitchen d’in babu shiri.....

A hanzarce ya k’arasa ya d’age kettle d’in yayi saurin d’agota yana mata sannu had’ida tambayarta ya hakan ta kasance, kasa ce masa komai tai sai narkewa da tayi cikin jikinsa tanai masa kukan shagwab’a...

Abinka da likitan k’una first aid d’insa ya d’auko bayan ya ciccib’eta ya kaita parlor ya kwantar saman kujera ya shiga mata dressing wajen, fad’i yake

“Sannu Partner, does it hurt..? Sannu koh.. Zai daina yanzu In sha Allah... Barin baki abincin a nan.....?”

Girgiza masa kai tai cikeda shagwab’a kana tace “Bazan iyaci ba na k’oshi please ka kaini d’aki...”

“Alright but ko fruits zaki sha....” Bai jira cewanta ba ya kuma sungumarta ya nufi bedroom da ita kana ya dawo ya d’ibi fruits a bowl ya koma d’akin yana bata a baki a hankali...

Kallonsa kurum take tana ayyanawa cikin zuciyarta da ace yanzu akwai d’iya ko d’a a gidan wannan gata da tarairaya duk bazata gansu ba saidai yayiwa gudan jininsa haka, dole k’aunar da yake mata da tarairayan da yake bata ya ragu a nata tunanin...

Haka Sameer yayita riritata yana mata sannu har bacci yayi gaba da ita tana mak’ale cikin jikinsa....

****

Banda safa da marwa Aunty Lami bata komai cikin tsululun dare ita kad’ai a cikin d’aki, sanin matsayin aminiyar sirri a wajen Ma’aruf ya haifar mata da shakku cewa bata kashe Ma’aruf ba kaman yanda sukayi zaton tayi......

SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*22*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

*Gaisuwa fatan Alheri gareku Ahalin SAN Aminiyar Sirri na gaisuwa ta gode da nuna k’auna🤪🥰*

Da k’yar bacci b’arawo yai gaba da Lami amma fah duk juyi sai fuskan matashin nan mai zubi da Ma’aruf ya fad’o mata, bata fata Mamy tai idanu hud’u da wannan saurayi kaman yanda tai, yanzu babban burinta bai wuce ta samu wata hanya da zata iya nesanta wannan saurayi daga gidan ba, don idanma ba shine Ma’aruf ba shakka babu jikinta na bata shi zai alank’antasu da Ma’aruf....

Washe gari da hantsi Mamy na zaune saman carpet a parlornta tana rage k’umbar hannayenta da k’afafunta, sai sautin karatun sheik Ahmad Sulaiman ke tashi ga wani had’edd’en k’amshin turaren wuta na ratsa sashen nata gaba d’aya, yaran nata duk sun tafi makaranta Aunty Lami tai sallama ta shigo rik’eda ‘yar k’aramar bokati na kindirmo had’ida fura k’ulle a bak’ar keda...

Mamy ta fad’ad’a murmushinta suna gaisawa sanda Aunty Lami d’in ta k’araso ta zauna saman sofa ta sha lullub’i alamun fita zatai....

“Su Marliya duk an tafi makaranta koh...?” Ta tambaya murmushi kwance saman fuskarta,

Mamy ta rage sautin karatun kana tace “Duk sun fice Nabila ma sun koma satin nan....”

Aunty Lami ta kuma murmusawa tana furta “Allah sarki b’angaren namu duk sai yayi shiru, koda shike gidanma gaba d’aya tinda duk sauran yaran ma sun koma...”

Mamy ta jinjina kai tace “Haka ne... Fitane zakiyi...?”

Aunty Lami ta kuma murmusawa kana tace “Eh zanje gidan k’awata Hajiya Tani kinsan an saka bikin d’anta....”

Mamy ta d’an murmusa kana tace “Kai Masha Allahu, Ubangiji Ya sanya alkhairi, ki gaidata idan kinje, lokacin bikin idan Allah ya kaimu ma lek’a...”

Aunty Lami tace “Haka ne.....”

Lokaci guda ta mik’awa Mamy ‘yar bokatin kindirmon da fura tace “Jiya aka kawomin daga gari mai kyau dashi...”

Mamy ta amsa fuska d’auke da murmushi saida tinda taji k’amshin fura fuskanta ya d’an canza, ta shigo tuno d’anta Ma’aruf abinda yafiso kenan a rayuwarsa, kullum idan Abbah ya fice kasuwa sai ya dawo dashi, tinda Ma’aruf ya b’ace kindirmo da fura sukai k’aura ma gidan, shi kanshi Abbah sai ya zamto ko k’anshinsa baiso balle yayi ido dashi....

Aunty Lami tana hankalce da yanayi Mamy dama abinda take son gani kenan....

D’an muskutawa tai kana ta kwantar da murya yawa mutuniyar arziki tace “Mamy rashin Ma’aruf bai kamata yasa rayuwarki ya canza gaba d’aya ba, karki mance shifa Allah na son mai hak’uri da tawakkali, kar ki biye na mijinmu sabida ke kin fisa zuciya mai taushi dukda rauni da zuciyar taki kedashi... Mamy shifa duniya tinda muka zota toh fah duk daren dad’ewa wataran zamu barta, yau shekaru ak’alla talatin ya kamata ki mance komai kici gaba da gudanar da rayuwarki kaman da dukda cewa nasan hakan nada matuk’ar wahala amma daurewa zakiyi....”

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Haka ne Lami, kuma na gode da shawarinki masu kyau, tabbas Allah na tareda masu hak’uri da kuma tawakkali... Amma cireshi a zuciya gaba d’aya abune mai matuk’ar wahala, yau da ace naga gawan Ma’aruf da idanuna da abin bazai dameni har haka ba tinda na sani duk mai rai mamaci ne babu babba babu yaro babu tsoho lokaci tanayi dole a tafi.... Amma banga gawanshi ba, shin yana raye ko ya mace, idan yana raye a ina yake rayuwa...? Wane irin addini da tarbiya ya samu, shin a ina yake samun abincinda yakeci har ya rayu ya girma, inane makwancinsa.... Shin idan ya girma yanada iyalai ko baida shi....?” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in

“Lami wad’annan tambayoyi sune suka tsaya min a zuciya, sannan duk yanda nakaiga amintar da zuciyata cewa Ma’aruf ya mutu abin yaci tura, zuciyata tak’i amsa tak’i yarda cewa Ma’aruf baya raye a duniyar nan... Zuciyata tafi k’arfafa min cewa akwai ranar da zai dawo gareni ranar da zan kuma tozali dashi, ranar da bak’in cikina zai yaye zuwa akasinsa... Sannan inaji wannan rana gab take da zuwa....” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska....”

Kaman daga sama sai jiyo muryar Mamani sukai tana fad’in “Daga baya kenan wai sadaka da bazaura, duk kinsan da wannan kika jajib’esa kikaje kika jefar dashi... Yo waye ma ya sani ko saidashi kikayi tinda babu irin abinda ba’ayi a wannan duniyar tamu, uwa takan haifi d’a ta toni rami ta bisne sabida bata sonsa, uwa takan haifi d’a ta saidashi ma k’ungiyar asiri ta shan jini don ta sami kud’i, munafuncin banza kizo kina damun mutane da bak’in iyayi, bazan daina miki Allah ya isa ba Mariya b’atarmin da jika da kikayi... Algunguma kawai....” Wiwiwiw nan ta shiga rera kuka kaman an kunna injin markad’e...Aunty Lami ta mik’e da sauri ta rik’eta tana bata baki ta fitar da ita zuwa sashenta...

Tinda Mamy ta kifa kanta hawayene kurum ke zubo mata, jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi uwar d’aki don yin alwala dama bata gabatar da sallan walha ba kaman yanda yake d’abi’a nata, tuni ta shiga mik’awa ubangijinta kukanta.....

***

*Kaduna*

Yana kishingid’e saman sofa a parlor yana kallon shirin The Dr’s da ake gudanarwa da hantsi ta sauk’o daga saman bene taci uwar gayu kaman ba itace jiya da dare take kwance nasha nasha ba....

Da mamaki Sameer ya d’ago ya dubeta kana yace “Ina zaki da k’afar taki, ko ta daina zafin ne....?”

K’arasowa tai had’ida aje handbag d’inta saman kujera kana ta manna masa sumba a gefen fuskarsa tace “Partner nayi latti, presentation ake jirana zanyi a office....”
Chapter 23 · 0% Book details